Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

yace "Ji nan please je kiyi wanka, Kuma idan domina kike shafa wannan turaren don Allah ki canza bana so, ki tabbatar da kin teafe kitson attachement din nan, ki yanke wadannan akaifar da kika bari kamar ta masu cikin kare idan ba haka kuwa sai dai mu hakura da juna." Nan da nan ta amince "Wallahi dyk zanyi abinda kake so, amma ban dade da yin wanka ba sai na sake wani yanzun? Ya gyada Kai "Manufata kenan, idan ba zai tuwwu ba okay my kwana lafiya.". Ta zabura ta duro daga Kan gadon ta fada toilet..... Haseeb ya bita da kallo ya mike tsaye ya fuskanci alkibla ya daga hannayensa sama ya fara jero addua "YA Allah kasa yau ya zama mafarin shiriyar wannan baiwar taka saboda kai ka halasta saki amma kana kyamar yinsa, ya Ubangiji kar ka kaddareni aikata abinda idan nayi Al'arshinka zai girgiza, Allah ka karamin hakuri da juriyar zama da ita, ka bani ikon yin adalci tsakanin matana, Ya Allah ka shirya Mana zuriyyarmu idan zaka Kara Mana ka bamu masu albarka shiryayyu salihai masu shiryarwa, ka gafarta mana dimbin zunubanmu, ka yafe Mana baki daya." Ameen. Ya shafa kenan ta fito ta ganshi a tsaye, ta dauka ita yake jira, da sauri ta isa garesa ta kwantar da kanta bisa kirjinsa, yasa hannu ya rungumeta, ko adduar da yayi ne yasa zuciyarsa ta rage radadin tsanarta? 18/09/2020, 00:18 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 43 Kiran sallar farko ya zame jikinsa ya shiga yai wanka tareda alwala ya fito yai shirin zuwa masallaci, tashim duniya Zuwaira bata motsa ba hakan ya fita ya barta, ya nufi dakin yaransu ya tashesu suka yi akwala ya tafi dasu masallacin.. Har suka isar suka dawo bata farka ba sai juyi take a gado, yai mata tsaye saida yaga ta sauka ta shiga wankan ya Kyaleta, a gurguje ta gabatar da sallar ta koma gado taci gaba da barcinta, ya kalleta yace "Allah ya shiryeki." Bai tsaya jiran wata Mai aiki ba da kansa ya hadawa su Khalifa breakfast suka ci tare dashi, ya shiryasu ya kuma kaisu makarantar ya ajiye ya dawo gidan bai sake bi ta kanta ba ya koma falo yai zamansa. Ya dauki 'yar redio ya kunna, but sauraren kowanne programme ya gagara saboda daidai lokacin tunanin Rahima ya kutso masa, al'amurranta suka rinka masa yawo cikin kwakwalwa, ya saki wani dan murmushi, kasa daurewa yayi ya zaro wayar ya danna mata kira. Ta rufe Qur'aninta kenan Kiran ya shigo ta daga ta sallama ta gaisheshi har da dan rusunawa kamar tana ganinsa. "Ya kwanan su Aunty da Yara?" Ta tambaya . "Lafiya kalau Ina Abdul?" "An kaishi school." Ta amsa a takaice ta kuma yi shiru.. Hhmmm bai san dalilin da yasa da yaji muryarta yake daburcewa ya kasa furta kalaman da ya shirya zai fada mata ba, and she's not helping matters sai tayi shiru ta barsa yana kame- kame. A nata bangaren kwarjinsa ke haddasa masa increased na heart beat wanda hakan ke sa ta kasa magana. Yaji shirun zaiyi yawa ya gyara murya yace "Jiya bamu gama zancen mu ba." "Wane zance kenan?" "Zan tuna miki on one condition, kin yarda zaki bani abinda nike so?" Ta gyada Kai "In dai bai fi karfina ba insha Allah." "To baki ce komi ba, Kinga kifayen?" Ta sake amsawa da "Na gani sunyi kyau nagode sosai but still Ina cikin duhu, rashin fahimtar ma'anarsu." "Zan miki bayani idan na shigo anjima kadan." "Ina ce a asibiti zamu hadu kawai.". Takaici ya kamashi, Lalle yarinyar nan