Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

amanar mu kaso ci muna zaune tun baka da komi daka samu shine zaka dauko wata taci arzikin? Da wallahi kun gane kurenku data gwammace bata aureka ba." Rahima ta dafe kai tana dariya tace "Wai ni kaina Ya Hayatu ka yarda da batuna, Kuma na baka goyon baya muddin suka ci gaba da halinsu ka aikata abinda kace daga nan a ga wacce tafi sonka.". Suka taso kamar zasu cinyeta danya dyk da sun san wasa take, Saida ta basu hakuri tace ai ba sauran batun wata amarya tunda kun hada Kai Kunji ance zama lafiya yafi zama dan sarki, muddin za ayi hakurin zama da juna sai kuga Allah na taimakanku, wadata ya sameku, maigida yaji dadin kyautata muku, yaranku su tashi cikin ingantacciyar tarbiyya da kyakkyawar hadin Kai da zumunci da son junansu ga kwanciyar hankali da samun natsuwa.".. Suka ce wallahi mun gane kanwarmu Allah ya ganar da sauran mata Ina alfanun mugun zama, mun gode da shawarwarinki, Allah ya kawo mana suruki nagari." Nan da nan ta bata fuska "Anya zaku same shi da wuri?" Hayatu yace "To aure dai sunnar manzo ne nasan kinsan hakan, mu ba zamu so ki zauna ba aure bayan rasuwar Rabiu ba sai a rinka zargin wani abu." Ta nisa "Ai ba cewa nayi ba zanyi ba, Kai kasan zaman da mukayi da kaninka, Ina zan samu Mai kwatankwacin halayensa?" Jamila tace "Su din dangin gujiya ce, sai an fasa ake sanin na kwarai, ki fasa ki gani Mana." "Na tabbata zata sami Mai gari kuwa, mu dai mun kosa mu sha buki." Tace "Tsokanata ma kuke, bari in shige gidanmu. Ta koma gida tana tunanin hirarsu dasu Hayatu. Aure? Ita har tsoro kalmar ke bata ba don komi ba sai domin rashin cikakken kwanciyar hankalin zabin wanda zai zama abokin rayuwarta da tunanin yadda zata Kara sake koyo kaunar wani da namiji tunda har lokacin bata sami Wanda ma ya kwanta mata a rai ba ko jininsu ya hadu balle a kai ga batun aure.. Maganar abokin marigayin ma bata taso ba don a ganinta da zata aureshin ma taci amanar marigayin kenan duk da ba addini ne ya hana ba, a daya bangaren surutun jama'a fa kasancewarsa saurayi Wanda bai taba aure ba, ita kuwa harta haihu, shin zata iya daure gutsuri tsoman daka iya yiwa auren dabaibayi? Ina batun danginsa, shin zasu karbeta ba tareda wata tsangwama ba,? Ajiye batunsa a gefe shine alkhairi,to Alh. Suraj fa dake da magoya baya irinsu Maryam harda Umma da ta fara shiga ciki, idan bata yi taka tsantsan ba sarkin yawa yafi sarkin karfi lalle suna iya taruwa sufi karfinta, ta tsaya tayi nazarin Alh Surajo lalle yes mutum kamili sai dai ba nan gizo ke sakar ba ta kwatanta kaunarsa a zuciyarta abu ya faskara in ba hakuri zata yi ta auresa hakan Nan ba ta koyi so da kaunarsa yadda tayi na Rabiu amma idan tayi hakan shikenan bata da ranar jin dandanon zakin zumar soyayyar da Maryam ta kwadaita mata kenan? Oh oh Allah gani gareka, kayi min zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwata. Wasa-wasa watanni sun Mika sunyi nisa har ana neman hada shekara da rasuwar mijinta, amma ba amo ba labari ba alamar zata fidda miji cikin masoyanta da suka kasa rabuwa da ita suyi fushi. . Abdul karami har ya shiga nursery, mamansa kuwa ta Kara sadaukar da kanta ne a aikinta, lokacinta na yaran da take koyarwa ne Wanda Allah ya dorawa lalurori iri daban-daban, kullum tausayinsu karuwa yake, kusancinta dasu ya fiye mata komi don haka ta manta shaf da wani batun aure, tunanin zama da wani ya shafe ya goge a ranta. 