Chapter 56
Chapter 56
goyon bayanku nike bukata sannan ku tayamu addua." Hjy Kaltume tace "Shikenan Allah yai miki albarka ya cika burunki na alkhairi. Daktan ya wani kalleta yace "Naji duk kun goyi bayanta ne, to ni kam ina nan kan bakana, idan Kuma kun matsa na amince to Kar ayi kuka dani idan wani abu ya taso nan gaba " Mahaifiyarsa tace "Wannan ne baka isa ba, ka tara 'ya'yan mutane kace ba ruwanka.". Rahima tace "Rabu dashi Hajiya naji sharadinsa na dauka Allah ya kama mana." Ya sake kallonta a fusace yace "Yanzun sai ki fadi inda kuke son ku zauna tsakanin Dorayi da Galadancin." Ta girgiza Kai "Ba ni da wannan matsayin, Kai da Aunty Zuwaira kuyi deciding Ni 'yar amshin shata ce.". Ya juya gasu Hajiya "Kunji amsar ta ko?" Hajiya ta gyada Kai "Laifi kake son Dora mata dai amma gaskiya ta fada, tabbas zabi na gareku, ta ba Zuwaira girmanta da Kai kanka." Da yaga ba zai samu goyon bayan da ya zata ba dai ya amince cike da fargaba. Yayi deciding kara gyara gidan da Rahima take saboda akwai filin da za a dora wani ginin sosai. Ba bata lokaci aka fara aikin sake tsara gidan Daktan don zaman iyalinsa. 19/09/2020, 13:57 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami 46 An kammala komi na gidan Dakta har gashi Uwargida Zuwaira da tawagarta sun rakata tarewa a nata bangaren. Yanuwanta da suka san mutunci sun shiga sun gaisa da Rahima aka taba barkwanci suka musu addua suka tafi, kawayenta kuwa sai shirmen da suka saba, hatta da falon Zuwaira Saida suka leko yanayin tsarin da Rahima ta yiwa nata suka dawo suka kwatanta irinsa, suna yo suna yar da maganganu don dai neman jidali. Bata kula ba balle tasan Allah yai ruwan tsironsu, to Rahima a banza take miskila? A wannan ranar Zuwairar ke da maigidan yadda ta shirya saboda Wai ta nunawa Rahimar ita ke da gida da maigidan ma gaba daya, to wace take yi dominta bata san arziki na bori ba. To idan ba shiririta da neman zubar da aji irin na Zuwaira ba, kowaccensu sashen daban, sai ma kaso sanin halinda yaruwa ke ciki ne zaka leka inda take, sai kuwa idan sun hadu a general parlour na gidan, kowacce tana da masu aikinta to me ye na hana Kai sukuni? Dawowar su Zuwaira yasa yaranta suka Kara shakuwa sa Rahima saboda tana jansu sosai a jikinta, ta hanyar kulawa da duk bukatocinsu ba gajiyawa, ga kokarin tarbiyyarsu da take yi tareda danta, to jama'a ko yaro yasan mai son shi. Zuwaira bata kaunar kusancin yaranta da Rahima ko miskala zarratin, da taga tayi kokarin rabasu ya faskara sai ta shaidawa abokiyar shawarar nata. Husaina ta buga kirji tace "Zauna ki saki baki galala kamar wata sauna bayan ta mallake miki mijin ta hada da 'ya'yanki kina zaune sokoko ta mallake zuciyar yaranki tas, an fada miki da bakin hura wuta wannan yarinyar ke zaune a gidan Nan?" "Da alamun kamshin gaskiya a batunki Husaina, nima zargina kenan don wallahi ko kaffara ba zanyi ba, ba haka kawai Dakta ke rawar jiki da ita ba, ke baki ga yadda take juyashi ba fa, Daktan da bana ganin tsadadden murmushinsa sai na sha ruwan dala amma ko waya yake da ita haka zaki ga yana wani rausayar da Kai Yana zuba murmushi sai kace wani sick lover boy." Husaina ta kyalkyace da dariya tace "To ai ba murmushinsa kadai ba shi kanshi tsadadden ne Zuwaira, yanzun dai meye shawara?" "Kinji kuma, ke din dai nike