Chapter 23
Chapter 23
hakura dame? Haba Ina! Idan har shi take nufi na fasa amsa batunta, ba Zan iya zama dashi matsayin miji ba." "Kina son zancen yai tsawo kenan, shikenan mu bari har zuwa sauran kwanaki ukun data diba miki mu gani, mu ci gaba da addua Allah ya tabbatar mana da khairan" Hankalinta a tashe ta shiga tayi sallama da Hjy Suwaiba ta wuce gida. Nan da Nan Umman ta gane akwai abinda ke damunta tana cikin matsala saboda tunda ta shigo ba walwala a tareda ita, abin mamaki ko Abdul bata tambaya ba. Har zuwa karfe biyar na bayan la'asar babu canji a tareda Rahima hakan yasa a matsayinta na uwa Umma ta kira cikin daki ta yambayeta meke damunta. Nan take ta musa cewa babu komi, Umman ta kalleta cikin damuwa tace "Shikenan tunda ban isa ki fada min matsalarki ba." Rahima ta saka mata kuka tace "Idan ma akwai matsala nina janyowa kaina Umma imda nayi aurena tuni da ban shiga kangin Nan ba, yanzun ya zanyi da Raina?". Umma ta Kara rudewa "Ya za ayi in baki amsa tunda ban san damuwar taki ba?" Da yake sun saba basu boye Mata komi ta zayyane mata labarin mafarkinta da yadda suka yi da Maryam" Ta dade bata iya magana saboda zancen ya daketa itama amma ta daure ta kalli 'yarta "To in banda shirmenki mene na tada hankali harda koke-koke? Aure ba nufin Allah bane, matar mutum kabarinsa, kin taba ganin mijin da bai auri matar da ba tasa ba? Idan Allah ya kaddaro Haseeb mijinki ne babu Wanda ya isa ya hana, don haka ki natsu ki barwa Allah muga abinda zaiyi tukunna." Tasa handkerchief ta share hawayen dake fitowa tace "Ba abinda ke damuna irin alkawarin dana daukarwa Hajiya na amince da zabinta ba tare da tunanin wai shi take nufi ba, haba Umma ya za ayi wannan danyen aikin?" Umma ta kalleta "Ta yaro kyau take bata karko, tashi jeki share hawayenki, Zan nemi Hajiyar mu tattauna mai yuwwa in har hakanne." Tace "Don Allah Umma idan zaki, ki kwashe kayan Abdul ki Kai musu na hakura dashi, don ina ganin ita kanta Hajiyar sabida shi ta yanke hukuncin Nan, watau Kar in auri wani can daban in tafi dashi." Ta bude baki tana mamakin kalaman diyarta, lakle sai sunyi da gaske, tace "To Ina Kuma ruwan Abdul da za ayi masa mai gaba daya, ki bari zan maidashi gidansu idan lokaci yayi Kuma don Allah kar in sake jin kin zargi Hajiya kinsan ba zata cuceki ba, ko alama bai dace kiyi furucin da kika yi ba." Ta kwana ta yini cikin zulumi da fargaba abinda zau faru. Gaba daya komi yai mara dif, brain dinta ya hargitse, zuciyarta ta kasa sarrafa komi sai tunanin yadda akayi ta amince da so da kaunar wanda bata taba gani ba, to ai yanzun ta daina ikrarin haka, shin ba Ya Haseeb ne ta tsunduma cikin kogin soyayyarsa ba? Satin data dauka tana adduoi suka cika amma ta kekasa kasa taki komawa gidan Hjy Kaltume, bata aika an dauko Abdul din ba ma, ko da tanada tabbacin Umma ta ziyarci Hajiyar amma bata ce mata komi, ita da Baffa sun sa mata ido sai wani lallabata suke, ta share kowa a gidan hatta Maryam data taho ta rasa gane kanta. Babu Wanda bai san asibitin nan mai suna *HASEEB MEDICAL CENTRE* ba, ba don komi asibitin tayi fice ba sai domin kwarewan babban likitan(CMD). Dr Haseeb Junaid Galadanci dogo ne mai dan jiki, launin fatar jikinsa chocolate ne hakan yasa tsakar mallacin da aka yi masa suka fito sosai a gefen kumatunsa a 'yar doguwar fuskarsa wadanda suka kara fito da kyaunsa na zahiri. Yana da