Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

gayyar take watsewa, ko yaranmu baka ja su a jiki ba, Ina iya cewa ma yadda ka shaku da wannan yaron Abdul baka shaku da 'ya'yan cikinka ba, basu Sami wannan gatan ba." Yaji tayi shiru, ya aje remote ya fusknceta " kin gama?" "Eh ta amsa. Yace "Tunda Allah yasa yau da kanki kie son ayi batun sai ince alhamdulillah do n many times nayi yunkurin mu zauna mu tattauna issues dunmu kika ki yarda kika nuna abinda ke faruwa duk laifinane, Amma tunda kin yarda akwai problems a zamantakewar mu sai ki fadi muji a Ina na kuskureki? Zuwaira tace "Baka ji abubuwan dana lissafo bane?" Yace "Oh sune kike ganin problems dinmu kadai? To bari ni in bayyana miki ko ince in baki amsa ki hujjojina na sanya miki ido da nayi. Na farko duk matar arziki tana nunawa matukar kulawa da harkokin maigidanta na yau da kullum, har idan akwai shawarwarin da zasu amfaneshi ta bashi , idan gari ya waye ta kula da dawainiyar breakfast dinsa Dana yaranta in akwaisu, idan zai fita aiki tayi masa adduar fatar alkhairi, su rabu cikin farin ciki su yini begen juna, idan ya dawo ya sameta cikin suturar mutunci, ta tarbesa da da abinci masu gamsarwa, idan lokacin barcinsu yayi suyi hirarsu Mai sanyayar da zukatansu har in suna cikin mood su kusanci juna ta hanyar da Allah yai mana umurni Kuma Manzon Allah yai mana koyi a addinance sabida hakan zai haifar musu da nishadi da Kara musu shakuwa ba a kwana ana jin haushin juna ba. To ke kuwa duk safiya na Kan tashi ne in barki kina barci baki sa niyyar tashi ba ma saboda kinada rauni a addinin naki, batun hidimata dana Yara kuwa kin halastawa mai aikinki tayi Mana, lokacin da na dawo gida ba lale in sameki ba, kin dau mota kina garari a gari, ba Kya gidan wannan buki ba Kya gidan wancan abokiyar kasuwanci. Idan anci saa kin zauna a gidan, Zan shigo in taras dake da kawayenki ne yan duniya, wadanda suka fi karfin mazajensu iskar duniya na dibansu. Abincin da kikan girls so da yawa nakan gwammace zuwa ci a hotel da inci naki sabida baki zauna kin kula yadda mutum zaici hankali kwance ba, ke kanki ba Kya cin abinda kika dafa a tukunyarki kin gwammace kullum ki aika a sayo miki nama ki ci. Batun rashin kusantar yara da kike kin basu damar zama cikin gidansu ne? Ko kuwa kin kaisu wajen mahaifiyata tace na zata iya ba? Nasan gidanku kike kaisu but mun san zama gidan ubansu yafu musu fa'ida. A nan ta hayyayako "Ai da tuntuni ka nuna rashin amincewarka dana rinka barin maka yaranka muga tsiyar da zaka basu a gidan.. Yayi wanumi dan murmushi "Duk takamarki kudi ko? Gidanku ba matalauta bane, to Ni dinma ba matsiyaci bane. Yanayin aikina yasa na amince miki Kan ki rinka kaisu gidanku din sabida da kina zama a gida da yaran basu rinka watangaririya ba. 09/09/2020, 14:13 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 21 Dr Haseeb yaci gaba da fadin "Shin kin taba tunanin kai yaran nan wajen Mahaifiyata su rinka debe mata kewa? Ah ah ke sam babu ruwanki da harkar dangina sai wadanda suka zama miki dole, yau satinki nasa rabonki da gidan Hajiyar? 