saurare." Husaina tace "Ya zanyi dake yanzun,kince ke ba zaki shiga malamai ba, to ki zauna ta saki a tafin hannunta ta murza ta juya son ranta, mu dai idan da malamai da bokaye a duniya mun gi karfin tsara balle irin wancan da aka dauko miki, ke Kika yi sake tun farko amma ai ba ajinki ba ce." Zuwaira taja dogon numfashi "Ai yanzun dole mu san matakin dauka that's why na neme ki." "Karki samu damuwa 'yaruwa, kin yarda ko wane irin taimako na kawo miki zaki yi amfani dashi ko?" "Me zai hana kuwa Husaina shakkun me kike?" Husaina tace "Ai dole in jinjina kar kisa in kashe kudina a banza alhalin kin san samun su da wuya." Zuwaira tasha mur tace "Ke fa problem dinki kenan in dai batun kudi ya taso alhalin ni Ina kashe miki kowacce irin lalura ba tareda jin kyashin komi ba, ke kuwa in dai za ki yi min Abu sai kiji tamkar naman jikinki zaki diba." Nan take Husaina 'yar bariki ta share wannan batun cikin dabara tunda tasan gaskiya aminiyarta ta fadi tace "Wasa fa nike miki, amma da gaske kinsaj business din mu yaja baya Kuma mijina ba irin naki bane da yake sakar miki dala kina fantamawa yadda ranki ke so, nasa Dan banzan makon tsiya, hannun nan nasa a dunkule tamkar na "yan dambe." Zuwaira ta tuntsire da dariya "Oh sharri ma za kiyi masa Kuma? Ai kuwa Yana kokarinsa shima.".. Ta tabe baki. "Me Kika sani game da mugun halinsa, ke ni fa auren ma na gaji har na nemi ya sauwaka min, in gutsire igiyar auren in yi gaba in sami Wanda ya dace dani." Ta zaro idanu "Ke Husaina ki rufaea kanki asiri, Ina ke Ina wani rabuwa da mijinki yanzun, wa zai wani aureki yanzun bayan ga 'yan matan Nan ma suna yawo a titi a mashinshini?" Ta gyada Kai "Ai da kika ganni da agenda ta, na riga na shirya komi jiran lokaci nike in gabatar miki.." "Toh! Al"amarin ba sauki kenan to Allah ya nuna mana alkhairi." Tace Amin "Bari inyi azama Kar Malam ya fita sai kin ganni." Tsakanin matan Daktan biyu zama yaki dadi,ta kowanne bangare Zuwaira bata da dama. Matsalar farko da Rahims ta fara karo da ita daga uwargidan nata itace gasa, Zuwaira irin matan nan masu shegen gasa, duk abinda taga Rahimar tayi sai ta kwaikwaya, ko silifas ta lura Rahima ta canza itama saita saya, balle a kaiga su kayan jiki ko na gyaran gida. Wasan wasa rashin mafadi, gasa idan ba na nuna bajinta wajen bautar Allah bane ya zama shirme. A ka dawo Kan abinci, a kullum mai aikin Zuwaira na yaeon gulma sa sunan tana zuwa wajen Uwale ne amma su sun San yar leken asirin uwardakinta ne, duk abinda yazo taga ana girkawa a sashen Rahima zata nade taje ta fesawa uwardakinta musamman idan Daktan wajensu yake, ita Kuma ranar nata girkin saita wanke tukunya ta kwaiwayi irin Wanda su Rahimar suka yi ta sake dafawa. Sai ayi rashi dace, Wanda akayi dominshi ba zai ci ba, Zuwaira ta fara bala'in hatta abincin ta ya daina ci sai na Rahima. Tunanin bai kawo mata dalilin rashin cin bai rasa nasaba bai dade da cin irin nau'in abincin ba kazaliza method da aka hada ma ba guda ba. Rahima ta gaji ta yanke shawarar aikawa Zuwaira ko me ta dafa. Uwale ta kalleta galala tace "Ni fa kina bani mamaki, yaushe ne Zaki yarda da kishiya har dai wace bata kaunarki har da batun Kai Mata abinci? Kin san ba zata ci na saidai ayta asara kawai. Rahima tace "Uwale kenan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66