Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

ba sai kuga kowacce ta fito tana kuri da fankamar ita yafi so. Idan anyi dace da irin mazan da suka san ciwon kansu sai kiga su zaman lafiyar suke matukar bukata a gidajensu, idan Allah yasa ya dace da matan kwarai sai sai ya kula dasu matuka ya rinka kyautata musu har kiji danginsa na fadin sun mallakeshi sun gama Mana dashi alhalin jin dadin zaman lafiya da kwanciyar hankalin da yake samu dasu ya haifar da hakan. Kin ganni nan Maryam bana shakkar zama da kowacce irin mace Allsh zai hadani da ita matsayin kishiya." Ta gatsina baki "Karki cika baki Rahima, me kika sani game da zama da kishiya, kowacce mace fa da nata salon munafunci da kisisinar data kware, idan an debe masu shige-shigen gidan bokaye da malamai don wata ba zata zauna dake da bakin hura wuta kadai ayi kishi ba." Tayi murmushi "Aunty Maryam kenan ai ba wani cika baki, in har hakane Kuma Ina iya ce miki yes na cika baki ne domin nima da nawa baiwar da Allah yai min, ba wani abu bane da ya wuce kakkarfar madogora." Ta kada Kai "Ko Zan San wane irin madogara ne?" Ta girgiza Kai "Nima ki bini bashi zuwa nan gaba in har Allah ya kaddareni da auren kiga matsayins zamana a gidan mijin da wajen shi kansa mijin tukunna, yanzun dai muyi sallar isha'i ki bani amsar tambayata ta tuntuni don Ina jin ga wannan karon na fada kogin nan na so da kauna sai dai ko za ku iya tsamo ni?" 06/09/2020, 19:35 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 16 Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake. Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta. Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da 'yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa? Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace "Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra'ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki " Ta gyada Kai "Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa." Yace "Lalle kin cika 'yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya.".. Tace "Godiya nike sosai Allah saka da khairan." Yace "Ba komi Rahima." Goma da mintoci har Maryam ta fara barci Rahima ta tashe ta "Barci tun yanzun?" "Yes tunda ranar hutun kenan da Alhajin ba nan yake ba." "Kina nufun idan yana nan ba Kya hutawan?" Ta amsa "kusan hakan ne kina wasa da Alhajin nan da kike gani, wallahi duk ta sangarce, daidai da spoon bai iya dauka da hannunsa ya Kai baki idan ina kusa." ."Su soyayya masu gari." Maryam ta gyara kwancita "Karki zargeni, ke din wa yasan abunsa za kiyi nan gaba, ya kuka kare da Alh Suraj?" Rahima ta sanya rigar barcinta kafin ta amsa "Na fada masa gaskiya yai accepting wai sai Kun Kai masa Iv." Maryam tace "Ko nifa bana amince dashi bane just tsokanarki nike da naga baki da niyyar fidda kowa, yanzun shi Wanda Hajiyar tayi magana ne a fagen?" Wani irin murmushi da farin cikine suka bayyana a fuskarta, Maryam ta daki kafadarta da matashi tace "Lalle wannan ya samu karbuwa a zuciyarki, fada mini ya kike ji?" Saida ta kwanta ta tasa kafadarta da matashi tace "Za kiyi mamaki Yaruwa domin nima cikinsa nike, ashe mutum Kan so Wanda bai taba gani ba, ni fa ko sunansa ban sani ba, labarinsa ma not in details naji amma na kagu na kosa in gansa inji yaya zanji ranar dana fara ganinsa?" Tayi dariya "To ya zaki kwatanta abubuwan da kike ji yanzun da wanda kika ji game da marigayi." Ta tashi ta zauna "Ai sun Sha banban 'yaruwa, son Rabiu a hankali ya riga shigata kwatankwacin mutum ta dora ruwan zafi bisa wuta, a hankali ya fara dumi, ya kai ga zafi har ya nuna alamun tafasa sai wutar ta mutu, to yadda ya fara zafi hakan ya rinka hucewa yana sanyi a hankali har ya zamto yanzun na hakura, dana tunasa adduar samun rahama nake ci gaba da yi masa kullum, wannan kuwa gaba daya ruwan ya dau zafi, kafin in ankara har ya tafaso ya fantsama koina, zuciyata na kuna, babban abinda ke firgitani addua nike lamarin na kara tsanani, ko yanzu ji nike kamar in rufe ido in gansa a gabana don inga wane irin mutum ne da yai saurin raunana min zuciya?" Maryam ta gyara "Tirkashi! Babbar magana, Lalle lokaci yayi da ya dace in baki amsar tambayarki akan menene so? To a iya fahimtata soyayya itace ni'imar mafi daukaka da Ubangiji yaiwa bayinsa baiwarsa, soyayya itace zuciyoyi dunkule ko a cure waje guda, abin nufi idan mutum yaso wani ko wata son nan kesa ko yaushe a kasance cikin tunanin masoyi, rashin damuwa da kowa sai shi/ita, mutum yakan zama bai jin son ji da ganin kowa sai masoyi kamar yadda kika kasance a halin yanzun. Ba abinda so bai haifarwa, so na sa mutum yai hauka ya zauce, idan zuciyar bata samu abinda take so ba ta Kan fita hayyacinta, tayi rauni wani har sai an hada da addua kafin a sami komawa normal. So kansa mutum yanke hukuncin da bai Dana sani matukar ya shafi masoyin, a cikin lamarin so na hakika babu shakka, ba munafunci ba yaudara, ba karya balle zargi, so nasa masoyi tsananta addua ga Wanda yake so ko da sani ko basa saninsa ba. Mutum Kan gane ya kamu da son wani/wata ce ta faduwar gaba a duk lokacinda aka ambaci sunan masoyi, ko gani a zahiri, hoto ko murya. Zaki yawaita son ambatonsa ko son kiji ana labarinsa ko hirarsa, zaki rinka jin son sirrinsa maana halinda yake ciki, jin dadin zancensa, tausayi, fadar gaskiya, nisantar karya in har son na gaskiya ne, haka nan zaki rinka yaba kyautarsa komin kankantarsa da son kema kiyi masa alkhairin komin yawansa,

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66