Chapter 58
Chapter 58
lafiya balle a samu piece of mind da kike ikrarin za a samun." "Ni fa har yanzun ban fahimci manufar maganganun ka ba, karata ta kawo ko me?" "No, na dai yi zaton sanin halin Zuwaira da kika yi zai hana biye mata shiriritar ta." Ta danyi murmushi "Idan ranka ya baci afwaan ba za a kara ba. Kamar yadda na fahimci halinta tun ranar dana fara ganinta, na lakanci tana cikin mutane extrovert, wadanda masu sanin halayen Dan Adam suka ce yawancinsu akwai su da shishshigi, karancin basira, wasu su hada da karya da kwadayi, son shigewa gaba kan al'amurra ko wanda bai shafesu ba, su Kan nunawa jama'a sun san komi irin yadda take nuna min, ni Kuma idan naga zata kureni sai in nuna mata ba hakan bane, nan muke samun tangarda. .. Yace Fahimtar banbancin halayenku ita mai yawan surutu ke Kuma introvert nasan ba wani dadin zama za kuji da juna ba." Rahima tace "Ni kuwa sai Ina ganin har ta fara canzawa, cikin dabi'unta marasu kyau na lura sun ragu sosai. Ka dai ci gaba da yi mana addu'a wata rana sai labari l." Ya nisa yace "Gaskiyar Kuma nima na lura da hakan but na kasa accepting cewan zata canza, Allah yasa ta dore." Rahima tace "In Sha Allahu, duk ranar da Allah ya ganar da ita influence din kawayenta ba alkhairi bane zata natsu." 19/09/2020, 22:40 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami 48 Dakta yai shiru yana kallon matarsa yana yaba halinta cikin zuciyarsa. Hakika yaga canji wajen Zuwaira, tun yana mamaki har ya daina yaci gaba da sa ido yana lura da dabbin dabi'un data bullo dasu, misali gabatar da sallar asubah ba tareda makara ba shine babban canjin da yai masa dadi a ransa,ta rage yawo kusan rabon da tace zata bukin kawa ko aminiya ya manta, business din ma yayi sanyi ba kamar da ba, yaranta suna samun kulawarta sakamakon ganin irin kaunar da Rahima ke yi musu da yi musu tarbiyyar kwarai, shi kansa yasa mata dokar hana kaisu ko'ina da sunan a barsu can, sai dai a kaisu su gaida kakanninsu da yanuwa direba ya dawo dasu. A gaskiya problems din da yake fuskanta da ita sunyi sauki sosai thanks to beloved Rahima, matsalar data rage yanzun shine yadda Zuwaira ta shafawa idonta toka taki amincewa zuciyarta matsayin Rahima na da can da wanda Allah ya kawota a yanzun, sai dai inda yake jin sanyi Rahima ta daure kowanne cin Kashi da Zuwaira ke mata, inda take Burgesa ma duk iya masifar Uwargidanta ba dai kaji bakinta ba, sai dai na Zuwaira wace takan Kara masa gishiri tace anyi alhalin ba ayin ba. Ta dan bugi hannun kujerar da yake Kai tace "Lafiya kayi shiru haka cikin zurfin tunani?" Ya juyo ya dau glass dinsa ya manna a fuskarsa ya sakar mata lallsusar murmushinsa yace "Just thinking of how lucky iam to have you in my life." Tayi dariyarta mai fitar da kyawawan jerin hakoran ta cikin shagwaba ta "Ya Haseeb kenan, godiya nike sosai." A can cikin dakinta Zuwairan Dakta ta zauna tana cizon yatsarta cikin damuwa domin kissar data shiryawa Rahima kamar kullum bai yi wani tasiri ba. Gaskiya yarinyar akwai dan Karen wayo, duk wani plan data shirya don taga downfall dinta sai dai ya wargaje ko ta wargajesa cikin ruwan sanyi. Gaskiya da sake lale, ba zata zauna ace Rahima ta kwace mata miji ba. To me rage, me yai saura? Matar da babu irin kissa da kisisinar da bata kware a Kai ba, matar data iya hilace miji ta hanyoyi daban-daban? Sai