Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

... Ta dade tana zuba adduointa, ta rufe da salatin Manzon tsira, ata kwanta ba saida sallaci asubah kana tayi matashi da hannunta na dama ta bingire bisa sallayar. Hanyace data kasu har uku, ta rasa wace zata bi, dama,hagu ko tsakiya? Ta yanke shawarar bin hanyar dake damanta, 'yar siririyar hanyar cike take da itatuwa da ciyayi Korra shataf, bata yi nisa ba sai gata gaban wani tafkeken kogi Mai shakare da wasu garai-garain ruwa masu kalar sararin sama, nan ta gane baby hanyar wucewa kenan. Ta juyo cikin hanzari da niyyar ta koma baya nan ta rikice dalilin hanyar ta rikide ta hade danyen ciyawa da itatuwa ga ruwa male-male ta ko' Ina, daga saman bishiyoyin wasu irin kyawawan tsuntsaye ke kuka tamkar suna busa sarewa, sanyin tafkin nan ya fara ratsata, sanyi ya kadata ta shiga makyarkyata, hakan yasa ta waige-waigen da tunanin ratsawa ta cikin ruwan ta fita wannan wajen, tsoro ya kamata, nan take ta daga hannayenta sama ta fara rokon Maiduka ya kawo mata dauki.. Cikin ikonsa Allah sarkin sarauta sai taga wani mashahurin haske ta ko'ina, wani doki Mai fuka-fuki da ya ratso ta cikin hasken nan a guje ya sauko daf da ita. Jikin dokin ba irin dawakan data sani bane, wannan ilahirin jikinsa kalar azurfa ne, gashin bayansa gazar-gazar da kwarar idanunsa ne kawai bakin kirin. Tsananin ganin wannan halitta daya cikata yasa bata lura da mutumin dake Kan dokin ba, bata ankara ba taji an dagta sama an dorata bisa dokin nan ya tashi sama suna tafiya tamkar wasu tsuntsaye, basu dade ba taga sun sauka daf da kofar wani farin gida gewaye da furanni, hancinta ya shaki wani hadadden kamshin data rasa inda yake fitowa, kamar tafiyar slow motion ta tsinci kanta cikin wani lambu cike da kayan marmari, ta mika hannu don ciro nunanniyar goba tsawonta bai Kai ga iccen ba, Mai dokin Nan ne ya matso yasa hannunsa ya ciro goban Nan har zai Mika Mata sai dokin yai haniniya ya kada fukafukinsa sai ya fasa bata Saida ya saka a bakinsa ya gutsura kana ya mika Mata sauran ta karba cikin mamaki, har zata Kai bakinta ta tuna bata san ko waye ba, ko kafin ta dago Kai ya haye dokin ya fara tafiya, ta daga masa hannu tana kiransa da muryar data shake, waigo wan da yayi yasa taga fuskarsa a zahiri ... Ganin ko waye yasa ta nemi yar da rabin gwaibar da ya bata Amma abin mamaki taki faduwa kamar ansa gam an manne gwaibar a hannunta, cikin hanzari ta sake juyowa ko za tayi katarin sake ganin fuskar.. aka yi dace shima ya sake waigowan yana murmushi a gareta, kamar walkiya dokin da Mai dokin suka bace... Alhamdulillah Hamdan Kaseeran... A nan littafin RAHIMA na daya yazo karshe. Za mu ci gaba dana biyun insha Allah. Ina godiya ga Masoyana a duk inda kuke ina muku adduar fatar alkhairi a gareku. Nayi kuskure ban bada number waya ba a farkon wannan littafi, to ga masu son saye da nemana ta WhatsApp a neme ni a wannan num 08034243456 WhatsApp kawai plss Masu son kirana Kuma a nemi a wannan num 07036391747 06/09/2020, 19:50 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami 16 Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake. Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta. Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da 'yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa? Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace "Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra'ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki " Ta gyada Kai "Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa." Yace "Lalle kin cika 'yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya.".. Tace "Godiya nike sosai Allah saka da khairan." Yace "Ba komi Rahima." Goma da mintoci har Maryam ta fara barci Rahima ta tashe ta "Barci tun yanzun?" "Yes tunda ranar hutun kenan da Alhajin ba nan yake ba." "Kina nufun idan yana nan ba Kya hutawan?" Ta amsa "kusan hakan ne kina wasa da Alhajin nan da kike gani, wallahi duk ta sangarce, daidai da spoon bai iya dauka da hannunsa ya Kai baki idan ina kusa." ."Su soyayya masu gari." Maryam ta gyara kwancita "Karki zargeni, ke din wa yasan abunsa za kiyi nan gaba, ya kuka kare da Alh Suraj?" Rahima ta sanya rigar barcinta kafin ta amsa "Na fada masa gaskiya yai accepting wai sai Kun Kai masa Iv." Maryam tace "Ko nifa bana amince dashi bane just tsokanarki nike da naga baki da niyyar fidda kowa, yanzun shi Wanda Hajiyar tayi magana ne a fagen?" Wani irin murmushi da farin cikine suka bayyana a fuskarta, Maryam ta daki kafadarta da matashi tace "Lalle wannan ya samu karbuwa a zuciyarki, fada mini ya kike ji?" Saida ta kwanta ta tasa kafadarta da matashi tace "Za kiyi mamaki Yaruwa domin nima cikinsa nike, ashe mutum Kan so Wanda bai taba gani ba, ni fa ko sunansa ban sani ba, labarinsa ma not in details naji amma na kagu na kosa in gansa inji yaya zanji ranar dana fara ganinsa?" Tayi dariya "To ya zaki kwatanta abubuwan da kike ji yanzun da wanda kika ji game da marigayi." Ta tashi ta zauna "Ai sun Sha banban 'yaruwa, son Rabiu a hankali ya riga shigata kwatankwacin mutum ta dora ruwan zafi bisa wuta, a hankali ya fara dumi, ya kai ga zafi har ya nuna alamun tafasa sai wutar ta mutu, to yadda ya fara zafi hakan ya rinka hucewa yana sanyi a hankali har ya zamto yanzun na hakura, dana tunasa adduar samun rahama nake ci gaba da yi masa kullum, wannan kuwa gaba daya ruwan ya dau zafi, kafin in ankara har ya tafaso ya fantsama koina, zuciyata na kuna, babban abinda ke firgitani addua nike lamarin na kara

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66