Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

Lalle ita zata amshi Rahima wajen jinyar domin ta huta, jinya fa ba karamin al'amarine ba, so da yawa Mai jinyar maras lafiya kanyi ciwo na musamman saboda yanayin kulawar ko zirga-zirga da sauransu. Rahima ta dage ita zata karike don ladan take kwadayi. Suna cikin gardama sai ga Hayatu da nashi ayarin sun shigo cikin dakin da Hajiyar take, wurin ya kacame... Sai ga Ya Haseeb ya danno kai, wuri yai tsit, fuska a murtuke ya kalli Hayatu "Daman kana cikinsu kana kallonsu suka dami mutane da hayaniya?" Hayatu yai turus yace "Sarkin yawa fa ya fi sarkin karfi Ya Haseeb, duba ganni ka gani mata hudu ni kadai?" Yayi murmushi "To lauya, hayaniyar me ake?" Zuwaira tace "Wai nace Rahima ta koma gida haka nan ta huta ni zanci gaba da zama taki, ita Kuma Haulatu tace itama zaman za tayi." Ya kalli Mahaifiyarsu cikin kauna yace "Me kika ce?" Tasha mur ta mayar "Me zance kuwa, in da ka barni cikin dakina ai da kowa ya huta, yanzun sai kasan nayi " Ya sake yin murmushi yace "Shikenan na yarda da shawarar Zuwaira, kowa ta koma gida a barta ra zauna shikenan ko?" Duk suka yi tsit har Rahiman kuwa da yai tunanin ta furta wani abu bata kala ba, to wa ya isa ya daga hukuncin da babban Yaya ya zartas?" 21/09/2020, 22:59 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami 51 Da kansa ya dauki Rahima suka koma gida, ta cewa Uwale bata jin cin komi a daren don haka suka yi sallama ta wuce dakinta, ta tube ta shiga wanka inda ta dade cikin ruwan dumi tana shakar lemon scent na bath salt data zuba, ta rufe idanunta tana hamma.... Haseeb ya gama nasa wankan ya kimtso ya shigo domin mika godiyar dawainiyar da take da mahaifiyarsa, ya zauna shiru bata fito daga toilet ba, ya dauki wayarsa ya scrolling ma'idanar wakewaken da yai saving, ya danna daya daga cikin wakar da yake so mai taken *What have I to do to make you love me,what have I to do to make it right?* Wace mawaka da suka lakabawa kansu suna *Blue* suka raira. Ya gyara kwanciyarsa ya l lumshe idanu yana tuhumar me yasa idan yana sauraren wakar nan ya kanji tamkar domin shi da Rahima aka rerata? Me yasa zuciyarsa taki amincewa da Rahima na so da kaunarsa yadda take ikrari,baya son yana doubting but Rahimar ce wani lokaci sai ya kasa gane kanta, sai ta saki jiki Sai Kuma ta janye sai ya rinka bi yana rarrashi, ko kuwa har yanzun bai fahimci ita din mai murdadden hali bane kamar sa? Ta kanyi taka tsan-tsan da gujewa duk abinda tasan zai jefata a damuwa. Ya sake duban agogo, ta dade fiye da kima cikin bathroom... Ya kasa daurewa ya mike yai knocking daya biyu har uku shiru ba amsa, habawa a gigice ya bude kofar ya afka cikin toilet din a tsorace... Ya saki kyakkyawar ajiyar zuciya yayinda ya ganta zaune cikin bathtub tana barci. Ya matsa ya zauna bakin bath din tare da saka hannunsa cikin ruwan wankan da har ya fara hucewa, don kar ya firgitata ya matsa daf da kunninta ya rinka Kiran "My dear....a hankali. Kamar a mafarki ta farka ta jita tsundum cikin ruwa, ta girgiza kai tana kokarin gano halinda take ciki Ya mika mata dauke da towel ta amsa ta mike tsaye ta daura yasa hannu ya daukota cak bai direta ba sai kan gado, sanyi ya fara kadata ta shiga rawar dari, yai saurin dauko riga mai kauri ya saka mata kana ya lullubeta