Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kanki but tunda ta fiki wayau da iya siyasa ko in ce duniyan cin zauna Ina zuwa." Ta koma gefen gado ta zauna tana sharar hawaye, ya wuce Kai tsaye ya bude wardrobe dinsa ya bude wani safe da key ya ciro wata katuwar envelop ya mika mata yace "Duba contents din nan kafin inje in dubo Rahima in dawo. Ta karba gabanta na faduwa, ta rinka zaro pictures dinsu ne da Husaina wasu da abokan huldar kasuwancin nasu tana jinjina Kai, don ita ta manta ma anyi wadannan hotunan don bata basu mahimmanci ba. Da alamun kowa yai barci a sashen Rahima sai ita kadai dake zaune a falonta rike da dan karamin littafin adduar Nan *Al-Ma'asurat* tana karantawa. Ya isa gareta bayan ta amsa sallamarsa, cikin kyakkyawar kulawa yace "My dear Iam so sorry." Ta sakar masa murmushi Mai kwantar da hankali "Haba karka damu isn't all that serious." Hannunsa yasa ya taba jikinta, wuya da goshinta, ya rike tsintsiyar hannunta ya duba pulse, saida ya tabbatar temperature da vital sign normal ya saki ajiyar zuciya yace " Kiyi hakuri su Zuwaira sun saka ki cikin shiriritar su." Tace "Dakta duk misulmin kwarai yasan kaddarori da jarabawar rayuwa, fatan mu Allah yasa mu ci jarabawar." Yace "All the same sai na sa an daure wannan matar." Ta bude baki ta sauka kasa gwiwa biyu tace"Haba Dakta kana son ayita zuzuta zancen kenan, don Allah ka bar magnar a rabu da ita kawai in don ni" Yasa hannayensa ya dagota "Kin san ba laifinta gareni kenan ba?" "Kamar Yaya?" "Could you believe matar nan messages ta rinka turo min harda letters wai don Allah in aureta?" Rahima ta zaro ido "What? Kiji min maras mutunci taci amanar Aunty Zuwaira take nufi?" Ya gyada Kai "Why not tunda ita Auntyn taki bata san ciwon kanta ba?" Ta jinjina "Taf mutum sai Allah, Allah ya tsaremu da sharrin mugun mutum." "Ameen ya Azeez, gobe in Sha Allah zan Kai Hajiya asibiti mu dan binciketa tana bukatar kulawa ta musamman.". Tace "Yakamata gaskiya, Allsh ya bata lafiya yasa ba wani serious problem bane." Ya mike kana yace "Insha Allah ba matsala." Yai mata sallama ya koma wajen Zuwaira ikon Allah. 21/09/2020, 15:53 - Anty saliha: ....RAHIMA...doc by jami 50 Zuwaira ta zauna turus tana karanta takardun da wai wace ta dauka da suna aminiyar ta aikowa mijinta, ta girgiza kai cikin dimuwar ganin irin kalaman soyayya da bata zaton Husaina zata iya bayyanawa wani ba balle mijinta. Hhmmmm abin tambaya ma a nan tun yaushe Husaina ta fara karakainan turowa mijinta sakonni, tabbas wannan dalilin na daya daga cikin reasons din Haseeb na dagewa cewan ta rabu da Husaina, ita kuma saunar bata gane komi ba sai kara cusa kanta take gareta tana badadi da sirrin mijinta a duniya. Yanzun ta fara regrtting watsi da nasihohin da mijinta da iyayenta ke mata tana watsu dasu. Kaicona ni Zuwaira! Ga batun da Iyayenta keyi nan cewan idan basu isa su fada mata taji ba duniya zata yi mata hankali cikin ruwan sanyi gashi ta gani. Oh oh ya Haseeb yaji da ya fara ganin sakon wannan maras mutuncin? Hmmmm ita tasan halin mijinta ko a mafarki ba zai ji sha'awar Husaina ba, rikon addininsa da kamallarsa zasu sa Allah ya tsare fadawa sharrinta don idan ance ta kai sunansa gidan malamanta ba zata musa ba, za tayi abinda yafi hakan shu'umar banza. To ni Zuwaira mene na gani laifin Husaina, ai sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga. Me na rasa? Duk da Ubangiji yai mini muwafaqa ya azurtani da samun nagartaccen miji maimakon in