dai ita kanta ta amince Rahima mace ce Mai matukar ladabi da biyayya halayen da kowanne namiji ke so wurin matarsa, to ko wadannan halaye basu isa su mallaka mata mijinta ba? Ga yadda taji labarinta tun aurenta na farko Rahima bata yiwa mijinta musu, duk abinda yace fari ne zata tas kuwa koda kuwa baki ne za tace yafi nono fari. Bayan haka ko taso ko taki Rahima macece mai hakuri mai son zaman lafiya da kowa bata son tashin hankali sam amma bata daukar raini, to ita yanzun ya zata yi? Tas ta gama amfani da magunguna da Husaina ta kawo mata bata ga wani canji ba, Husaina bata da mutunci ga wata gurguwar shawara da take bata wai ta rabu da Haseeb, hhmmm da ne zuciyarta ta rinka gigin yayo mata wannan mummunar tunanin, but ta rabu dashi ta auri wa? Ina zata sami kamarsa? Ita kuma don sakarci ta rinka daukar shawara... Zuwaira ta muskuta a gado taci gaba da tunani, to yanzun data gane kuskuren biyewa Husaina wane mataki ya dace ta dauka don mallake zuciyar mijinta irin Rahimar? Gidan malamai? Ta girgiza kai, no ba ya cikin dabi'a ko tsarinta, tayi saurin kawar da wannan, bata yarda da yawon gidajen bokaye Rahima ta shigewa Haseeb zuciya tayi daram ba, to meye sirrin? Inganta tsabtar jiki da tufafi da muhalli ko kuwa iya sarrafa dadad'an nau'ikan abinci? Kai ah ah wadannan kadai basu isa su mallaka mata zuciyar gwarzon namiji irin mijinta ba. To ko kuwa kamun kai da rike mutuncinta ne silar suka zama silar zama 'yar gaban goshin sa? Shin Ina zata gano sirrin don itama ta kwatanta taga ko zata ci riba tayi nasara mijinta ya rinka kaffa-kaffa da rawar jiki da matar da a da yake nuna ita din dole ce tasa ya aureta? Kafin ta samo amsarta ya dace tasan ita macece , tasan martaba, kima da darajar da Allah yai Mata, to idan ta zubar da mutuncin nata tuntuni fa, yanzun ne take son tattaroshi ta kwaso ta zama equal da Rahima fa duk da hausawa sunce mutunci madsra ba a barinsa a kwashe duka? Nan take hawayen nadama suka fara gangaro mata, tabbas mijinta yai hakurin zama da ita, da wani ne da tuni ya koreta amma ya daure ya riketa duk da yasan illolin dake tattare da masu irin halinta, oh ni Zuwaira Allah ka shiryar dani hanya madaidaiciya ka hana min ci gaba da aikata sabonka,ka yafe min dimbin zunuban dana jibgawa kaina. Babu wani abinyi yi a gareta illa ta roki mijinta gafara kana taci gaba da istigfari, tsayuwar dare da azumin nafila ko Ubangiji zai ji kanta ya yaye mata matsolinta, ciki harda rokon Allah ya mallaka mata zuciyar mijinta, to bangaren Rahima fa? Ya zan dole ta ajiye duk wani kishi da kyashi da hassadarta su zauna lafiya ko ta Kara samun haske daga gareta wadanda zasu gyara mata al'amurranta. An dade da fara Kiran sallar magrib kafin ta dawo hayyacinta tayi hanzarin dauro alwala ta gabatar da sallar kana taci gaba da istigfari har aka Kira isha'i, ta mike ta gabatar ta sallame ta yi adduoinnta ta shafa. Kafin maigidan ya dawo daga masallaci ta shiga wanka ta fito ta canza ado ta fito da kayan abinci, tana harhadawa ya shigo falon tareda su Khalifa harda Abdul, suka zauna suka ci abinci suka kare, bayan sun wanke baki da hannu ta kallesu tace "Kun ga ku tafi sashen Aunty Rahima ku ce Ina gaisheta " Yara suka dubeta galala Kuma basu tashi ba to basu taba ji tace hakan ba,Saida ta maimaita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66