Chapter 12
Chapter 12
yaso tsegumi. Kin ganni ni ba miji ba, Ni ba wani kwakwkwaran bazawari ba mene nawa na hanzarin cire yaro a bakin nono, Maryam ko tausayin Abdul ma ba kya ji." Taja tsaki "Ke da Umma ke ban tausayi sabida ga gaskiya kiri-kiru Kun take, shun Umma kin kalli diyar taki da kyau Kinga yadda ta kode tana kanjamewa?" Cikin damuwa tace "Na lura sosai, nima ramar nata har tsoro take bani, yarinya taki sakin ranta ta hakura, wallahi kullum fadar da nike mata safe da yamma kan ta fauwalawa Allah rashin da muka yi shi Kuma Allah yasa yana cikin rahamar Ubangiji.' Maryam ta gyara zama daman gangara take nema tace "Umma ban tari numfashinki ba, ya za ayi ta samu natsuwar hankali tana zaune muku haka kawai. Ni a ganina duk halinda data shiga laifinku ne, baku matsa mata ta samu miji tayi aure? Kawai Kun Kyaleta sai biye mata kuke, har kin yayen nan don kar a sami kafar mata batun aurene." Rahima ta harari Maryam "Umma ki daina saurarenta kinsan halinta da zuga." Umma ta nisa "Wannan karon Kam gaskiya take Fadi na Kuma gano kamshinta bari Baffanku ya dawo." Ta sunkuyar da Kai ta dafa Umma "Don Allah karki hadani da Baffa Umma nayi alkawarin yayesa cikin satin nan.". Maryam tayi Mata gwalo tukunna kafin taci gaba "Ai ba yayen ba ta fitar da miji shine batu, tayi alkawarin zata amince ba zata kara kin sauraren wani abu har Allah ya zaba mata mijin." Rahima ta rike haba. "Oh ni na shiga uku, Maryam hala kudin kanfen Alh Surajo ya Baki?".. Umma ta kallesu "Wani ne Kuma haka?" Maryam ta gyada Kai "Kyaleta Umma da 'yar halas take magana, amma ba za aji mutuwar uwar sarki a bakina ba, ta fada miki ko waye shi." Baki dai shi kan yanka wuya, dole ta yaye Abdul din ranar jumma'a bayan an aikawa kakarsa. . Kaji, zabbi,madara dasu bornvita da sauran tarkace banda sabbin tufafi aka tarkato, banda buhun shinkafa da jarkar Mai, matan Hayatu suke takewa Hjy Kaltume baya wajen zuwa diba Dan yaye, shima wan baban nasa kudi ya bashi matansa kuma crates din kwai. Rahima na gida bata futa aiki ba saboda zazzabin da ciwon nono ya sa Mata, ganin bakin yasa ta tashi ta zauna. Bayan an gaisa Abdul ya dare bisa cinyar kakarsa yana baje sabbin kayansa. Umma nata zubawa su Hjy Kaltume godiya. Hajiya tace "Duk aikin iyayensa tawa tukunyar farfesun na gida sai ya taho zai ci. Umma ta kalli su Hayatu "Madallah Allah ya baku ladan zumunci." Yace "Ba komi Umma Abdul danmu ne koda Rabi'u na nan balle yanzun da kasa ta rufe idanunsa." Tun dai Rahima na dauriyyar Kar suga kwallan da take kokarin maidawa har ta bara sai nishin kukanta suka, hankalin kowa ya tashi din sun san ba shakka uban Dan ta tuna. Ana haka Baffa ya shigo cikin sauri ya tsugunna suka gaisa da bakin kana ya fara rarrashun diyarsa cikin kalamai masu taushi har hankalinta ya koma jikinta ya kara yin godiya ya fita.. 04/09/2020, 21:15 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by jami 12 Sun dade suna taba hira tun Rahima bata saki jiki ba ta warware a nan ne Jamila ke ce Mata "Kiri-kiri kin guji gidanmu Rahima." Haulatu ta kalli uwargidanta tace "Ke dai bari Yaya nima abinda ke zuciyata kenan." Rahima tayi murmushi tace "Aikine yai min yawa a school amma kuyi hakuri Ina nan zuwa." Hayatu ya kalli matansa cike da jin dadin ganin yadda suke tafiyar da al'amurransu yanzun sabanin da, yayi murmushi yace "Idan baki taho don komi ba Kya zo mana murnan tafiya