gode masa ta hanyar karfafa imanina da tsarkakke zuciyata, bin dokokin Ubangina da sauke hakkokin mijina, faranta ran iyayena da kokarin zama uwa ta gari ga 'ya'yana sai nayi kunnun uwar shegu na fandare na butulcewa Mahaliccina baiwar da yai min.. Ta matso wasu zafafan hawaye yayinda take tambayar kanta shin na ma sauke hakkin iyayen nawa ma kuwa bayan su din sun sauke dukkan hakkokina gwargwado? Mahaifina yai min zabin uwa ta gari, da aka haifeni ya rada min suna Kan tsarin islama, ya kokarin ganin mun samu ilmin addini dana zamani daidai yadda zasu taimaka mana gyara zamantakewar mu na duniya da gyara lahirarmu, iyayena sun bani ingantacciyar tarbiyya kana su kayi min zabin miji nagari dana isa aure to amma ni wane sakamako na basu a rayuwata ta duniya? Shin nayi kokarin sauke hakkinsu mai girma a kaina kuwa, bayan ance Annabin Rahama ya la'anci duk Wanda ya wulakanta iyayensa, an horemu da yi musu d'a a, mu yiwa Manzon Tsira, mu kyautata musu domin wajibi ne a garemu matukar basu kauce hanyar islama ba, hatta da magana ance Kar muyi musu kalamai masu muni, sabida girman iyaye a garemu ne har aka wajabta girmama 'yanuwa da abokanansu ko kawaye kamar yadda zamu girmama su iyayen namu. Ni Zuwaira 'na shiga uku' sunan wani littafi na 'Gidan iko' . Duk inda aka tabo ni inada rauni da nakasu. Can tunaninta ya koma kan abokiyar zamanta Rahima da taki amincewa da kaddarar take wulakanta ta a idon kowa alhalin ba laifinta bane ko Haseeb bai aureta zai auri wace duk Allah ya rubuto masa. Ya jima a tsaye yana kallonta tana share hawayen da suka gaza tsayawa, tausayinta ya kamashi, ya isa inda take ya rungumota yana fadin "Ya isa haka nan Zuwaira komi ya wuce tunda kin gane kuskurenki. Ta kallesa cike da damuwa "Anya Ubangiji zai yafe min laifukana kuwa?" Ya rufe bakinta "Kasancewarsa gafurun rahimeen, Yana amsar tubarmu ko da zunubanmu sun Kai girman Uhud ne, hakika Unangijinmu mai afwa ne, yana kankare mana dukkan zunubanmu idan mun gane munyi, munyi nadama mun rokesa gafara da niyyar ba zamu sake komawa ga daukan zunubin ba. Ba shakka ya soki da rahama tunda yai gaggawar fahimtar dake har kika kaskantar da Kai Kika nemi ya yafe miki." Daman ba wai Dr Haseeb bai kaunar Uwargidansa Zuwaira bane, halinta ne ya tsana yake kyama Kuma, da Allah ya nufe ta da shiriya alhamdulillah ya rungumi abarsa. Yau kwanan Hjy Katume uku a Haseeb Medical Centre, a dalilin rashin lafiyar data taso mata mai suna *NEURASTHENIA* Wanda idan cutar ta kama kwakwalwar mutum zai rinka jinsa ko yaushe bai da isassar lafiya, kasala da rashin kuzari su addabesa, ba wata cuta ce mai tsananun gaske ba, nan da nan likitocin kwakwalwa ke ganota suka taimaka da magunguna da bada shawarar samun isashshen hutu ga maras lafiyar don shawo kan cutar. Tunda ya gano cutar dake damun Hajiyarsa kenan ta matsa ya daukota da kansa ya kawota asibitin gashi har jikinta yayi kyau ta samu sauki sosai, likitoci da sauran ma'aikatan asibitin sai ina ka saka ake da ita, kulawa ta musamman ake bata, to wani ma yai rawa ballantana dan makadi? Mahaifiyar Chief Medical Director ce fa da kanta. Tunda aka kawota Rahima ce ke zaman jinya tunda ba tada diya mace, da kyar dai Hajiyar ta amince da dawainiyar ganin alamun 'yar gidan nata na dauke da juna biyu. Kwananta na hudu kenan yau ta Kara samun sauki Amma likitan yaki sallamarta yadda ta bukata don haka Uwargida Zuwaira ma ta taho tace

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66