Chapter 41
Chapter 41
ba although ya tabbatar da zasu gina rayuwar aurensu kan kyakkyawan kudiri saboda ya amince da ita duk da babu wata akaka ta soyayya tsakaninsu. Ya ji shuru bata fito ba, ya dau waya ya kirata cewan yana son ganinta a falonsa, kafin ta fito ya kagu da son sake ganinta da tsarin kwalliyarta, tayi masa kwarjini kwarai a fuskarsa. Bata fito ba saida ta saka hijab, ta isko shi tsaye gaban aquarium ya gama baiwa kifayen dake ciki abinci, ta danyi murmushi, ashe ra'ayinsu ma dayane wajen kaunar kiwon kifaye.. Bayan ya amsa sallamarta ba tare daya dago ya kalleta ba yace "Zauna mana." A natse ta zauna a takure tana kara yaba tsarin falon likitan, idanunta suka Kai kan babban hotonsa dake manne a bango da hoton tsohon shugaban kasa Sani Abacha. Shima din yazo ya zauna kujerar dake fuskantar ta yana kallonta ta kauda Kai, ya sauke ajiyar zuciya "Kin san illar tunani kuwa?" Ya tambayeta "Tunani yin kansa ya keyi ai balle Kuma idan mutum nada reason na yi din." Yace "Hakane, but na Kira kine muci abinci." "Ni na koshi gaskiya." Ya ci gaba da kallonta kanta a kasa dai ya ce "Ya za muyi kenan, bana cin abinci Ni kadai Kuma Ina jin yunwa ke Kuma kin koshi a cewarki, in hakura kenan?" Tana jin haka ta dago suka hada ido, zuciyarta ta buga da karfi saboda tun saninta dashi bata taba ganinsa ba glass ba, da ya cire sai ta fahimci yafi kyau da kwarjini, his gazing eyes sai haske suke yayinda yake kallonta.... Ta lumshe nata idanun ta budesu da kyar tamkar Mai shirin yin barci, Daktan yaji tsigar jikinsa ya tashi, shawa'awar amaryarsa ya diran masa a kahon zucci Wanda yasa ya manta da matsayinta na da can sai matsayin matarsa. Cikin rashin kuzari dalilin kasalar data taso ta lullubeta ta mike a hankali ta nufi dining table ta kwaso warmers din data jera ta maido su gabansa ta ajiye a bisa carpet kana tace "Ina rokon arziki ka sauko kaci komi kankantarsa. karka kwana da yunwa." "Bana magana biyu Rahima, as long as ba za muci tare ba na hakura." Ba yadda zata yi dole ta sauka ta zuba musu abincin a plate guda bisa umurninsa. Tafdijan ita bata taba cin abinci da namiji plate daya ba, ko Rabiu kuwa, dole haka ta daure cikin jin nauyi ta rinka tsakalar abincin, shima ba wani ci yayi ba sai uban nacin kallonta da yake duk ta tsargu kamar ta tashi da gudu ta bar falon. 14/09/2020, 17:50 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 32. A takaice tare suka ci abincin suka gama ya tayata kwashe kayan zuwa kicin, niyyarta ta shige daki ta kwanta yace yana son magana da ita.. Suka koma falon suka zauna, tsawon lokaci bai ce komi ba, shi fa problem dinsa kenan, banbancin su day Rabiu karara ne yaushe shi zai tsaya yana jan aji kafin yai magana? Duk kokakarinta na avoiding tunanin Rabiu yaci tura. To wai me zai gaya mata nema yake wani shan kamshi kafin ya furta? Ta rinka motsi da kafafunta don ya gane ta matsu bai kula ba. Ita bata taba ganin mai kyuyar magana kamarsa ba, ashe kuwa za ayi zaman kurame, don idan takamarsa miskillanci gidan ya taras. Shin ko nauyin abinda zai fadin yake? Zuciyarta ta bada dam! Ba dai yana tunanin irin kusancinta da marigayi ya kasance tsakaninsu ba. Tafdijan! Aiki jawur!! Tunanin hakan ya haifar mata da damuwa maras misali, hawayen data rinka kokarin dannewa suka kubce suka fara gangarowa,sheshshekar kukanta ya zaburar da shi daga duniyar tunanin da ya