bata kaunarsa, dubi yadda ya kwanta ya tashi da tunaninta a rai amma ji irin reaction dinta da ya kirata." Yace "Okay mu hadu a can din ba problem." Sai karfe hudun bayan la'asar ya kirata suna cikin hira dasu Hjy Fatima." Kamshinta kawai ya isar masa da sakon ta shigo office din nasa, ya juyo yana kallonta, taku daya ana biyu yaja ya tsaya a gabanta, yai niyyar embracing dinta, ko me ya tuna ya fasa, daidai lokacin aka kira wayarsa ta office, ya juya ya dauka ya fara magana. Tsawon mintoci Yana ta magana daga harshen turanci ya koma larabci, *Hal anta bi khair?* Ya tambaya ashe patient dinsa ne daga Riyadh yaji sauki ya murmure, Daktan ya ci gaba da magana taga zasu dauki lokaci, ta fita ta basu wuri, tana fita ta shiga ta yiwa su Hjy Fatima sallama ta koma gida. A ranar kuwa Zuwaira ta kasa gane kansa, yayi zamansa a falo shida Yara har suka yi barci ya maishesu ciki ya dawo falon yaci gaba da latsar wayarsa.. Ba wani abu ke cinsa ba illa tunanin Rahima, zuciyarsa kamar ta fashe , wannan wane irin bala'ine? Ya dace ya shareta dalilin abinda tayi masa tayi tafiyarta ta barsa but ya kasa daurewa why? Ya yanke shawarar tura masa sako but muddin ta gani bata yi responding ba bayan ya tona mata sirrin zuciyarsa zai kyaleta sai ta ne me sa don kanta. Nan take ya rubuta mata *Lokacin da zaki karanta sms dinnan, ki tabbatar tunaninki ne ya addabeni, may be in kasance cikin murmishin da na kanyi duk lokacin da tunaninki ya bijiro min cikin kowanne yanayi a ko'ina nike ko me nike yi Kuma. Bayan kin karanta warannan kalaman, ina fatar zaki fahimci matsayinki a gareni a yanzun da anjima, da har muddin rayuwa even if it's for a blink of an eye. Kiyi murmushi domina yayinda kike ci gaba da hidimominki don zan kasance cikin tunaninki.* Zuciyarta ta cika fak da murna da farin ciki duk da bai furta ainihin kalaman da take son ji ba wadannan ma kadai sun isa Mai hankali ya gane *So da Kauna * aka dunkule waje daya. Fahimtar inda ya dosa yasa ta maida masa martani kamar haka: *Daga awoyin da muka rabu ina fatar ka sakani cikin ruhi da zuciyarka ya kasance ko rufe idanu kayi Ni kake gani cikin tsananin tunaninka da irin wannan ci da zuccin saboda nayi matukar maraicinka, ban ki a ce a yanzun Ina tare dakai cikin raina, zuciya da ruhi ba.* Ya rasa me zai ce da ita don dadi, hakika Rahima ta fahimci manufarsa fiye da zatonsa, ashe daman m shi take jira ya bara kafin ta tona nata sirrin zuciyar, me wayon tsiya ya Fadi a fili yana murmushin farin ciki.. Ba bata lokaci ta sake aika mata *Hakika nayi maraicinki kamar in janyo sauran time din da zamu kasance tare, ashe kewar masoyi ukuba ne.*. Ta maida masa reply *Tawa kewar ta zarce taka Ya Haseeb.* *Karki damu zamu magance su duka, sai ince sai mun hadu.*. Ta rubuta Waiting for you with pleasure. 18/09/2020, 15:48 - Anty saliha:...RAHIMA..doc by jami 44 Ranar d zai koma gidanta Rahima ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kara tsabtacce ko'ina cikin gidan ya ci gyara tamkar ranar aka kawo ta, komi yayi fes, ta bangaren abinci ta shirya masa light food ta dafa masa mai suna "Muhammas' abincin larabawa ne yana yanayi da cous-cous, hade da farfesun kaji, a gefe ga dambun kifi, banda drinks na kwali, ta hada masa lemon tatacciyar abarba da gwanda kana ta saka kwalbar favorite drink

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66