Chapter 32
Chapter 32
halinda ake ciki. Malam yai murna ya shiga yi masa nasihohi musamman kan kwatanta adalci tsakanin matan daman tsoronsa kenan tunda yaga yadda mahaifinsa yaiwa Mahaifiyarsa. Malam ya Kara masa da shawarwari da adduoin fatar alkhairi da neman jagorancin Ubangiji. Yana Kan hanyarsa ta komawa gida yana mamakin irin na'am da farin cikin da kowa keyi Kan wannan auren, zuciyarsa ta Kara karfi, nan bisa hanya ta fara tsara yadda yake son a tafiyar da sha'anin amma har sai ya isa gida yaji ta bakin Zuwaira da ita kanta yarinyar da akeyi dominta. 10/09/2020, 06:02 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami 23 Karfe goma sha daya na dare ya isa gida amma har zuwa lokacin Zuwaira bata koma ba, ya tube ya shiga wanka ya fito ya hada ruwan shayi tukunna kafin ya zauna kallon tv Sai sha biyu saura na dare yaji maigadi na bude mata gate din gida ta shigo da motarta. Ko da ta shigo falon bata lura yana kwance bisa settee ba, tana tafe tana 'yan wake-wakenta, sai wani irin kamshin turare Mai shegen haea Kai take, har zata wuce bedroom ta gansa taja ta tsaya masa kerere bisa Kai "Oh ashe ka dawo ban lura da motarka ba." Ance tankawa yabawa biyan bashin matsiyaci, bai ce Mata uffan ba, ta fasa shiga ciki ta dawi ta zauna kusa dashi ta fara kame-kame, kusan minti biyar tana ta surutu ba tareda ya tanka ba ta gaji tayi shuru. Ya kalli matar da suka shafe shekaru fiye da takwas da aure Amma m har zuwa lokacin Nan bai San dadin auren ba, bai San me zai karas ba, ya kanji dai abokansa na hirar hidimar da matayensu keyi musu. Ya sake kallonta ya rasa me zaice Mata, to bata jin wa'azi, in anyi mata fada ta tashi tana masifa tace an tsaneta, idan aka rarrasheta ta zake har tafi da don haka ya zabi yin biris da ita kawai yafi masa alkhairi ya ci gaba da yi mata addua Da taga yaki ce mata komi ta mike zata shige ciki harda sakin dogon tsaki... Takaici ya kamashi kawai ya sakin mata bom "Zuwaira Ina sanar dake Zan Kara aure." Tayi wani irin juyi gaba daya, hankalinta ya dawo garesa sosai taga Yana kwance lakadan kamar bashi ya furta Mata wadannan kalaman masu dacin gaske ba, ta buga kirji "Aure! Aure fa kace?? Ya amsa "Kwarai ba kince gara inyi ba zai fi Miki nono fari?" Ta sake buga kirji "Ni din wace sakaryar macece zata ce da mijinta ya kawo Mata kishiya?". " Sai ke Kuma shawarar taki na dauka." Amsarsa ya sake tunzurata "Oh ashe zargina ya Zan gaskiya da wace ka aje a waje that's why kake wulakanta ni kana nuna min halin ko in kula." Yace "Ni ban wulakanta ki ba, ban Kuma ajiye kowacce mace a waje ba don Ni ba fasiki bane." Tayi tafi " Abokiyar yin naka dai zaka auro a tahi a cakuda min 'ya'ya da shegu." Ya tashi daga kwance da yaji zata wuce gona da iri yace "Kinga karki batawa yarinyar mutane suna, ba wata daban da baki sani ba Zan aura, ai kinsan Rahima maman Abdul ko,Allah yai nufin ita Zan aura " Taji dum amma hakan bai hanata yin shewa ba "Ahayye girma ya Fadi, su Yaya babba anji kunya, to daman kace ka gani ka kyasa tuni ba damar yi masa snatching ne da ransa, yo Ashe duk shan mur da kau da Kai na munafunci ne ana so ana kaiwa kasuwa, to me yasa tun farko bka aureta ka barshi ta aureta. Gaske naga danta ya zama dan lelenka sabida son uwa ke sa na