tafi, nan take zuciyarsa ta shiga kuna don ya fahimci zubar hawayenta bai rasa nasaba da halinda suka tsinci kansu a ciki na *Mata* da *Miji* wanda iya dakewan mutum sai ya bara. Sai dai shi ya daukarwa kansa alkawarin rike Rahima da danta bisa amanar da kaninsa ya damka masa, yayi saurin ciro white hankerchief cikin aljihunsa ya share kwallar da suka ciko masa, ya zabura ya mike ya nufi fridge ya bude ya dauko fresh milk ya tsiyaya a 2 cups ya matsa kusa da ita ya mike mata 1cup "Sha madara ya sanyaya miki zuciya." Ta karba ta kurba sanyin ya ratsa makoshi ya shiga cikinta, ta rumtse ido ta bude sannan ta sake kurba kadan ta rike sauran a hannunta... "Rahima ya kira so, softly,. kamar ta cikin kunninta ya rada mata sunan har tsigar jikinta na tashi, ta kasa amsawa, ya sake Kira ta daga masa Kai alamun tana jinsa...tausayinta ya kamashi yayinda yaci gaba da magana kamar yanayi da karamar yarinya "Don Allah ki daina kukan nan, i hate to see a woman crying. Ina rokon ki kwantar da hankalinki kan al'amarin nan da Allah ya kaddaro mana, ba da yin mu bane, rubutaccen al'amarine Ubangiji ya kutso da hikimarsa ta wajen Hajiya, mu Kuma muka yi mata biyayya don bamu isa mu kauce abinda yai nufi a garemu ba, don haka hakuri da tawal'u ya dace muyi da duk wani tunani da ba zai haifar mana da komi ba illa damuwa. Nasihar sa ya shigeta sosai ya haifar mata da karin fitar hawayenta, ya kalleta "Oh my God! Ya furta cike da damuwa yayinda ya taso da hanzari ya iso gareta, ya mika hannu tamkar zai rugumota, ya taka burki yayi reverse tareda girgiza kai ya shiga yawo a falon yana ci gaba da rarrashin ta. Kamar yana Kara mata volume, cikin kukan tace "Nasan kaddara ce amma wallahi na kasa daurewa... Yayi saurin dakatar da ita "Karki bari bacin rai yasa ki kauce hanya ki kai ga sabo please, tunda har kin amince a barta a haka mu ci gaba da adduoin Allah ya yaye mana kuncin dake tattare damu, ya karemu daga dukkan sharri ya kuma tabbatar mana da alkhairin dake cikin aurenmu." "Ameen ya Hayyu ya Qayyum." Ta amsa murya can kasa Yayi dan murmushi yace "Nagode and in Sha Allah nayi miki alkawarin you'll never regret this marriage, yanzun kije ki kwanta ki huta kin sha aiki yau, gobe in Sha Allah zan daukeki muje gidan Zuwaira mu dauketa muje wajen Hajiya, in lokaci bai kure ba mu wuce har wajen su Umma da rijiyar Lemu da Galadanci." Tace "Duk yadda ka tsara hakan za ayi." Yace "Ki dai yi tunani, oh sorry na hanani dukkan wani tunanin da zai saki kuka, no more tears." Ta amsa "Zanyi kokarin daukar shawararka, nagode." "Ni ne da godiya ai, sai da safe kenan." Ya amsa mata wannan karon fuska a sake. Tace "Allah ya tashemu lafiya. Nan ta barshi tsaye ta wuce dakinta. Maimakon su kwanta kamar sun hada baki, kowanne daura alwala yayi cikin daki suka fara jera nafiloli da adduoin samun ingantacciyar rayuwar auren da tsabtatacciyar soyayya, kowanne yaiwa marigayi adduar samun rahamar Ubangiji sannan kowa ya kwanta barci. 14/09/2020, 17:51 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 33. Sun tashi cikin farin ciki da annashuwa tamkar basu suka kwanta cikin kunci da damuwa daren jiya ba. Bayan ta gama azkhar dinta ne ta nufi kicin domin hadawa maigida abincin kalacinsa da hannunta musamman da ya kasance tun suna gida ita mai sha'awar girke,-girke ce har sukanyi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66