Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

da na amince ka zama abokin rayuwata.". "Na amince sosai Rahima nagode, bari in koma gida, ba sauran abinda kike bukata?"?. Ta kada Kai "Tsakaninmu ba wannan, lalurarka tawa ce kamar yadda tawa take taka, kasan nima 'gata ce su Umma sunyi min komi, kasan sun so a hada bukin nan dana su Maryam amma Allah bai kaddara ba Abbas ya roki arzikin a bari sai ya dawo daga Dubai, sha'anin Dan kasuwa.". "Lalle naji, Allah yasa shine alkhairi mu dai Allah yasa ba za a daga namu ba." Tayi murmushi kawai ba tareda bashi amsa ba. Ya fiddo kudin da Hjy ta bashi ya mika mata taki karba saida yace sakon Hjy ce ta tara jannu biyu domin karba, maimakon ya saka mata kawai sai taji caraf ya kama hannayen nata ya rike yana kallonta... Tayi saurin kwacewa tana fadin "A'uzu bilahi minal shaidanin rajim, wa iyazu billah." Shima yai saurin juya baya Yana tasa adduar korar shaidan din, kana ya juyo a hankali yace "Rahima ki gafarceni, banyi da niyya ba wallahi." "Hhmmm Allah ya gafarta mana Rabiu nasan ba halinka bane, babu zargi tsakaninmu." Yace "Nagode, gashi. A wannan karon hijabinta ta santa ta rufe tafukan hannunta shi Kuma ya saka Mata, suka yi sallama ya tafi cikin damuwa. Shaidan mugune, la'ananne, masheranci, Allah ka Kara yi Mana katangar karfe da dashi. Adduar da Rahima keyi kenan har ta shiga gida ta iske Umma da 2000 din da ya bata. Nan take ta fara fada "Anya Rahima ba nace karki sake karban ko sisi daga hannun yaron nan ba, yaro dan makaranta da wane hidimar zaiji taki ko nasa?" Ta durkusa "Umma naki karba ya tilastani Wai Hajiyarsa ce tace ya kawo min." Umma ta kyalkyace da dariya "Hjy Kaltume kenan, aikinta yafi da haka, wallahi kasancewar danta ne zaki aura yasa nike farin ciki, domin duk unguwar nan kowa yasan macece mai matukar sanin yakamata, ba a taba jin kanta da surukanta ba balle na tsakaninta da 'ya'yanta. Gashi Allah yasa babban danta ya saya mata wannan babban gidan take zaune da kowa lami lafiya, keni yadda labari yazo min ance ba irin wahalar da bata sha ba da mijinta na fari daga ita har danta, ance yai masa kaskanci kamar bashi ya kawosa duniya ba to ga sakamakon Allah nan tana gani, shi yaron ya zama kwararren likitan kwakwalwa ba unda sunansa bai Kai bba daga Nigeria har kasashen waje, ke naji ance ma har turawa hayarsa suke yaje can yai musu aiki su biyasa.." Tunda ta fara bayaninta ba tace komi ba Saida ta numfasa tace "Umma kema kina sauraren gulmar matan gidan buki ko?" Tace "Ba gulma bace, wafannan batutuwa da kika ji ba karya ba za'ida, Ni nasa aka binciko min don dole insan halayyar mutanen sa zan Kai Diyata cikinsu, ko nayi kuskure. Rahima ta kada Kai "Uhmmm Uhmm Ymma, Ni zani in kwanta.". Ta kalli kudin tace Dauka ki ajiye a jakarki ba zaki rasa amfani dasu ba bai kamata in kashe kyautar sarakuwarki ba ta karike tana dariya. Cikin shagwaba tace "Umma abin ya koma zolaya Kuma, Saida safe. 03/09/2020, 22:19 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 8 Suka ci gaba da shirin buki har zuwa ranar daurin auren, Yayan ango ya biya sadakin Rahima lakadan, an daura aure lafiya an tashi lafiya, shagali ya rage na mata inda suma suka ci gaba da saukar qur'ani mai girma aka dora da wa'azi da nasihohi yayin walimar don taya ma'auratan murna da fatar alkhairi. Iyayen amarya sunyi rawar gani wajen gyarewa diyarsu dakunanta ras, sai wanda ya gani, sun kuma nuna