Chapter 29
Chapter 29
zata yi wajen bukin wata kawarsu da za ayi a Hotoro, Kuma a kullum ta kanso tayi shiga ta burgewa da tsadaddun kaya don ta nunawa duniya ita 'yar business ne, matar shahararren likitan da ake damawa dashi a kasarmu Dr Haseeb Junaid. Ya lura hankalinta bai tare dashi, ya kakkabe rigarsa ya tashi ya dauko key din motarsa yai bar mata gidan Bai zame ko'ina ba sai gidansu Zuwaira ya wuce Kai tsaye cikin gidan y gaida matan gidan su uku, sarakuwarsa ce Uwargida sai masu bi Mata. Dr Haseeb ya koma falon surikin nasa ya zauna Yana jiran fitowarsa, nan ya tsudumma tunani, kwakwalwar sa ta tariyo masa tarihin rayuwarsa tun yana karami da dalilin haduwarsu da Alh. Muhammad.. Shi dai an haifesa a unguwar Galadanci, mahaifinsa Mal Junaid rikakken dan boko ne daya kware a fannin kimiyya, malamine a jami'ar Bayero. Ya mallaki mata daya Kaltume da albarka da guda daya tilo, sun day dogon lokaci basu Kara samun haihuwa ba a dalilin haka Mal ya nemi auren wata bazawara Kuma daliibansa ya aure. Tun tarewan amaryar ta nuna ita babu ruwanta da Uwargidanta balle wani danta daya tsone Mata ido. Yaron ya zama wajen uwarsa kadai yake samun sararawa wace ganin halin ko in kula da uban ke nunawa danta bayan ya Kara auren yasa ta ajiye kunya ta rungumi abinta. Yana kara shekaru yana fahimtar yadda mahaifinsa ke yin nesa dashi Wanda da ya dauka kunya ce irin wanda iyaye kanji na dan fari but daga baya ya gane wata irin kiyayyace da bai San mafarinsa ba Abinda ban mamaki ace farad daya uban daya haifeka ya dawo bai kaunarka, duk da haka daga Kaltume har Dan basu danganta hakan da komi ba. Amaryar malam ta fara haihuwar diya mace ta rasu, tun daga lokacin Abdul Haseeb ya fara karaya da lamarin mahaifinsa domin rashin jaririyar nan da akayi tamkar zautu yayi, bayan nan Allah ya bata haihuwar diya biyar, mata biyu, maza uku, Allah ya sake amsar matan ya bar Mata mazan. Duk da ya kasance shine babba, a kullum mafarkin mahaifinsu ya ta'allaka Kan kanninsa ne kawai na su din su gajeshi fannin karatu. Ba zai taba mantawa wata rana suna zaune gewaye da uban suna hira,kowa na fadin abinda yake son ya zama idan ya girma, Abdul Haseeb yace shi likita yake shaawar zama maimakon uban yaji dadi ta bashi kwarin gwiwa sai ya hantare sa ya daka masa tsawa yace "tafi can da wace dakusassar kwakwalwar? An fada make batcu ake a tashi a zama likita? Ko da wannan tsamin bakin da in inar taka ce zaka zama likita? A lokaci bai wuce shekaru goma sha biyu amma yaji zafin gorin da mahaifinsa yai masa, kalamansa sun sa hawaye masu zafi gangaro masa wadanda uban ya lura yace ya tashi ya bashi waje .. Kaltume ta gansa yana kuka ta tambayi dalili yaki fada Mata don ta fara wayon gudun bacin ranta, sai dai tun daga ranar ta Kara zage damtse ya daukarwa kansa alkawarin zama wani abu a rayuwarsa duk wuya iya wahala, ij karatu nasa mutum yai suna to sai yayi suna gabas da yamma kudu da arewa sai an San da zamansa. Ya dage da karatu ita Kuma uwa ta dage da neman maganin gyaran tsamin baki da in Ina da ya tashi dasu, duk inda taji magani zata nema ko Saida wani Abu nata ne ta amso ta bashi bayan adduoi da yake karya kummalo dasu,idan zai kwanta barci su din zasu masa bargo. Kullum cikin sanya masa albarka da Kara masa kwarin gwiwar cin ma nasarar