04/09/2020, 23:29 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami 13 Akai-akai take zuwa gaida tsohuwar sarakuwarta, duk sati ta Kai Abdul yai mata hutun karshen mako, su da kansu dangin uban suka raba yadda yaron zai rinka ziyaryar ko'ina don ya saba da sauran 'yanuwansa. Ko yaushe Rahima ta ziyarci Hajiya saita yi mata fadan kin yin aure, a gida ma tun iyayen nayi sun gaji sun saka mata ido, yaruwarta Maryam ma na irin nata kokarin don ta ciwo kanta su zama matan abokai duk tayi kunnin uwar shegu. Wannan satin Abdul gidan takwaransa yai weekend, ya daukosa ya maido gidan Hjy don mamansa nan zata taho daukarsa kasancewar Zuwaira bata gari. Tunda suka shiga gidan Abdul ke manne da Haseeb yaki yarda ya sauka daga cinyarsa balle yaje wajen kakar Saida tayi masa dabara aka samu da kyar mairo mai aikinta ta goyasa suka nufi wake sannan ya gaisa da mahaifiyarta.. Hajiya tace "Yaron Nan ya shaku da Kai Kwarai da gaske.".. Ya amsa "Haka kowa ke Fadi, gashi yana jin maganata ko rigimar banzan sa ya fara yaki sauraren kowa Ina masa magana zai daina." Tayi shuru cikin tunani kafin ta furta "Daman Rabi'u yace danka ne dole yaji maganarka." Yace "Dalili kenan da in har ya gama nursery mamansa bata yi aure ba zan karbi dans kawai tunda daman an bar mata shi bisa yarjejeniyar zamu amshi abinmu ne idan zata sake aure to tunda ba alamun hakan gara mu karbeshi kawai." Ta zaro ido " Zaka tayar mata da hankali, da wanne zata ji, yaron nan shi take gani tana jin sanyi, idan an nuna mata fun karfi a kansa zaku dau hakkin yarinyar Nan." Ya bata fuska "Ai munyi mata Kara Hajiya, Ni ke, 'yanuwanta ita kanta da sauran jamaa sun san haka sai dai in za aki gaskiya." Ta daga masa hannu "Naji, naji meye hujjarka na son amsar sa?" Ya gyara zama "Hujjata ya dawo cikin 'yanuwansa ya zauna gaba days ba a rinka yawo da hankalinsa ba, Kuma ke da kike wannan magana da zaran ita iwar tasa ta sami miji ba dawo mana dashi za a ayi ba?" Ta dade Bata ce dashi komi ba zuwa can tace "Hakane na amince da batunka amma Ina ganin da abinda za ayi a magance wannan matsalar ta bangarenmu da na uwar yaron saurara: Ni a hakikanin gaskiya tunda Allah ya amshi ran danuwanka nike tunanin baka shawarar auren Rahima.... Bai bari ta karisa bs ya buga kirji ya zabura kamar zai tashi tsaye ya koma ya tsugunna jikinsa ba inda baya rawa, ya kama kansa da hannu biyu ya rinka jinjina maganar a ransa, nan take idanunsa suka rikide suka canza launi maimakon farare sol, ya bude baki yai magana kalmar ta kasa fitowa ya koma ya zauna yaraf saboda matukar sanyin da jikinsa yayi sai kace Wanda ya kwana ya yini Yana aikin wahala ba ci ba Sha. Ta dauki tsawon lokaci kafin ta kallesa da kyau tace "Maganar da nai maka na auren ne ya firgita ka har ka fita hayyacinka?" Yaja dogon numfashi ya saki ajiyar zuciya, sannan ya dago Kai a hankali ya kalli mahaifiyarta yace "Hajiya idan ma auren zan kara in rasa wace zan aura sai matar kanina da ya rasu, ki tuna yadda muke dashi fa, idan anyi hakan ba a kyauta ba." Ta danyi murmushi saboda tayi niyyar hada auren nan ikon Allah ne kadai zai hana yuwwarsa. Tace "Ni kuwa a nawa tunanin yadda kuke da danuwan naka ne zaisa ka

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66