Chapter 19
Chapter 19
zaki so ki kula da al'amurransu ko yaushe, sannan uwa uba akwai kishi tsakanin masoya na gaskiya but ba irin kishin nan Mai haifar da zargi ba saboda da zaran Kun amince da so da kauna tsakaninku, girmamawa, yarda da aminci ne za suyi tasiri a zukatanku. Ki kula ba kowanne so ne na hakika ba, majority mu kanyi kuskuren fassara shaawa da kalmar so, irin sa za kiga ko an Kai ga aure lokaci kalilan an fara samun problem musamman idan an riga an gusar da sha'awar, hakuri da juna sai yai karanci saboda ba a gina zaman kan tubalin so da kauna na gaskiya ba. Masoya na hakika Kan jure komi don su zauna da juna. Maryam ta numfasa ta kalli Rahima kina fahimta kuwa?" Ta amsa "kwarai kuwa, karance-karancenki ya amfana ta wannan bangaren, kinji bayaninki kamar wata marubuciya?" Tace "Da kenan dana rinka mafarkin zama daya daga cikinsu.. Rahima tace "Ko yanzun kina iya farawa dauko alkalami da takarda ki gani, gashi kina tsaro min zance kamar kina karantawa ba?" "Rufan asiri don Allah, ai na kwatanta naga ba ci dole na hakura, nan na Kara yarda da batun wani malaminmu cewa rubutu baiwa ce, duk Wanda Allsh yaiwa baiwar hikima da basira yaita gode masa kullum domin a cewarsa koda mutum ya sauke kundin karatu ba lale ya iya rubutu ba, don sai in Allah ya bashi hikimar ne zai rubuta a karanta a fahimta har a sami darasi ciki a amfana, Kinga shiga hurumin da Allah bai kaddaro maka bama shishshigi ne da karanbani in dai ba so kike in rinka satar basirar wasu ba." "Ah ah a Kan me, zauna matsayin da Allah ya aje ki,in kinyi hakan ma ai baki kyautawa kanki ba ko?" Maryam ta kyalkyace da dariya "Ban ma ja da nisa ba kin sani, dana gwada naga bai yuwwa bane na hakura, na dai ci gaba da saye Ina karantawa Ina karuwa.... "Karuwa ta wani fannin ba, wani bangaren kam karatun kawai kike don jin dadin labari amma ba Kya daukar darasin komi. Da kina dauka da baki biyewa Hjy Siwaiba kunyi gaba ba, da baki bi nata Kun raba kan yaranku ba, zumunci fa kenan kuke neman yankewa tsakaninsu alhalin Ubangiji yace Duk Wanda ya yanke zumunci bai tare dashi gobe kiyoma, ban da haka, mijin Nan naku fa na iya mutuwa ya barku kowa ta kama gabanta zaman tsakaninku ya farraka, amma yaranku dole suyi zumunci da juna sabili da jininsu daya, ko Allah ya karbi ran daya daga cikinku takalihun yaran ya koma hannun dayanku dole, ko Kuma ma ya kasheku gaba dayanku, mijin naku ya auro wasu su o suci gajiyar yaran da kuke tinkahon Kun haifa, kinsan dai ba yadda Allah bai iya juya lamarinsa ba don haka ake son mu kasance masu hangen nesa, idan ka ciza ka hura, idan kace zaka biyewa zuciya sai ya kaimu ta baro tunda batavda Kashi, shyasa ake son mu rinka adduar Allah yasa mufi karfinta, Kar shaidan ya rinjayeta, ya karfafa mana imaninmu, Ni da zanga dayan marubutanmu ko dana nunaki cikin days daga cikin makarantarsu amma masu karatu suji dadin labari kawai ba daukar darasi balle ku amfana." Ta bude baki "Tafdijan Rahima yau kin gama dani tsaf... "No ba haka bane 'yaruwa, wajibine in taroki idan naga Zaki ksuce hanya in fada miki gaskiya komin dacinta, marubutan fa suna yi don gyaran tarbiyyarmu dana zuriyyarmu don al'ummanmu su samu nagarta mu gyara rayuwar duniya dana lahira." Maryam tayi kasake tana saurarenta, yes Rahima gaskiya take fada mata ba karya ko kadan, Ina amfanin badi ba rai? Wajibi ta taho ta gyara halinta dana zamantakewarta