Chapter 62
Chapter 62
Shafa'atu ta shigo gaisheta suna hira Zuwaira ta damu ta shiga Ina ka saka da kanwar nata don tunda suka shirya haka suke kaffa-kaffa da kulawa da juna musamman idan rashin lafiya ya shigo. Kasancewar Rahimar ce da aiki Zuwaira ta shigo sashenta ta tambayeta abinda zata dafawa maigidan tunda ita tana kwance. Tace Aunty akwai time table na nau'ikan abincin da muke dafawa kowacce rana Uwale ta nuna miki ko ki dafa duk abinda kika ga ya kamata, nagode." Zuwaira tayi dariya "Godiya Kuma tsakaninmu kanwata, in dai lalura ce yau gareka ne gobe ga danuwanka balle ance ko baka iya alkhairi ba ka yiwa mai maka, ni so nawa kika shigo Kika taimaka mini? Fatanmu dai Allah yasa murar alkhairi ce." Sallamar su Maryam yasa Rahima ta dafe kai tace "Aunty ga 'yan baka nan don Allah karki maimaita batun nan a gabanta." "Yaushe Kuma ai na riga naji, Hjy Zuwaira Allah ya amsa harda nan bangaren don naga sai wani sisi kike yara sun dade da zama samari." Zuwaira tayi dariya "Marhabin sannunku da zuwa, Aunty Maryam karki ga laifinmu a nan tuhumi Dakta, may be tsufa ne ta fara aikinta." Maryam da kawarta Ummul khair suka shiga ciki Zuwaira ta bisu aka gaisa kana tace "Komin tsufansa idan ba zaku tabuka ba sai mu sake darzo masa amarya.". Rahima tayi murmushi "Yo ta taho mana wa ke tsoronta?" Ummulkhair tace "Ai tsoron ba naku bane nata ne don duk wace tace zata shigo cikinku gaskiya sunanta sorry.' Maryam tace "Tabbas zamanku na burgeni, Allah ya Kara hada kanku." Zuwaira ta amsa "Ameen Bari in shiga kicin in dawo." Ummulkhair ta rike baki "Oh ina ma ace gidanmu ya dawo irin naku? Rahima tace "Wai har yanzun babu canji a yanayin zamanku?" Ta girgiza kai "Ai Rahima yanzun ne ma gidan ke Shirin zama sansanin fada sabida ga goron amaryarmu ta hudu na kawo muku." Rahima tace "Ikon Allah! Duk kwasar karar mahaukaciyar da akeyi a gidansa bai isa ba sai ya karo wata masifar?" Shafa'atu tace "Namiji ne fa,? Ai sun fi son su tara ayita bala'i da masifa a kansu." Maryam ta gyada Kai "Wannan idan Allah bai sa kun fahimci rashin alfanun rashin zaman lafiyar ba kenan. Muddin kuka yi hakuri da juna sai ku sami salama da kwanciyar hankali.". Ummukhair ta gyara "Dace da irin wadannan kishiyoyin da zasu fahumci zaman lafiyar yafi zama Dan sarki, su fahimci arziki bai samuwa saida hakuri Abu ne mai wuyan gaske a zamanin nan da muke ciki. Idan ba a samu mai shurin shigowa ra fishsheki ta tsigeki cikin yaranki ba za a samu Mai cewa ki shigo din ki gane kurenki tunda kin auri mijinta, sai kace kowanne namiji an lika masa lambar zama da mace guda ne a goshinsa, ku dai kunyi dace da kishiyoyin." Daidai Zuwaira ta leko tace " Hmmmm all the credit goes to Rahima, tambayeta ta baki sirrin." Tana juyawa Ummul khair ta kalleta "Da gaske?" Rahima ta danyi murmushi "Fada kawai take yi, yes ba shakka mun dan fuskanci problem tsakaninmu amma hakuri, kau da Kai, dogaro da kai wajen samun sana'ar da zata hana maka bata lokacinka kan al'amurran kishi, kyautatawa juna, girmama juna, tarbiyyar yaranmu tafarkin gaskiya, sanin hakkokin junanmu da yadda zamu sauke hakkin, danne zuciya daga saurin fushi, toshe kunnuwanmu daga kunji-kunji, rashin ganin kyashi da hassadar junanmu, tsayawa a matsayin da Allah ya ajemu, kyautata ibadarmu wajen bautar Ubangijinmu da mika dukkan