Chapter 14
Chapter 14
amince a kulla wannan abu don kaji dadin rike amanar da ya damka maka?" Ya girgiza Kai "Kayya ba sai na kaiga hakan ba duk inda take zanyi kokarin taimaka mata gwargwadon zarafina, yaro kuwa dama namu duk da haka ba Zan tauye mata hakkinta matsayinta na uwa ba dole zamu bata damar kulawa da al'amuran danta a duk lokacin da bukata ta taso." Hjy tasha mur "To ka ga ni shawarar dana yanke kenan kaje kayi nazari, na baka sati guda kacal bayan haka ka taho ka fada min abinda ka yankewa zuciyarka, yi ko tsallake maganata?" Da jin zancenta yasan ba zata kara saurarensa ba,bai hana ya durkusa yana rokonta Allah da Annabinsa ta bar wannan batun da baida ko dadin ji. . Tace " Ka daina yi min magiya, Wai ma tsaya tunda ka girms kasan ciwon kanka na taba tursasaka kayi min abinda nike so ko kuwa na taba baka shawarar da ba kaga amfaninta a rayuwarka ba? Yace "Ah ah! Tace "To kaje ka dawo bayan sati guda Ina saurarenka, na riga na gama maganata." Yayi shiruuu ya rasa me zai sake ce Mata in har zata sauraresa kenan, yafi kowa sanin halin mahaifiyarsa kaifi daya ce ita, idan ta tsaya akan abu babu daga kafar ba ja da baya don haka Kar ma yace zai sake bata baki, ta riga ta kudurtawa ranta sai abinda Allah yayi kenan. 05/09/2020, 12:14 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 14 Hjy Kaltume bata tsaya nan ba, aikawa tayi makarantar da Rahima ke koyarwa tace direba ya daukota yace tana nemanta. Ba a jima ba ya hangeta ta fito tare da wasu malaman bayan an tashi, ya tareta ya durkusa ya gaisheta ta kallesa cikin mamaki "Bala lafiya?" Ya amsa "Lafiya kalau Hajiyar ce ke nemanki da gaggawa." Alamun damuwa ya bayyana a fuskarta, kace kuma lfy? Bata taba min haka ba ka tabbata ba matsala Bala?" Yace "A sanina ba komi." To shikenan mu hanzarta Amma sai mun tsaya in shiga gida in Fadi Kar Umma taga ban dawo da wuri ba su damu.". Yace "Ai tun hanyata ta zuwa na shiga na fadowa Umman uzurun Hajiyar kamar yadda ta umurceni." Jikinta dai yai sanyi, ta shiga sake-saken zucci har suka isa. Ta shiga cikin gidan da sassarfa, ta isko Hajiyar a tsakar gida tana alwala, ta saki ajiyar zuciya don a zatonta ko rashin lafiya ce, Hajiyar taga alamun a firgice take, ta danyi dariya tace "Maraba lale Rahima, yi hakuri 'yan nan ban so firgita ki ba, zo ga buta kiyi alwala." Saboda jin nauyinta tace "Na riga nayi, a zahiri kuwa tana period. Kai tsaye ta shige dakin, Hajiyar ta miko mata kulolun abinci tace "Ci abinci kafin inyi Sallah." Ta zuba abincin amma ta kasa cin ko loma guda sabida tsananin tunani. Ta kosa ta kare adduoin da take yi bayan idar da Sallah. Zuwa wani lokaci ta Kai makura kagara da son jin dalilin nemanta, da kyar ta amsa gaisuwar Mairo data shigo daidai lokacin. Hjy Kaltume ta aje tasbaha bayan shafa adduarta ta juyo tana fuskantar Rahima tare da kallon plate din abinci ta danyi murmushi " Ba ki ci abincin ba lafiya?" "Na koshi ne.' "Ko dai kin razana da sakona ne?" Ta gyada kai "Gaskiya na dan firgita tunda baki taba min irin wannan Kiran ujula ba." "Karki damu alkhairin." Rahima tace " Hajiya meke faruwa?" Hajiya tace "Kafin kiji komi Ina son sanin shin ya kika daukeni lokacin da kike auren marigayi da yanzun?" Tayi wani da fuska "Hjy ban fahimce ki ba." Hajiya tace "Abin nufi wane matsayi kika bani a zuciyarki." Ta saki fuska tace "Baki da wani matsayi a gareni daya