da lallausar blanket ya koma ya zauna yana kallonta cikin takaici, sun jima ba wanda yai magana har saida ta ji ta daina jin sanyin, dumi ya ratsata ko'ina ta yaye blanket tayi mika ta dago ta kallesa tace "Thanks for rescueing me ban san lokacin da barci ya daukeni ba." "Na fahimta." Ya mayar mata a takaice. Jin irin amsarsa yasa ta yunkura ta zauna tace "Me ke faruwa naga you're worried?" Yace "Ke ya dace a yiwa wannan tambayar Ina bukatar sanin meke faruwa?". Ta amsa "Kamar me?" "Ina son sanin dalilin da yasa kike yawan barci yanzun duk inda kika zauna al'amarin ya kai Kuma har a bathtub, why?" Tace "Nima haka na tsinci kaina ciki." Ya dago cikin mamaki "Kina nufin rashin lafiyace ta sameki ban da labari?" "Kalau Nike, may be dai yawan tashin da nike cikin dare bana samun isashshen barci ne." Yace "Uhhmmm, do me a favor, Miko min hannunki." Tayi nawar mika masa don tasan da abinda yake son ganowa ya tabbatar... Ya riko hannun da kansa ya juya tafin hannunta ya kura ido ya tsaya shiru kamar mai nazari.. zuwa can ya saki ya saki ajiyar zuciya kana cikin muryar da bai taba amfani da ita wajen magana da ita ba yace "Yaushe Kika shirya fada min kina dauke da cikina Rahima?" Da ace ba kusa da ita yake ba da wuya taji abinda ya Fadi, da tajin Kuma yanayin muryar tasa duk ilahirin gashin jikinta mikewa saboda taushinta, ta kasa bashi amsa saboda kalamansa sun ratsata sosai, ua akayi ya gane tana dauke da juna biyu? Kaji wani wauta, to idan shirmenta rashin laulayi da dafewar cikinta zai hana kowa ya fahimci halinda take ciki shi ba likita bane zai iya ganewa cikin kowanne yanayi? Wace amsa zata bashi yanzun? Bata da wani kwakkwaran dalilin rashin sanar dashi illa jin nauyin a ce wai ita ke dauke da cikin Ya Haseeb, kunji wata sabuwa! Meye na jin kunya tunda an riga an zama daya anyi auren nan me ya rage illa fatar samun zuriyya dayyiba?" Shirunta ya kara tunzura shi ya mike zai bar dakin ga tunaninsa zargin da yake yi ne ya tabbata tabbas bata damu dashi ba, Rahima bata wani sn shi, because idan ba hakan ba ne why zata samu ciki almost 3months taki fada masa me take nufi? Ta lura da niyyarsa tayi saurin durowa daga gado ya juyo a fusace, nan da nan ta durkusa a gabansa "Nasan nayi laifi kayi min afwaa kayi hakuri. Ya nisa "Hhhhh inda take kamashi kenan, da zaran tayi ba daidai ransa ya baci zata gaggauta bashi hakuri sai dai wannan karon yayi fushi sosai ya kalleta rai bace "Da hakurin ta mutu nawa kika bayar? Ki zauna kiyi tunanin abinda kika yi min dinnan ya dace, idan ban San halinda kike ciki ba wa ya kamata ya sani? But tunda kina ganin hakan ne alkhairi a gareki is okay ki neme ni lokacin da kika shirya." Yana gama magana ya fice abinsa ya barta a durkushe. Ita kanta tasan ta tsokano zuciyar maza ba fus kenan. Tun daga ranar bai sake waiwayarta da batun na ita Kuma ta rasa yadda zata bullo masa, rayuwar tasu ta canza salo suka koma kamar yanayin zamansu da farkon auren. Satin Hjy Kaltume biyu cif a asibiti ta matsa ya sallameta, ya dauketa da kansa suka maishe ta gida shi da Zuwaira. Hajiyar sam bata San da wata matsala tsakanin Daktan da amaryarsa ba, babu ma wanda ya lura su kadai suke abinsu. Yau Rahima ta tashi cikin matsanancin zazzabi hade da mura,

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66