Chapter 36
Chapter 36
yiwa kanta rigafi ta danne zuciyarta zai fi mata alkhairi. Ba sauran barci a idanunta don haka ta fito daga dakinta ta nufi kicin inda ta taras da Uwale harta kama aikin hada breakfast, tana ganin Rahima ta durkusa ta gaisheta "Hajiya barka da fitowa." Ta amsa "Ina kwana Uwale ashe kin tashi tun dazun." Tayi dariya "Ai mun saba, a can kauye ina muka ga lokacin barcin safe, muna alla-allah bayan munyi sallah mun karya kummalo da dumammen turo mu zuba hatsi a turmi mu shiga neman na abincin rana mu da yara.. Rahima tace "Gaskiya kuna kokari,kuna wahala, shiyasa akace mutum ta rinka kallon na kasa da Kai, nan zaka gane ni'imar da Allah yai masa sai Kuma ka gode masa don wasu sun fi kane Kai Kuma kafi wasu, amma gaskiya idan kika duba rayuwar matan karkara sunada matukar tausayi, sai muce mu aljanna muke." Uwale ta nisa "Ina ma ki kasan haka Hajiya, sai Kinga macen kauye a ce miki sa'arki ce ki yita rantsuwar ba haka bane don ta kusa haihuwarki a fuska, ta tsofe ta komade saboda wahala, hakora sun zube, ba isashshen ingantaccen abinci, ba hutu, na kyakkyawar muhali balle wani sutura mai kyau ga rashin samun kulawa daga mazajenmu, yawanci mazanmu fa basu San darajar mace, iyakar ki dashi ki dafa abinci, wata har noman abincin ma da ita za ayi, kiyi surfe da daka, idan ya bukaceki ya sarrafaki kamar yadda yakewa jakarsa da yake kiwo,idan kin dauki ciki ki babu wani kulawa, wajen haihuwar ma wani a rabu kacar sabida yaushe ya barki Kika je wani asibiti don inganta lafiyarki balle na dan cikin ko jariririn da aka haifa, wasu kuwa don su doki mace ba wani aibu bane a garesu, to mazan nawa ne suka san hakkokin matan da ya rataya a kansu?" Dalili kenan koda mijina ya mutu zawarawa suka yo min caa!! Nace bada Uwale ba, anyi daya ba za a kara na biyu ba, da in zauna cikin jahilci da rashin sanin me auren ya kunsa da rashin sanin hakkokin juna gara in taho birni in nemi sana'a." Rahima ta nemi kujera ta zauna tace "Bari in tayaki aikin mu ci gaba da hirar sai mu karu da juna.. Uwale tace "Ai ke Hajiya Allah ta tarfawa garinki nono, da mata na dacen irin mijinki da ba za suyi kukan komi ba, ko su Mairo da suke 'yan aiki sun shaida balle ku, kin kuwa ji ance kyakkyawar safiya tun daga maraice ake fara ganewa, jumma'ar da zata yi kyau tun laraba ake ganeta, wallahi haka nake son namiji yasan mutuncin 'ya mace. Rahima tayi dariya "Ai ko mazan namu ana samun wadanda basu San darajar macen ba, da na dauka jahilci ne yasa wasu mazan ke maida matansu tamkar jakuna ashe ba hakan bane, ko a birnin haka wasu mazan suke, kiga namiji bai san mutunci da darajar matansa ba, mace bata isa yai shawara da ita ba, don a ganinsa shirme ne, ke wani fa ya dau mace tamkar Mai karamar kwanya ce don haka baki Kai matsayin da zai fada miki wasu sirrinsa ba, sai kiji wani na kiran matarsa Wai dabba ko jaka don rashin sanin kimarta da rainin hankali, amma bai hana ya nemi biyan bukatarsa, bayan haka sukan manta mace dai ta haifesu suke mata isgillancinka bayan Allah ya daukaka darajar martabarta, saboda duk inda namiji ya Kai da mukaminsa, sarauta, jin Kai dole macen yake dawowa. Uwale tace ai baki ma san wani abu ba, mijina madokine, kina masa laifi komin kankantarsa sai ya jibgeki, shi bai kyautata yadda Allah yace ba, bai baki isashshen