Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

son ayi masa biyayya, bai daukar jita-jita, baya son girman Kai ko nuna Kai wani ne, bai taba daukan kansa wani abu ba, Yana son hira da Wanda ya amincewa, idan har an zauna dashi mutum ne da ake karuwa dashi ta hanyoyi da dama, Allah yai masa laqanin iya zama da mutane. Haka nan yakan kaunaci duk Wanda ya nuna masa kauna ya Kan guji makiyinsa cikin kowanne hali. Dr Haseeb mutum ne Mai tsananin kusantar Ubangijinsa, wajen ibada da adduoi neman taimakon Mahaliccinsa a dukkan al'amurran da suka jibanci rayuwarsa, bai Kuma taba tunanin Ubangiji bai amsa bam Ranar da Mahaifiyarsa tayi masa batun auren matar kaninsa Rabiu ya razana sosai, batun ya dameshi ya tsaya masa a rai matuka, amma damuwar data fi masa ciwo itace yi mata musu sabida in har yana kaunar mutuwarsa to zai so abinda zai bata mata rai, baya kaunar abinda zai sosa Mata rai ko kadan. A kullum yana danganta samun nasarar da yake a rayuwa da dimbin adduointa ne garesa bayan albarkar da take sa masa kullum. To yanzun data gangamo aure, auren ma na wace ko a mafarki bai taba tunanin faruwarsa ba ya zaiyi da bukatar ta? Ba wani abinyi illa amincewa da bin umurninta da fatar Allah yasa ya zame musu alkhairi duka. Amma ya yankewa kansa the most difficult decision in his life duk da bai yanke shawarar ba sai da yayi adduoi kamar yadda ya saba ya roki Ubangiji fa'ida kan al'amarin, da alamu akwai haske sai kara neman taimakon Allah. Tunaninsa ya koma Kan yarinyar ko yace matar da ake son ya auran, zuciyarsa ta amince Rahima yarinya ce mai natsuwa da hankali, tanada biyayya tunda bai taba jin ance wani sabani ta shiga tsakaninta da marigayi ba, yasha jin irin yabawar da Hajiya ke Mata, yasan yadda ita din take girmama Mahaifiyarsu wanda mutuntata da take yi me ya Kara haddasa son hada wannan auren. Idan ya tuna yaronsu Kuma, Abdul ya shaku dashi, shima jaksn fiye da 'ya'yan cikinsa ma wanda bai rasa nasaba da matsalar uwar yaran da tafi son 'ya'yanta su yini su kwana a can gidansu fiye data kawosu wajen Hajiyarsu. Da ya nuna rashin amincewarsa ta kawo masa uzurin sunfi sakeea a can saboda akwai yara sa'oinsu Kuma tunda shi ba mazauni bane meye na complain. Yan kwanakin nan da Hajiyar ta diba masa ayyuka sunyi masa sauki don hakane ya Sami daman yin nazari da adduoinsa a natse, ysi reaching decision don haka bai bata lokaci wajen dumfararta da shawarar da ya yanke ba. 07/09/2020, 23:52 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by Jami 18 Ganinsa tunda sassafe a Rana ta takwas da yin maganarsu baisa ta saki fuska, ya durkusa ya gaisheta ta amsa a dakale. Daga can cikin uwar daki Abdul yaji muryar babansa ya tashi daga barci ya fito yana mutsuke idanu, Haseeb ya riko sa ya zaunar dashi cinyarsa ya rungume ya kalli Hajiya yace "Ashe har yanzun bai koma ba?" Tace "Mamansa bata zo ba Ni kuma ban aika ba.".. Ya kalli yaron da kullum idan ya hansa sai ya Tina da danuwansa, ya kada Kai tare da kara rungumarsa, nan da nan ya koma barci, Hjy Kaltume tace "Wannan shakuwa taku tayi yawa, muryarka fa yaji yasa ya taso barcin bai ishe shi ba." Ya kada Kai hakane, ba a kaishi makaranta ne naga har kusan tara yana barci?" Ta amsa "Yana zuwa mana ka sani, bai jin dadi ne tun jiya da dare ya kwana zazzabi har yana firgita yana Kiran uwarsa Yana kuka." Ya dafa kansa "Ashsha subhanallah, ya taba jikinsa, gaskiya har yanzun da alamun zazzabin ko asibiti za a kaishi?" Tace "Nima tunanina kenan." Ya Kara duba shi Kuma yace "Ba sai yaga likita ba idan yasha magani ma zazzabin zai sauka bari inyi masa addua yanzun." Dr Haseeb ya dafa jikinsa ya karanto *BISMILLAHI A'UZU BILLAHIL AZEEM MIN SHARRI KULLI URQIN NAARIN WA MIN SHARRI HARRIN NAAR... Ya kara dora hannunsa na dama saman goshinsa ya karanto *AS'ALUL LAHAL AZEEM RABEEL ARSHIL AZEEM AN YASHFEEYAKA... Bayan ya gama yace insha Allah zai samu waraka." Ya mike ya maida shi cikin dakin ya kwantar dashi kana ta dawo ya zauna.. Ta daina abinda yake yi ta fusksnce shi sosai tace "Tun shigowarka nike alla-allah inji ta bakinka ka barni inata ci da kuda, wace shawara ka yanke?" Ya sunkuyar da Kai tare da yin kakkarfar ajiyar zuciya, to in ba domin uwa, uwa ce ba wa ya isa ya tursasa masa yin abinda baiyi niyya ba? Ya dago Kai a hankali yace "Tunda kin ganin auren alkhairi Kuma kin amince shikenan." Ta saki murmushin jin dadi tukunna kafin tace "Fito fili kayi min bayani, shikenan kamar yaya?" Ya sake jan dogon numfashi "Ina nufin na yarda Zan aureta, sai dai kin tuna ina tsoron ajiye mata biyu domin shakkar rashin yin adalici tsakaninsu bayan haka kina ganin zamu zauna cikin kwanciyar hankali bayan Ni da ita ba son juna muke ba?" Dariya ce ta kubuce mata tace "Itama Zuwairar da bata zake a kanka ba da tasha wuya, miskillancinka ba boyw yake ba, wannan Kuma batun soyayya bata ko taso ba ya ma rage naku, ko kuso juna ko ki da zaran Allah ya hadaku addua kawai za muci gaba da yi muku.' Hhmmmm ya Fadi a zucci Hajiya mahaifiyarsa ce yana alfahari da hakan, har bugun gaba yake yana ganin yafi kowa sanin jakinta but akwai so many times da ya kanyi doubting hakan musamman idan ta murde ta rikice ya kan rasa inda zai bullo mata kamar yanzun. To in ma banda abinta ya za ayi mace da namiji suyi zaman aure da ya dace bayan babu so da kauna tsakaninsu? Har gara ace mutum guda na so, in tafiya tayi nisa sai dayan yaja ra'ayin gudan amma wannan halin kaka Ni kayi dane yai kama?, Da shi da ita duk basa so, sai yaya kenan?.. Tayi kamar baya dakin ta jawo tarkaccenta zata fara kulle-kullen ta, yasan hali muddin bai sake magana ba ta kare nata zancen kenan don haka yai saurin tambayarta"Yanzun me zanyi abin nufi wane mataki za a dauka nan gaba?". Taci gaba da hidimarta "To ni Kuma zaka tambaya kana namiji kace baka san yadda ake neman aure ba, Kai don Allah baka ji kunya ba, lokacin da kaje samartakat auren farin nina koya maka yadda zaka yi?" Ya dafe Kai!Oh oh ya shiga uku, ya lura so take ta tursasa shi, ya daure yace "Hajiya wancan da wannan ba daya bane, kin manta inada matsayi a gidansu Zuwaira tun fil azal bayan kaunar dake tsakaninmu?" To nan dinma sai ka gwada gidansu Rahimar ka gani su ma wanne matsayin zasu baka idan itama kana neman samun gurbi a zuciyarta kasan hanyoyin da suka dace ka bi, Allah yass a dace.' Yadda ta hakikice tana maida mishi martani yasa shi dariya da sha'awa yace ",Idan naje anjima da laasar na ganta banyi laifi ba ko?" "Wane Kuma irin laifi ai sai fatan Allah ya kulla alkhairi, kaje ka gabatar da kanka matsayin mijin dana ce nayi Mata Kuma tayi alkawarin ta amince, idan zaka tafi ka biyo ka tafi da takwaranka yaga

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66