zafin nama sosai, hanzarin nasa ya dace da irin aikinsa watau kwararren likitan da ya shahara yai suna bangaren daya shafi rashin lafiyar kwakwalwa, kashin baya da halittun da suka danganci wadannan ababe masu matukar muhimmanci a jikin Dan Adam Dr H.J.G yadda ake kiransa yasan hallitar kwakwalwar bil adama tamkar yadda yasan tafin hannunsa, kazaliza don ya bude kan mutum ko baya ya mayar ya dinke ba wani abu ne mai wuya a wajensa ba, da taimakon Allah duk wata matsala da aka kawo masa akayi sa'a ya duba yai aiki ko bada magani a kanyi nasara. Dalili kenan da sunansa ya bunkasa tun daga gida Nigeria har kasashen waje, manyan asibitocin ketare ma dashi suke takama don ba inda kafafunsa basu taka ba. Sabida yawace-yawacen da yake yi ne yasa shi jin harsuna daban-daban, yana jin harshen larabci, faransanci, jamusanci, dangane da yaren harsunan kasarmu kuwa tun Yana jami'a ya iya yaren yarbanci, fulatanci dana igbo, abin ban sha'awa duk yaren daya juya harshe Yana yi sai mutum ta rantse daman shine mother tongue dinsa. Ganin yadda ayyuka suka yi masa yawa, zirga-zirga na neman tauyesa wajen sauke hakkin iyalinsa dana iyaye yasa ya yanke shawarar gina makekiyar asibiti Wanda ya nemi wasu kwararuj likitocin suka hadu suna gudanar da harkar asibitin gadan-gadan. Babban abin shaawa da yawanci maganar da mutane suke fadi shine ma'aikatan asibitin nada karamci tun daga leburori zuwa nurses da doctor's dinsu balle shi kanshi uban tafiyar, ta ta shahara wajen tsabta sosai, babu wulakanci tsakaninsu da patients, sun dauki Mai kudi da talaka gudane, patient sunansa patient Kuma Abu guda suka zo nema (lafiya) don haka babu banbanci. Ba nan ya tsaya ba da kyautatawa patients dinsa ba, da duk ya lakanci basu da halin biyansa hakkinsa ya kan taimaka yayi aikin kyauta tareda kulawa ta musamman. Daga bayan nan yawanci manyan asibitocin gwamnati ke turo masa da patients yai musu abinda ya dace gwamnatin ta biyasa hakkinsa. Can kasashen waje ko yaushe irin aikinsa ya taso sukan bugo masa waya ya tafi don ceton rayuwar Al'umma, a dalilin hazakarsa ne suka yiwa sunansa laqani da Mr Brain. Ga Wanda bai taba ganinsa ba kuna yin ido biyu fuskarsa zata nuna maka alamar mutum ne mai ji da kansa domin miskili ne na karshe. Wani irin mutum ne da samun irin halayensa sai an tona, fuskarsa a daure take ko yaushe, baya dariya gaban kowa amma kuma mutum ne mai saukin kai idan aka fahimci halinsa. Dr Haseeb mutum ne da bai dauki abin duniya da ita kanta duniyar wata tsiya ba face wajen gwaji da neman tsiran gobe kiyama har ya kance mutane na shirme wajen maida duniyar wajen zama tamkar ba za a mutu a barta ba, mutum ne shi mai sadaukar da kai da maida dukkan al'amurranss ga Allah. Bai da saurin karaya don haka ya fita zakka cikin abokai da sa'oinsa musamman ma da wuya suke gane inda yasa gaba. Mutum ne Mai son rayuwa don ance ka nemi duniyar tamkar ba zaka mutu ba, ya rike addininsa matukar gaske saboda ance ka gyara lahirarka tamkar yanzun zaka tafi. Ya kanyi wuya a tabashi ya hakura in dai har ya tabbatar da gaskiyarsa, mutum ne Wanda baya karya yakan Kuma kure duk Wanda ya nemi yai masa hassada har sai yaga abinda ya turewa buzu nadi. Bai da fargaba, bai da tsoro, bai da hayaniya, mutum ne natsatstse kamilalle, bai son raini don bai rana na gaba dashi ba, yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66