bajinta wajen kawowa ango garan buhunnan abinci da su Mai da sauran tarkace harda kudin cefane a sama, a yayinda dangin angon suja karbi sabuwar 'yaruwar tasu hannu bibbyu. Sati guda suka dauka sua amarci sannan suka koma school don ci gaba da neman ilmi. Kafin nan Saida Rabiu ya zagaya da amarya gidajen 'yanuwansa kaf da abokan arziki don you musu ban gajiya su Kuma san juna, gidan Ya Haseeb ne farkon ziyarta inda suka yi karo dashi zai fita cikin hanzari domin ana nemansa a asibiti, sama-sama suka gaisa don Rahima ma ba zata tantance kalarsa ba, saurin da yake bai bashi damar tsayawa ba balle suyi masa godiya. Washegari Ya Hasseb ya Kira kanin nasa bayan ya bashi hakurin rashin tsayawa su gaisa a jiya ya mika masa key din mota "focus" a matsayin gift dinsa na aurensu tareda taya su murna da adduoi. Murna a wajensu bai faduwa, Hjy Kaltume kuwa harda hawayen dadi Saida ta fitar tana ci gaba da sanyawa Haseeb albarka. Wani weekend Rabi'u da amarya suka shiga kanti suka cikowa yaran Hasseb kayan kwalam suka nufi Galadanci misalin karfe sha daya na safe. Tuni yaran da mahaifiyarsu sun tashi sunata Kara kaina a kicin, Rabi'u ya sallama Rahima na biye dashi a baya dauke da ledan tsaraba. A guje yaran suks rugo suka nufo shi "Uncle oyo-yo. Ya duka ya dauki karamin mai suna Junaid suna kiransa Khalifa sabida sunan mahaifin maigidan kenan, shekarunsa biyu harda rabi, ya rike hannun babban Mai suna Mohammad suna kiransa Abba shima kasancewar sunan shakikin Haseeb ne Wanda ya taimaka masa kwarai a rayuwa kana shine surukinsa mahaifin matarsa Zuwaira, shekarunsa hudu. Zuwaira ta daina abinda take yi ta juyo garesu cikin murna ta rungume Rahima "Maraba lale da amare da ango, Rabiu ba kace min aure kake so daman tuni, kaga kibar da kayi kuwa, ko zan San sirrin?" Yayi wani irin juyi a tsakiyar kicin yace "Wasa Ni da kyau Auntyna amma kash sirrin tsakaninmu ne Rahima ko in Fadi?" Cike da kunya tace "Kyaleshi don Allah Aunty har akwai wani sirrin da ya wuce shagwabamun da kuke kullum." Zuwaira tayi dariya "Laifin Dakta kenan na fada masa ya rage Kar nan da shekara guda muga Rabiu ya aje tozo." Kusan awa biyu suka kwashe suna hira saboda ance Yayan nasu bai tashi daga barci ba. Rahima ta zauna gefe ta zuba tagumi tana kallon yadda Rabi'u ya kwanta su Khalifa nata dumurmusarsa,ya daga wannan ya aje, yaiwa gudan cakulkuli, su fada a jikinsa dukansu suna dariya, gefe guda ga kayan wasansu da suka watsar sunyi kaca-kaca, shaawarsu ya cikata Nan take tayi shaawar samun nasu babyn harta fara imagining yadda babansu zai rinka wasa dashi kamar yanzun, gaskiya Rabi'u mutum ne Mai son Yara.. Bata ankara ba taji yana gaida Ya Hasseb, tayi saurin gyara mayafinta ta zamo daga kujera ta durkusa gwiwa bibbyu ta gaida wan mijin nata cikin ladabi da biyayya. Ya amsa cikin yanayin da bata iya fassarawa don babu sakin fuska a tareda shi sam. Bai zauna ba ya koma falonsa Kaninsa ya bishi can ita kuma suja ci gaba da hira da Zuwaira inda ba a dau dogon lokaci ba ta lakanci halin Antyn tasu tas Zuwaira macece Mai harka,tafi mijinta sakin fuska nesa ba kusa a, tana da son mutane da saurin sabo saidai fa akwaita da surutu don cikin awanni kalilan ta fayyace mata labarinta kaf , na iyayenta da 'yanuwanta da na shi kansa maigidan nata, ta fada mata irin zaman da suke da irin matukar son da take masa. Wani Abu da ta

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66