Chapter 45
Chapter 45
cikin zafin naman nan nasa "Ki dai tayamu addua please, sai na dawo." Zuwa karfe 12: am Dr Haseeb da sauran likitoci hudun da yake jagoranta sunyi nisa da binciken kwakwalwar patient din, sun Kara daukar awa uku cur kafin su ciwo kan problem din a inda ya yanke shawarar ba sai yayi mata surgery ba, abubuwan da suka yi mata zai taimaka jinin ya rinka gangarowa ta hancinta ana zukewa har yayi clearing. Bayan nurses sun Kai patient din dakin jinyar kuma ya shiga ya dafa kanta ya dade yana karanto adduoin samun shifaa gareta, wannan al'adarsa ce ga patients din sa Kuma Ubangiji na amsar adduoinsa yasa a samu waraka ko da an yanke teammanin samun waraka. Mijin maras lafiyar ya rasa irin godiyar da zai yiwa Dr Haseeb tunda ya shaida masa she's out of danger. Kwarai Alh.Ahmad Sharif ya yaba da kwazon gwarzon likitan musamman ganin irin dedication dinsa kan aikinsa, gaskiya he's very committed to his job.Dr Haseeb ya maida kansa bawa wajen geagwarmaryar ceton rai ko neman lafiyar duk maras lafiyar da aka kawo asibitinsa. Wata damuwa da Alh Shatif ya gabatarwa Daktan shine cewan basu San kowa a garin Kano ba labarin asibitin kawai suka ji ya dauko matarsa suka yo gaba, tunda satinta biyu da yin hadarin, bayan kukkujewa da tayi nan da can ne sai ta fara sumbatu Kuma, barci yai kaura daga idanunta, sai anga sauki abu ya dawo, so wasu ne suka basu shawarar su kawota wajensa. Daktan yace ksr ta Sami damuwa harkar accommodation, asibitin sunyi tanadin guest house dab da asibitin saboda irin hakan.Batun hidimar abinci kuma zaisa matarsa ta aiko. Alh Ahmad Shariff ya fara zuba godiya Daktan ya katse shi cewan musulmi duk inda yake danuwan musulmi ne, Kuma shima an taba taimakonsa. 15/09/2020, 18:50 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 36 Rahima ta kalli agogon dake manne a bangon dakinta, dare ya fara tsalawa, karfe daya harda wasu mintoci amma shiru maigidan bai dawo ba.Ta saki ajiyar zuciya auren likitan kenan, wata rana ma can zai kwana that's why ake son matansu su kasance masu hakuri da dangana. Ta juya gefe, ita ta rasa dalilin da idanunta suka kekashe ta kasa barci bayan na tattare da gajiya. To me ya hanata barci kuwa illa tunanin da ace maigidan bai fita da yanzun suna tare watakila ma a shimfidarta? Oh ni Rahima, shin Ina kunyar Ya Haseeb ya tafi ne har nike irin wannan tunanin?Anya kaunar da nike masa zata boyu kuwa? Barci ya fara fisgarta tana kokarin bude idanu amma ina! Sarkin karfin ya dauketa... Har ya shigo cikin gidan ya shiga dakinta bata sani ba, barcinta yai nisa, yayi kamar ya tasheta ya fasa. Duk da barci take ta Kara yi masa kyau da kwarjini, bai iya tantance tsananin bugawar da zuciyarsa keyi, shin dalilin matsanancin sha'awarta ce ko kuwa so ne ya fara surfafar zuciyar? Tunda baida amsa a lokacin, ya matsa kusa yasa hannu ya gyara mata hannunta data lankwashe tareda shafa kanta a hankali. Jikinta yai dumi amma ba na rashin lafiya ba, duk yadda yaso ya daure abu ya faskara ya duka yai kissing chicks dinta, ta dan motsa kadan taci gaba da barcinta kan dole ya cije ya nufi dakinsa ya kwanta. Qira'ar qur'anin da take yi ya bashi tabbacin ta jima da tashi, shima sai da ya kare nasa ya nufo dakinta yai zaune bakin gadonta yana jiran har ta kammala ta shafa adduointa sannan ta mike cikin natsuwa ta isa dab dashi ta tsugunna. "Ina kwana, ya kaga mai jinyar?" Ta