Chapter 63
Chapter 63
fara hada komatsaina nace na gaji gidan zan bari. Wai sai ita da yaran suka yo tsinke suka yi min tsaye a kofar daki suka ci gaba da rashin mutuncinsu wai ai daman sun gargadeni in bisu a sannu ko su shirya min tuggun da zan bar gidan dole, harda cewa igiyar auren kowacce matar gidan hannun uwarsu take sai sun so a zauna. To alhaki kwikwiyo a zatonsu Uban nasu yai nisan kiwo Ashe ya dawo ya shigo gidan basu sani ba yana tsaye yana jinsu, can suka ganshi da iccen faskare suka watse, yace ya saki uwar tasu saki guda, Ni Kuma yaita bani hakuri. Za kuyi zaton muna zaman lafiya da ta biyun, to kusan gara uwargidan ta fito da maitar ta a fili nasan bata kaunata, wannan sari ka noke ce macijiyar kaikayi Saida na jima a gidan na lakanceta, munafuka ce ta gaske, ita 'yar a buga nan da can ne,ta kware wajen iya kissa, ta zama bakin kalangu duk inda ta lura yafi zaki can zata buga. Lokacin da uwargidanmu ta fita nayi biris da ita tunda na lakaci halinta,sai ta ja yaran uwargidan a jiki, ta nuna musu Ni nasa a saki uwarsu da asiri. Wata rana kadangare ya shiga dakinta ta rinka kwarma ihu har saida maigidan ya fito ya shiga dakinta ya shiga aka koresa ya fita. Bayan kwana biyu sai kawai naji gulmace-gulmace na tashi wai na tura mata asiri da kadangaruwa din itama in koreta, wasu sun kama wasu suka ce sharri ne, abin ya dameni da farko daga baya nace Allah ya isar min ni da ban taba tsugunawa gaban malami da sunan neman taimakon asiri ba." Rahima tace "Ai sai ki barta da Allah ya saka miki." "Ai tuni nayi na Kuma rokesa ya tona asirin masheranta, Kar Kuma ya hore min ko sisin da zanje in cuci danuwa musulmi. Na rokesa da ya dawo da uwargidansa, yanzun da ya taho da batun auren ta hudu nace watakila idan ta taho na samu sassaucin tsangwamar da suke min. Kuma ga sakayya nan na fara gani wace zai auro diya aminiyar ita munafukan ce ce duk yawon gidan malamai tare suke zuwa, sun san sirrinta kaf. Mai 'ya'ya mata Kuma dake bugun kirji da takamar suke korar mata kishiya yarinyar da za a kawo ta dama su ta shanye a rashin ta ido, bata ganin Kan kowa da gashi kunga me zance na koma gefe Ina kallon yadda kowacce cikinta ya duri ruwa " Rahima tace "Idan ta taho ki kama girmanki karki sake ta rainaki, kiyi hakuri ki ci gaba da zama dasu da zuciya ki kama mijinki ki rike Kam,wace ta gaji da haukar ta warke kiyi huldar arziki da ita, wace taking ki shareta kici gaba da hidimominki, wace ta nuna bata kaunarki ki gujeta daga Nan har birnin sin din makiyi abin gudu ne." Shafa'atu tace "Ko Ni na dauki shawarwari nan insha Allahu." "Kema kishiyar gareki?" Maryam ke son sani.. Ta girgiza Kai ",Ba gara kishiyar da kuka hada miji daya kunsan duk shu ya ajiyeku ba a bisa tawa kishiyar sauri ce (Kishin bal-bal) "Mu dai Allah ya yaye Mana m wannan jarabar, tsakaninmu da matan kannin Dakta ladabi da biyayya muma mun rike girman mu." Maryam tace "Sa'a kuka ci Allah bai hadaku da masu shegen kyashi da hassada ba " "Kamar dai yadda matar wan mijina take. Gida daya muka zauna lokacin ina amarya,tun kafin in haihu Nike m dawainiya da yaranta har mijina na jin haushin yadda nike mata, yini guda Ina tsaye tsakar gida kamar wata tabarya, inyi hidimar girkinmu