abinda yasa a gaba take. Tsakaninsu da mahaifinsa ba wani canji haka yasa yaja baya dashi da 'yanuwansa da tun farko ba a nuna musu muhimmancin zumunci da junansu ba balle su kusance sa." Yayi kokarin gano dalilin rashin samun kyakkyawar kulawa daga mahaifinsu abu yaci tura a yayinda uwar ke kokarin hanashi kullatar mahaifinsa da komi cikin zuciyarsa tunda itama ta kasa gano komi zaman hakuri take duk da tana zaune dashi fisabilillah Kwatsam aka wayi gari malam ya saki Kaltume har saki uku, wannan Abu ya tsayawa Haseeb a rai, a nasa wautar yaso uwar ta zauna gidansu komi wahala amma zama ya kare. Tana gama idda ta sake aure inda Allah ya azurta ta da Yara biyu maza, Hayatu da Rabiu. Ba a taba tabbatar da hazakarsa ba saida ya shiga jami'a ya samu gurbin karatu kan koyon aikin likitanci. A nan Abdul Haseeb ke matukar neman taimako da dukkan kwarin gwiwar da ya dace iyaye da duk masu kaunarsa su bashi sai dai ina kana uban yayi alfahari da godewa Allah da ya bashi hazikin yaro amma Ina ! Bai samu ba, gashi uwa duk ta gama sayar da dan abinda ta mallaka a Kan neman ilmin da kwara daya tilo, hatta da yar gonar da tacu gado ta sayar anyi amfani da kudin basu isa ba. Shi Kuma bai son matsa mata saboda bai da kwanon abinci gidan ubansa, duk wata lalurar ci da sha da sauran abubuwan bukatunsa sun ta'allaqa ne kadai Kan mahaifiyarsa, tausayinta yake har dai da yaga mahainsa ya dara mahaifin su Hayatu karfi sosai, Kuma mahaifinsa na daukar nauyin hidimar sauran 'yanuuwansa shi kadai yake yiwa wannan yankan kaunar. Wata rana kudun sayen handout yai masa teahe ya rasa yadda zaiyi dole ya nufi wajen uban neman taimako amma me zai faru, fada ya rufeshi dashi yana fadin "Wa yace kaje ka zabi course Mai sa kashe kudin tsiya kassn ba Kai kadai na haifa ba don haka ba zan talike a kanka ba, ya wurgeshi da rabin kudin yace karya sake zuwa ya dameshi don da yai nasa karatun babu Wanda ya taimaka masa kwadago yayi shima yaje yayi ya nemi nasa. Ance gayawa Mai zuciya buki ba Mai dukiya ba, wadannan kalamai sun Kara zaburar dashi sunsa masa rai kwarai sun Kuma tunzura shi, ya zuciya, irin zuciyar da ake son yaro yayi ya ajiye girman Kai da tunanin shi wani ne ya tashi ya nemi na kansa. Ya fara yawon neman abinyi idan ya gama lectures ya shiga gari neman aikin, duk inda yaga ana gini ko aikin bulo ya nema ya tube yayi a biyashi, bashi wajen kafintoci bashi tashar mota wajen yun dako. Idan ya samu kudin aikin yinin ranar ya Kan raba uku, Kashi daya ya mikawa uwa, Kashi na bukatun yau da kullum Kashi gudan a jefa a asusu na hidimar karatunsa ne. Wata rana inda yake aikin bulo suka samu kwangilar ginawa wani dan kwangila sabin gida, a cikin maaikatar da aka dauka har dashi ga jarabawarsu ta matso ga bukatar kudin a tare dashi don haka ya kwashi takardunsa ya rinka tafiya dasu site din inda da ya samu lokacin tsaya sai ya duba tukunna kana yaci gaba da aikinsa. Lokaci lokaci Alh Muhammad Kan ziyarci site din don ganewa idanunsa yanayin aikin da ake masa, a nan ya hango wannan saurayi inda ta dade yana nazarinsa Yana karatu a natse, sau uku kenan yana ganinsa, haka kawai yaji yana son jin labarin yaron. Yasa aka Kira masa shi, ya kwaso littafansa ya zuba a jaka ya iso inda ake nemansa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66