abinci ba, ba suturarsa fa sai an bamu kwance nida yara, ya rinka hura hanci yana tafe yana busar iska da shan kamshi sai kace Wanda aka kadawa tambari, dare nayi yaje gashi nan bisa kanki, kina gardamawa ya kile ki yayi abinda yake so, ya barki da tsamin jiki ga yunwa dake kwakularki tunda ba ki ci abinci ya isheki da daren ba, gari na wayewa ki shiga fafutukar nemawa yara kalaci. Rahima ta kyalkyace da dariya tace "Uwale Kar kisa cikina ciwo don Allah don Allah ki daina maganar mamaci haka, ki yafe masa tunda ma ai kusan lefinki ne, wa yace ki rinka gardama bayan ance idan baki amince ba kuka kwana yana fushi dake mala'ikun rahama tsine miki za suyi, Allah yai fushi dake." "Hhmmm Hajiya na sani amma sai aka ce suma kar su kyautata mana su sauke hakkokinmu a kansu, kullum ko wa'azi aka tashi sai dai kiji ana fadin mu mata mu sauke hakkokin mazajenmu, su Kuma su rinka tinkaho suna gadarar aljannar mu na karkashin duga-duginsu, suna takamar tunda ance matarka gonarka ce ka zo mata duk lokacin daka so, ko a saman rakumi ne." Rahima ta Kara kyalkyacewa da dariya "Shin Uwale zaki bari mu karya mu kimtsa ko sai kinsa cikina ya cika da dariya tukunna?" Uwale ta kece da dariya itama "Da takaici ne Hajiya.". Tace "Kuma na yarda da batunki, ya dace maza su rinka bamu darajarmu da Allah ya bamu su daina raina hankali da tunaninmu, mu ma muna da kaifin hankali da zurfin tunaninmu, mu ba dabbobi bane mun san ciwon kanmu mun san ya kamata, mun san hakkinmu, mun san nasu, ya dace ace yadda muke kokarin kyautata musu suma su kyautata mana don mu kara ingantuwar zamantakewar aurenmu. Uwale tace "Hakane wallahi,idan muna kokartawa zamu rinka ganin canji, Allah ya taimakemu. Bayan sun kammala kalacin safe, Rahima tayi wanka ta tsala kana ta rinka zagaye sabon gidan nata. 12/09/2020, 22:49 - Anty saliha: ˆRAHIMA ..doc by jami 🦈🦈RAHIMA🦈🦈 27 Zuwaira ta gyara zama a tsakiyar kawayenta taci gaba da masifa "Ku barni dashi zai dawo ya sameni, tun kafin aje ko'ina ya fara nuna injustice." Karaf a kunnin Innarta yar mahafiyarta ta kirata gefe ta fara fada "Ni fa ko da ake gaya min kina hulda da kadangarun bariki ban yarda ba sai yau dana gani da idanuna, ashe wayonki ya zan na banza tunda za kiyi sake wadancan shaidanun su rika hure miki kunni bayan duk fushin da iyayenki suka yi dake ko a jikin ki ko?" Ta turo baki kamar na jaba "To ke Inna baki ga rainin hankalin da yai min bane sai nawa za a gani don na nemi hakkina?" "Yi min shuru sakaryar banza, har wani hakki Kika ajiye? Ana tarboki kina fandarewa, to wallahi duk Kika bari iyaye suka juya miki baya sai dai ki nemi na bariki da suke zugaki." Haka al'amarin ya kasance gareta har aka watse. A can gidan amarya mutane sai sha daya suka watse sai Maryam data tsaya suyi sallama sai kuwa matar da Hjy Kaltume ta nemo mata ta rinka tayata aikin gida wace yar uwar Mairo ce. Rahima ta yaba da tsarin gidanta sosai everything looking nice and cute, ta kama hannun 'yaruwata dake tsaye tana niyyar tafiya tace "Nagode sosai Yaruwa Allah ya bar zumunci.... "Haba kanwata tsakanimu ya zarce haka, Kuma da kike ta wani godiyar gida ba fa ni kadai na tsara ba harda angonki don haka shi ta dace ki yiwa godiya." Ta zaro idanu "You don't really mean that.. Maryam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66