d"a. Amma wallahi ka ban mamaki ka bani kunya, ka rasa matar da zaka aura sai matar kaninka Haseeb, wannan abun kunya dame ye kama?" Maimakon yaji haushin magsnganunta dariya suka bashi yace "Zuwaira wane irin kunya Kan abinda addininmu ya halasta bayan kinsan ance babu kunya a addini? Abinda ya halasta ne mu mutane muke haramtawa kanmu sabida jahilci, to in ba tsintsar jahilci ba Ubangiji ya halasta abu Kai bawa ka kawo al'ada da wasu shirme ka gindaya? So ki fahimci akwai aure tsakanin wa da matar kaninsa idan ya rasu za Kuma ayi shine na sanar dake don shi Alhajinku ma rokona yayi ayi da wuri Kar a dauki lokaci, to na bi shawararsa sai kije kiyi tunanin me kike bukata inyi miki ma fadar kishiya? Ta tabe baki "Idan duk jikina kunnuwane ba Zan taba yarda cewan Alhajinmu da kanshi zai goyi bayan ka yiwa diyarsa kishiya ba. "Me zai hana tunda diyar bata neman albarka bata faranta ran iyayenta?" Ta balla masa harara "Don zaka auro wannan yarinyar ce kake fada min magana?" Yace "Ke Kika ja yai nisa, and ki bar tunani cewan yarinya karama zan auro shekaru nawa kika bata?" Ta gatsina hanci "Yo Ashe ma tsohuwa ce kake wannan rawar jikin da dimirgishi Wai dafa kauri ba da." "Nima ai tsohon ne tinda na na Kai 41 yes Kinga za mu yiwa juna daidai kenan." Ta kallesa ta watsar "Kaji dashi Wai ciwon ajali a Dan yatsa." Ya dagi ya kalleta "Please shiga ciki ki kwanta kin dameni da surutu sai da safe." Tayi kwata "Surutu yanzun na bude chapter sai dai Kuma idan dinke bakina za kayi tunda baka da tausayi a zucci ka yanka ka dinke, Kuma gobe gidanmu za ni." Ya amsa "Allah ya Kai mana rai suma nemanki suke kije kije ki kwaso yaran da kika zube a can tamkar basu da gata." Yana fadin haka ya gyara kwanciyar sa nan alamun ba zai ma shiga bedroom din ba balle taci gaba da bala'in. Ta gaji da zama taja jiki ta nufi ciki tana Kun kunai kamar wata yarinya karama. 10/09/2020, 12:29 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 24 Gari na wayewa ko wanka bata yi ba tana idar da sallah ta nufi gidansu, Kai tsaye ta wuce dakin mahaifiyarta, Hajiyar na zaune tana lazumi don al'adarta kenan. Ta dago taga Zuwaira ce taci gaba da karatunta ba tare da sake kallon inda take ba, ita kuwa ta haye bisa gadon uwar ta kwanta. Ba a jima ba taji muryar mahaifinta ya shigo yadda yake yi duk safe ya zagaya dakin kowacce mata yaga yadda ta kwana tareda iyalinta yaji ko tana da wata matsala su tattauna hanyar da zasu bullowa al'amarin. Ya zauna falon uwargidansa Hjy Lami yana jiran ta kare adduointa, Zuwaira taji muryarsa ta taso ta fito ta durkusa ta gaishe shi. Ya kalleta cike da mamaki "Ba dau Zuwaira nike gani yanzun ba, tun yaushe kika shigo gidan Nan?" Ta sunkuyar da kai tace "Ban dade da shigiwa ba, ina kwana?" Ya kalli agogon hannunsa yaga ko karfe takwas bata cika ba cikin tsawa yace "Wace irin sakayyar yarinya ce, ki baro gidan mijinki tun sassafe ki zo me zaki dauka?" Ta marairaice "Karansa na kawo Baba, wallahi duk ya canza, yanzun ma wai aure zai yi, da karya ma har yana cewa ka bashi goyon baya?" Uwar ta shafa adduarta ta fito ta durkusa gaban mijinta ta gaisheshi ya amsa kana cikin bacin rai yace "Ya akayi kika Kyaleta a zauna har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66