fadi a hankali. "Lafiya lau, jiya ban dawo ba sai muka tabbatar bata cikin wani hadari, insha Allahu zata sami sauki." "Ubangiji ya amince ya bata lafiya, nima da har na tsaya jiran dawowarka unfortunately, barci barawo ya dauke Ni ban farka ba sai asubah." "Yes ai ma shigo na samu kinyi nisa sai na kasa tashinki saboda you were sleeping like a baby, looking so beautiful and innocent, naji kamar in zauna kawai in yita kallonki." Kunya ya kamata "Lah daka sani ka tashe Ni... Ba wani jin kunya ya kalleta yace "Kinsan abinda zai faru da na tashe ki?" Ta mutu a zaune.. Wai me ke damun Ya Haseeb ne yake zaro zancen da bai dace ba? Nauyin jin kalamansa yasa ta kasa dagowa. Ya girgiza Kai yana murmushi yace "Ba ni da amsar maganata kenan?" Ta daga kai alamun amsar sa. Yace "Hhmmm ashe zan zo in fara adduar Allah ya rage miki jin kunyar saboda idan baki saki jikinki dani ba ya za muyi zaman auren kenan?, I mean if you're not free with me ya Zaki lakanci halina, in san naki Kuma?" Tace "I will try my best." "Yauwa haka ya kamata, yanzun taimakonki nike nema kan patient din da aka kawo jiya.... Ya zayyane Mata halinda suke ciki da irin taimakon da yake son yi musu." Rahima tace "Ba damuwa Allah na taimakon Wanda ya taimaki wani. Bari inje mu shirya musu breakfast sai in shirya mu tafi tare?". Ya amsa "Okay, godiya nike." Sun isa asibitin kenan Allah ya nufi Hjy Fatima da farkowa daga barci daidai maigidanta Alh. Ahmad ya shigo cikin asibitin suka hadu da babban likita a nurses station, ya mikawa likitan hannu suka gaisa, Daktan ya tambayesa "Ya kwanan patient din tamu?" Alh. Ahmad ya washe baki yace "Ai naga abin mamaki jiya kamar wani magic wallahi tunda kuka gama dubata baiwar Allah nan ta samu natsuwa tayi barcinta lafiya, ba buge,-buge, ba wasu 'yan surutai da take yi a can inda aka fara dubata. Dr Haseeb yace "Alhamdulillah, yanzun tunda mun samu tayi barcin fiye da awa shidda, brain din ta zama relaxed, yau zamu sake sakata cikin na'ura mu bincika sosai ko da wata matsala a San matakin da zamu dauka, idan iyakar problem din da muka riga muka gani jiyane kawai, mun shawo kanta tun jiya din ma said mu jira karin samun sauki, Allah yasa mu dace." Ya amsa "Ameen Dakta, muna fa godiya sosai Allah ya Kara hasken ilmi." Yana magana ya kalli Rahima yace "Ikon Allah ga wata kamar 'yaruwa." Dr Haseeb ya kalli matarsa, ba shakka irin shigar nata ce tayi ta nannada lapayya, tayi kama da bare-barin, shi ko bata saka shi ba takan yi masa kama da matar kasar Chad. Ya sake bin ta da ido, ya juya yaga yadda Alh.Ahmad ke wani washe baki, kishi ya turnukoshi har yaji mamakin kansa, ya gyara murya yace "Wannan amaryata ce Alhaji ta shigo wajen ita patient din ce at least taji ko akwai abinda suke so tunda ku baki ne." Alhajin ya gintse dariyarsa har dai daya lura da canjin fuskar Daktan, ya gyara tsayuwarsa yace "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin auren, sannu Hajiya." Ta amsa a darare saboda itama taga yadda mijin nata ya hade gira, miskillancin ya taso kenan ta fadi a zucci. "Ina dakin da pateint din take?" Ta tambaya aka nuna mata. Soyayya gamon jini, haka Allah shi ke hada mutaneya sanya kauna tsakaninsu. Mintoci kalilan da shiga Rahima wajen Hjy Fatima Allah ya hada jininsu,bayan sun gaisa suka Dan fara hira a hankali kafin su saki jiki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66