'yanuwana sunyi korafin kin kama 'ya'ya kin rike basu san kowa ba sai danginku, sun gaji da complain sun hakura. Kina korafin bamu shaku da juna ba ko? Ta yaya hakan zai kasance bayan kin nunawa duniya mutanen da kike hulda dasu a waje sun fini mutunci da matsayi a zuciyarki, ya za kiyi tsammanin ni Haseeb in zama second best a rayuwarki? To bari ayita ta kare yau Zuwaira, shin kinsan nasan fa duk shigi da ficin da irin mu'amalar da kuke yi da wasu mazan da sunan kasuwanci in and outside Nigeria? That's why naja baya dake, na sakawa sarautar Allah ido, duk ranar da Allah ya kawo karshen aurenmu shikenan don na gaji da zama da wace zuciyata ke mata zargin fasikanci." Tana jin yai shiru ta tuma gefe ya dafe kirji tareda zaro idanu "Kazafi Kuma za kayi min Haseeb?" Ya girgiza Kai "Kinji Kuma daya daga cikin halayenki dana tsana *karya* duk maganar da zaki Fadi aka yi nazari aka tace sai an gano karyarki tafi gaskiyarki yawa a cikinta, kinga bani ba har Allah daya haliccemu ya la'anci mai yinta, yai hani da yinta, kince Kuma kazafi wane irin kazafi ga dahir nan kowa na gani? Ba ma sai an kaita da nisa ba, fara tuhumar kanki tun daga Kan irin shigar da kike yi, yadda kike gudanar da tsarin rayuwarki, na mijinki da zuriyyarmu, yaya tarbiyyarki ke tafiya, shin kina kokarin tsare abubuwan da Allah ya umurceki kiyi, kina gujewa abubuwan da suke munkar a gareki? Look at you now, just look at irin shigar da kika yi a matsayinki ta musulma, fara da gashin kanki, gaki nan roba ce ko yizgar doki ko wace tsiya ce kika Kara a kanki oho wai ke gayu, gayu ko yin biris da hanin addininki, ke kin isa kiba kanki abinda mahaliccinki bai azurtaki dashi ba? Dubi tun daga yatsun kafarki zuwa hannu, yanke kumba bai cikin tsarinki abinda Manzon tsira yai mana koyi da yanketa duk ranar jumma'a don inganta tsabtar jikinmu da samun lada saboda ita din najasa ce, wani lokaci har fenti kike musu wai duk cikin gayu tunda ibadar bata tsaya miki bane, bki ma san hukuncin barin lam'a wajen al''wala ba, kalli suturar dake jikinki, gata nan har Kara amma bata kare a hango yanayin surar jikinki ba.... "Karfa kaga laifina a nan, wallahi kai nikewa kwalliya saboda idan banyi ba ka isheni da korafi.' Ya kalleta wani iri "In don nine kike sabon Allah irin haka na yafe. Duk matar data san mutuncin kanta ba zata rinka irin shigar da kike yi ba, idan Kuma domina kike, ai ko Ina kasar ko ba nan hakan kike shigarki, haka kike fita duk inda kuka ga dama keda kawayen naki, mutuncinki a zube, na iyayenki a watse, Ni Kuma duk irin matsayina a garin nan wasu na min kallon namijin hotiho wace matarsa tafu karfinsa, to ba fun karfina kika yi ba, Allah ne shaidata tunda naga kin fara canza salon rayuwarki na fara yi miki nasiha, baki ddauka ba, na gaji na hadaki da iyayenki duk a wofi,maimakon ki canza sai kika Kara fekewa, Kika ce wai Ina neman hadaki dasu ne, to sai na gaji na sanya miki ido kije duniya taci gaba da rudinki, shaidan yaita busa miki sarewa kina taka rawa, abinda na sani gida biyune, da inda zamu tafi komin dadewarmu a duniyar, yau Ina Rabiu, kina ganin lokaci kalilan Allah ya rabamu farad daya, kafin shi mutane miliyan nawa suka rigamu gidan gaskiya, mu din ma ba zama za muyi ba, tun muna jin na wasu wata rana za aji namu, ke don Allah ko tunanin mutuwa ba kya yi? A kance wanda duk yai nisa bai jin Kira, Zuwaira ta fara nisa, tafiyar ta tafi sai nema mata shiriyar Ubangiji saboda rabi -da rabi take saurarensa, hankalinta ya dauku da tunanin irin cakewar da

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66