da abokiyar zamanta ko tace makwabciyar ta inji Rahima,ko bata kyautata mata don komi ba tayi don samun ladan, shin sai nawa ma wani lalura ke tasowa daya daga cikinsu Wanda suke takamar shi ya ajiyesun bai nan bai kusa balle ya magance musu? Su jawa suka taimaki juna musamman lalurar rashin lafiya maigidan na can bai ma sani ba sai ya dawo yaji labari? Idan har Ubangiji zai jarabci bawansa ba mu san ta hanyar da jarabawar zata zo mana ba kuwa ya dace mu saduda mu zauna lafiya da juna muyi hakuri tunda ba wace ke zaune kan wata, babu mai korar wata sai in kaddara ta gitta Wanda ba a fata, kowacce da halinta take zaune kota bangaren mijin ne, to wahalar da Kai na menene? Me zai hana suyi hakuri da juna har mai hadawa ya raba, ko tunanin mutuwa ya isa katsewa duk mai imani hanzari, rayuwar guda nawa take mutum ya tsaya Yana batawa kansa lokaci, duniyar guda nawa take, dubi yadda Allah ya dauke Rabiu farad daya aka raba Rahima da mijin da suke zaune lafiya, yaronta ya shiga maraici ko shi bai isa bawa tsoron Allah ba? Wannan duniyar da ba matabbata ba? Hawaye suka rinka gangarowa zuwa kuncinta. Rahima ta gani ta gigizata cikin damuwa "Lafiya kuwa?" "Hawayen godiyar Allah ne da ya kubutar dani ya ganar dani ya hana min biyewa sharrin zuciya, wallahi ba domin zuwanki na na kuduri aniyar mugun zama za muci gaba da yi nida Suwaiba don nayi sakacin barin shaidan ya shiga zuciyata ya fara dora min tubalin gina katangar da zai ci gaba da dora bulo Yana zugani Ina hauka, yanzun nasihohinki sunsa duk nayi sanyi na saduda na hakura na barwa Allah dukkan lamurrana, nayi imanin tunda bana nufun kowa da sharri zai kareni idan an nufoni, zai Kuma yi min sakayya muddin aka zalunceni." Rahima tayi murmushi "Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, munyi salati ga Manzonsa Masoyinsa Muhammad SAW, mun godewa Allah da ya baki ikon ruguje wannan ginin, Ubangiji ya Kara Mana kariya da kayangar karfe da shaidan la'ananne ya karemu daga dukkan sharrin abin ki. Abinda Nike son ki gane dukkanmu Nan masu laifi ne kullum cikin daukar zunubi muke amma Ubangiji ya Kan yafe mana idan mun roki gafararsa, wani zunubin ma ko bamu roka ba sai ya shafe mana kasancewarsa Mai tausayi da jinkan bayinsa, to kai waye da zaka ce ba zaka yi hakuri da wasu al'amurra dake faruwa da Kai ba, balle ka yafe, kana ajizi kaskantacce? Haba don Allah ki zage damtse ki bautawa Ubangijinki, ki kyautatawa mijinki, kiyi tarbiyyar 'ya'yanki, kiyi zumumci domin Allah, ki kyautatawa iyaye da yanuwa kiga irin daukakar da Allah zai miki." Maryam taja numfashi ta rike hannyn Rahima "Wallahi naji na amince na dauka na Kuma gode da nasihohinki 'yaruwa Allah ya saka miki da khairan. Yanzun kenan mun shafe chapter mutumin naki?". Ta zabura ta mike "Ina ai hankalin rabuwa yayi, Ina nan, Ina can, yanzun dai kiyi kwanciyarki don sulusin dare yayi, Sallah zanyi da adduoi na musamman in roki ya Azeez ya nuna min shi ko mafarki ne don hankalina ya kwanta." Maryam ta gyara kwanciya " In Kun hadu Ina Mika gaisuwa da jinjina masa saboda ya sace min zuciyar kanwata ya Kuma tsamota daga duhun jahilcin rashin sanin menene *so* Ta shifa toilet ta dauro alwala ta shumfiea sallaya ta fuskanci alkibla tare da natsuwa da kaskantar da Kai domin ganawa sa Mai rufan babu dogara, Mai amsa adduar bayinsa babu shamaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66