sauke farali ko don Allah yayi bana za muyi arfa Ni da Jamila." Tace "Iye! Shine baku Fadi ba tun zuwanku, laifinki nan wannan Aunty amarya." Haulatu tace "Yi hakuri wallahi labarin dana kunso in fada miki suna da yawa ganinki haka yasa nayi sanyi, da gaske Ya Haseeb ya biyawa Maigidan da Uwargida kujerar hajj bana." Jamila ta amshe "Itama amaryar anyi mata alkawarin badi da ita insha Allahu." Umma ta kalli Hjy Kaltume tace "Masha Allah Kai Allah yai wa wannan yaro albarka, shi dai dukiyarsa ta dawainiya da jama'a ce, kunga hidimar da yake yiwa su Abdul kuwa?" Hjy Kaltume tace "Don Allah ki bar wannan maganar Habiba, kula dasu ya zama dole." Rahima ta kalli su Hayatu tace "Naji dadin jin labarin nan, Allah ya nuna mana anje an dawi lafiya, shi Kuma Allah yai masa sakayya yasa muji na Aunty amarya haka badi idan muna raye." Daga nan sukayi sallamar tafiya, Rahima ta rakosu kofar gida tayi musu alkawarin ziyartarsu wani satin. Bata tafin ba sai wajen sati na uku bayan tayi sarai ta koma tamkar bata taba wani shayarwa ba. Tana isa gidansu Hayatu ta kara tabbatar da ba abinda yafi zama lfy da kwanciyar hankali, yanayin gidan ya canza, maigidan ya Kara gyara ko'ina tsaf, mata da yara sunyi shar, shima yayi fes har kiba yayi ya fara teba. Ta kasa boye sha' awarsu cikin hira tace musu "Nifa kun burgeni, Ina mamakin canzawarku, wani shahararren malami yai muku waazi ya shige ko Yaya? Suka kalli juna suna murmushin fahimta kafin Jamila ta fara magana "Alamarun Allah ne, kinsan idan yaso mutum da shiriya, ba abinda myuke yanzun sai godiyar Allah da ya ganar damu." Haulatu ta karba "Wallahi mun fahimci ba abinda ke jawo tsiya irin tashin hankali da masifa." Hayatu yace "Nima kullum cikin godiyar Allah nike, da har fargabar shigowa gidana nike, dana doso kofar gidan sai gabana ya Fadi don ban San bala'in da zan shigo in taras ba, Ina kuwa shigowa abinda nike gudun zan taras, kiji harshensu na tashi kamar zasu dafa naman junansu, inyi -inyi su bari ko kallo ban ishesu ba sabida sun riga sun hau dokin shaidan Yana sukuwa dasu. "To kuma meye na tashin tashina, kuskure ne munyumi, mun gane mun tuba mun dawi hanya. Jamila ta koro jawabin... Haulatu tace "Rabu dashi dai Hajiya to waye bai kuskure?. Rahima tayi dariya "Kwarai dukkan Dan Adam ajizi ne dole a samemu da aikata kura-kurai yau da kullum shiyasa ake son mutum ya rinka rokon Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya ya Kuma ganar damu ya bamu ikon bin tafarkin gaskiya, kana ya yafe Mana zunubanmu na biye da sarari, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.Amma Ina ganin fa tun farko laifinka ne Ya Hayatu.".. Ya kalleta cikin mamaki "Kamar yaya? Alhalin kullum Ina kokarin yin adalci tsakaninsu, fitina ce kawai amma da suka ga ba riba sun sauke.". "Au Kuma haka zaka ce?" Suka tara Fadi Rahima tace "Ni dai na fahimci bala'in son Yaya kuke shi ya jawo muku bakin kishin Nan." Ya sosa keys "Haka ake so? Ina ce in har son ne competition din kyautata min ya dace suyi ba rigima da juna dani kullum kaina dana aje su ba, tsaya kiji wani sirrin kanwata wallahi da sunci gaba da shirmensu ko da yanzun na Kara aure din har na kusa gama shirya komi, Kuma banyi niyyar hadasu gida guda ba, in. Koma can in tare hankalina kwance su kuwa suci tsiyarsu nan inga karyar kishi." "Allah ya tona maka asiri, ashe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66