al'amurranmu garesa suka shafe komi, suka kawar mana da dukkan fitunu dake tasowa ya mamaye cikin gida, sai kyautatawa shi kansa uban tafiyar Wanda sirri ne don kowacce da nata salon." Ummulkhair ta jinjina tace "A gaisheku da kokari, ko a nan kinga hannu guda ba zai dauki daki ba, Ni kadai ba zan ita gyaran al'amurran gidanmu muddin ba mataimaki." Rahima tace "Wajibi wata ciki tafi hakurin da kau da Kai saboda Allah bai halicci zuciyarmu iri daya ba, haka zurfin tunani da hangen nesa ba zai zo daya ba, abunda wata zata dauka a shekara wata ko na minti gudan ba zata iya dauka ba, to ana son idan an hadaku ita mai zafi ce ke sai ki yayyafawa kanki ruwan sanyi, tayi masifarta ta gaji baki tanka ba balle ku zama daya, ba Kuma za kiyi shirun don tsoro bane, no zaki nuna mata ke tarbiyyarki ta daban ce, sai ta gaji ta bari yau da gobe don kinsan akwai ciwo mutum ya takaleka baka kulashi ba." Ta gyara zama "Kin dai San mu uku ne, Ni ce karama, dukkanmu muna da Yara, na Uwargida sune mata manya sun girma sun isa aure, amma saboda mugun tarbiyyar da uwarsu tayi musu gaisuwa ta fatar baki bai hadani dasu dai dai kuji suna wake-wake da habaici har da zage-zage wata ran wai dani suke, in hanya ta hadamu su nemi bangajeni suce idan na isa in taka su karya banza.. "Tafdijan! Inji Shafa'atu me ya hana ki lallasata ki barta kwance ba kiga wa ya tsaya musu?" "Uwarsu mana tunda ita ke turosu suyi rashin mutunci, ai na taba daukar mataki na dake su da suka kaini makura sai uwarsu tazo taci dammara tace da ita zanyi itace kishiyata ba su ba, suka taso za suyi min taron dangi suka ga ba zasu ci riba ba don ba zan dau rainin da rashin kunyar da suke yiwa ta biyun mu ba sai suka canza salon rashin mutunci,idan nayi abinci babu mai ci, yarana cikin duka da kyara kullum, babu mai daukar musu, ko ciwo suke yi babu mai lekowa yace musu sannu daga su har uwar, ita wancan ce da suke yiwa cin Kashi ta kan Dan leko. Ga sata ga keta, komi na ajiye a sace, su bata na batawa su zubar da wasu, kullum Ni kenan boyon tarkace, ko wanke tufafina dana Yara nayi wajibi gareni in girke kujera in zauna jiran su bushe in kwashe karsu sa reza su kekketa min. Da suka ga ban nuna damuwa ba sai suka zuba min gishiri ko suka zunduma min ruwa yafi karfin sanwata,,sai su aza tukunya su dora wani su ci su koshi, ko su fita su sayo wani suci su koshi." Maryam tace ",To shi maigidan yana Ina ake badakala haka cikin gidansa?. Rahima tace ga abin damuwa nan gurbata tarbiyyar diya mata, ita wace irin uwace da zata saka 'ya'yanta mata a harkar kishi? Me take koyar dasu kenan, Shi Kuma uban ya Kyaleta tana la'anta tarbiyyar yaransa?" Tace "Ya Zama mijin tace ai. Ba ya iya kwabon yayansa Sam, nida nike kokarin kwabawa sunce na cika tsanani ne, nace a tafi haka. Kwanaki yaran nan suka shirya makurcin da Saida ya sakeni, ban San hawa da sauka ya shigo Yanata masifar wai na hana yayanshi abinci Wai bai auro matar da zata hanasu abinci ba, don ma na samu suna cin girkin nawa da ban iya ba? Har da cewa zai ita rabuwa da kowacce mace kan yayansa. Ban San dalilin masifarsa ba, ashe Wai sunce masa bana dafa u Isashshen abinci ranar girkina alhalin bai mana iyaka da store ba.Ba bincike ya shiga tsiya, Ni kuma zuciya ta kawo min wuya ba bata lokaci na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66