inyi hidimar shara wanke-wanke da lalurar yaranta duk a tunanin tunda nice karama, mijina ma shine karamin hidimomin sun hau kaina,ita kuwa ta kwanta ta shari barcinta. A nan na samu admission na zuwa school of nursing, karatu ba zai barni ci gaba da hidimar gida yadda na saba ba, na roketa tayi girkin rana in rinka na dare,matar nan fir taking yarda, tun a nan na gane bakin cikinta a tare dani.Ta amsa da kyar, ba ayi nisa ba ta fara korafin ta gaji da yi min wahala Ina can Ina gantali, wasa wasa muka raba girkin, sai raba mazajenmu cin abinci kwano daya, Sabiu yai bacin ransa ya hakura ga ba uwa ba uba duk sun rasu balle su tsawatar sai kanninsu Mata, yau ta bullo da wannan gobe wancan har dai na fahimci tsantsan kishina ke damunta dalili da Allah yaiwa mijina nasibi fuye da nata duk da haka yana kwatanta musu alkhairi don Yana son danuwansa amma mata ta shiga tsakiyarsu har ta kai ko ga maciji ba suyi tsakaninsu, a haka mijina ya sayi gida muka tashi yace ya yafe masa nasa rabin gadon ya hada da nashi, yanzun haka ba wanu shiri ake sosai ba saboda kawai Allah ya horewa wancan wannan bai Kai samun wancan ba, amma mace ko miji daya muka hada Ina naga lokacin fitina, kishin da ba na neman kudi ba ai ya zama shiririta. Rahima tace" Watau mu Mata problems din mu yawa ne dasu, haka kawai mace ta daukowa kanta rigimar da zata dameta ta rasa nayi, rayuwar duniya? Kan mazan yanzun ma da basu da tabbas Allah dai ganar damu yai Mana jagoranci. Zuwaira ta kare abincinta mai rai da lafiya ta zubo suka hadu suka ci banda Rahima da ta kasa cin komi tana kwance, sannan suka tafi bayan sunyi sallar la'asar. 22/09/2020, 18:19 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 52 Bayan tafiyar bakinta ta kwanta ta dafa kanta ta karanto suratul fatiha *7 hade da ayoyin shifaa, nan da nan ta sami saukin ciwon kai da ya dameta, ta juya ta dauki remote ta canza channel din dish tana kallon labarai, nan barc ya dauketa.. Ya shigo ya ganta a haka bai tasheta ba, ya karbi remote din dake hannunta ya rage sautin tv kadan ya fita zuwa sashen Zuwaira. Ta fada mishi Rahima bata jin dadi, ya gyada Kai ya wuce dubo yara da sukayi barci, ya tofa musu addua ya dawo yai ma Zuwaira saida safe ya koma sashensa, yaci abinci kana yayi wanka ya kimtsa kana ya sake komawa sashenta. Still bata farka ba, ya zauna shiru yana nazarinta kafin ya mike ya nufi bedroom dinsa ya kwanta. Can cikin dare ta farka ta ganta bisa settee, a takaice Ya Haseeb bai dawo ba kenan, da ya shigo ba zai barta ta ci gaba da kwanciyar haka ba, can ta shaki kamshin turarensa ta bude ido sosai, this isn't her imagination lalle ya shigo ya fita abinsa tunda har yanzun fushi yake da ita. Ita ma ta kai kul saboda bata ga dalilin da zai sa ya dau batun da zafi ba bayan ta riga ta bashi hakuri ta nemi afwar laifinta. Yes tasan tayi kuskure domin komi kunyarsa da take ji ba zai hanata mishi albishir din rabon da Allah ya basu ba, Wanda idan ba Ubangiji ba wa ya isa yai wannan ikon? Ya tsaga rabon haihuwa tsakaninta da wa da kani? Fushinta na wofi ne maras tushe tunda ta riga ta amshi Haseeb a matsayin mijin da Allah yai mata zabi, ta amince wani hanin ga Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66