wuce na uwa tun a da da Kuma yanzun saboda kin rike tamkar 'yar da kika haifa a cikinki, baki taba nuna min rashin kauna ko na dakika guda ba, akwai lokutta da dama dana kan tuna korafin marigayi kan cewa kamar kin fi sona dashi, na kance don baki da diya mace ce shiyasa kike kaunata amma a zahiri kishin yadda muka shaku yake." Hajiya tace "Alhamdulillah naji dadin wadannan kalamai, Ina so ki sani har gobe ina kaunarki Rahima, kauna fisabilillah irin Wanda Allah ke dasawa mutum, halayenki suka karfafa kaunarki a zuciyata. Itace Kuma tasa nayi tunanin sama miki miji Wanda banyi hakan ba Saida nayi nazari sosai na tabbatar idan Allah ya hada zuciyoyinku anyi auren nan zaku dace da juna matuka. Rahima tayi wani irin gingirin tace " Miji Hajiya? Gaskiya ban shirya sake aure yanzu ba don ban samu Wanda ya kwanta min a rai kamar Rabiu." Hajiya Kaltume tace "Na fahimci haka, wanda na sama miki zai kwanta miki a rai ne idan kuka shaku da juna, ina tabbatar miki zaku sami ingantacciyar rayuwar auren da zai ba kowa sha'awa. Nasan haka ne kuwa saboda sanin halayyanku kusan daya ne, na lakanci ke yarinyace data san ya kamata, kinsan girman na gaba, kina da hakuri da juriya da dauriyyar kowacce irin matsala ta taso miki, kinada tawali'u , kinsan yadda ya dace ki zauna da wanda ke matsayin mijinki cikin ladabi da biyayya, kin iya mutunta mutum cikin kowanne yanayi, kinada tausayi da jin maganar na gaba dake koda abinda zai gaya miki bai miki dadi ba. Rahima ke yarinyace mai yawan ibada, rayuwar duniya bata shagaltar dake barin bautar Ubangijinki ba, kina daure rashi, kiyi farin cikin samu komin kankantarsa, kinada yasan kyauta ba irinta almubazzaranci ba, da wuya inji kin Fadi karya komi rashin gaskiyarki, a yayinda gaskiyar ta zama Miki abin Fadi duk runtsin da kika shiga, baki da kyashi balle hassada ko munafunci. Kin zauna da mijinki damu tsakani da Allah.. Wadannan halayye naki sunzo daidai da namijin da nike so ki aura Rahima, zan iya cewa ma wasu abubuwan sunfi naki inganta kasancewarsa namiji, Kuma ya dandani wahalhalun rayuwa fiye dake amma duk da haka bai gaza ba." Rahima tayi kasake, gaskiya tayi mata yawa, ba shakka Hajiya ta santa tamkar tafin hannunta, lalle ta lakanceta tsaf fiye da yadda ta lakanci kanta, idan kuwa haka halin mutumin yake lalle ta samu abokin rayuwar aure irin Wanda take mafarkin samu tun tasowarta zata Kuma iya zama dashi saboda halayyensa ko bata son sa... Tunanin So da tayi yasa ta juya ta kalli Hajiyar dake kallonta, tayi saurin dukar da Kai kass tace "Hajiya naji bayaninki Kuma nagode sai dai abin tunani, ya ayi kisan shi din Yana son wannan auren hadi yadda kike so?" Tace "Amincewarki kawai nake jira, Ina son ji daga bakinki kin amimce da shi ko Yaya?" Ta Kara sunkuyar da Kai tace "Amincewarki dashi shine nawa Hajiya don nayi imani ba zaki sani hanyar da zan wahala ko yin dana sani ba." Hajiya tace "Alhamdulillah kamar yadda amincewata ya zama naki shima din amincewata shine nasa, Amma kafin a fara wanzar da komi kije kiyi nafila ki karanta istikhara ki roki Allah zabinsa Kan al'amarin kamar na kwanaki bakwai, idan kin gama sai inji daga gareki. Nima zan tayaku, Allah ya taimakemu, ameen." Rahima tace "Wai a Nan garin yake ko danuwanki ne da ban sani ba?" Ta boye murmushinta " Me kike ci na baka na zuba,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66