Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

uwarsa don da biyu taki zuwa gidannan, Nima naki aikawa dashine saboda jiran wannan ranar, sai kaje Ina saurarenki, Ina gaishets da kyau.".. Ya fita Yana murmushi itama haka. Ranar a gida Maryam ta yini, Rahima na dawowa makaranta kenan direba na ajiyesu, Walida tasa kuka bata ga Abdul abokin kirinyyarta ba, Saida aka tula mata kayan wasansa tayi shiru. Su kuma iyayen nata hidimar dora sanwar abincin rana saboda Umman tasu ta tafi Gumel dubo mahaifinsu da bai ji dadi ba, amma tana gab da dawowa, hatta yaran gidan kanninsu basa gida. Bayan sunci sun koshi sunyi sallar laasar Rahima ta shiga wanka ta fito ta sake dauro wata alwalar kana ta shigo daki ta shirya tsaf Kai kace shirin zuwa buki take. Maryam ta kalleta "Sarkun kwalliya kina burgeni wallahi karki so kiji yadda Nike sha'awar kirar jikinki 'yar caraf dake, wa zai ce wannan dafaffen cikin ya dauki da kin haihu."" Rahima ta kanne mata ido guda "Aunty Maryam sarkin mita, ke din ai kike jawowa kanki katon ciki, inda halitta da rashin kulawa, irin naman da kike dankara lafiya ne, ki ci kowanne irin nama, kisha kayan Zaki, kefa duk inda kayan dake Kara kitse suke kina Nan ya ba zaki ajiye teba ba, gaki Nan haihuwa daya kin zama wata guzuma, idan kin Kara sai Alh Abbas ya auro daidai misali don har Hjy Suwaiba barakallsh Masha Allah." Ta wurgeta da maficin dake hannunta "Shima din ba kiga yadda ya koma ba har tozon wuya ya fara fa." Rahima tace "Hhmmmm da Rabiu na nan da ya kusan kibar Alhajinku, dubi yadda ya koma kafin rasuwarsa." Maryam ta shareta, ta sake maimaitawa, a nan ta kalleta tace "Saboda Allah Rahima ba zaki bar wannan bawan Allah ya kwanta makwancinsa lafiya ba, ke kenan da duk aka tada magana sai kin sako zancensa, Ina amfanin haka, adduarmu kadai yake bukata.".. Ta nisa tareda dafe kanta "Nima bana sanin time din da nike ambatonsa Maryam, Ina kokarin dainawa." . "Ah to gara ki yiwa tufka hanci don ba namijin da zai dauki Yana aurenki kina zancen wani wanda ya rigamu gidan gaskiya." "Nace miki zan bari, da kike fadin hakan ai mijin fari wuyan mantuwa gareshi, balle ma kowa na aura dole yai hakuri dani." Ta kalleta a shagube "Sai dai kuwa idan bai sonku, muddin Yana kaunarki zaku rinka Kai ruwa rana ne, Wai ma ba haka ba ya batun Dakta?" Rahima ta canza nan take "Ki bar batun nan don Allah, ai don in nunawa Hajiyar ba Mai yuwwa bane in har hakan take nufi naki komawa gidanta, har Abdul na bar musu in dominsa suke son aikata abin kunya, ko hausawa sunce ana barin halas.... Maryam ta harareta " Jiya dominki nayi tambaya a islamiyya kan shirmen da kike yi Kuma in fada miki don kin auri Dakta ba abinda ya kaucewa shariar musulumci bane, Malam yace addininmu nai hana wa ya auri matan kani na idan Allah yai masa rasuwa hakan shuma kani na iya auren matsn Wan sa in haka ta kasance.. Har da misalin cewan ko suna da rai ce dayansu ya kamu da rashun lafiyar da ya hana yin sunna da matarsa an nemi magani an rasa na tsawon shekarun da aka gindaya masa zai sahale mata gashi ya yaba hankalinta bai son tabar gidan don kyakkyawar dabi',unta Yana iya yiwa danuwansa maganar cewan iin ya saki shu ya aureta idan sun daidaita tsakaninsu, Kuma auren ya halasta, ke dinma banga abun tada jijiyoyin wuya bayan da bakinki kika fada min kina son Daktan . Ta kauda Kai "Na dai so mutumin da aka bani labarinsa, da lamarin ya juye Kuma na sanu canjun ra'ayi. Ta wani kalleta 'Karki kawi mun burgar banza, karyarki wallahi, was yace Miki ana yiwa soyayya yankan kauna, yadda mashin son wancan ya soki kirjinki haka na Daktan zai huda zuciyark tunda batun mutum guda ake in dai dama ba karya kike ba Wanda a sanina ba a karyar so da kauna." Da taji alamun ta kamo hanya zata kureta saita canza hirar cikin dabara.... Suna cikin hirar suka ji yar karamar muryar Abdul ya shigo a guje Yana fadin 'Mami Kinga jirgina baba ya saya min." Murnan ganinsa ya rufeta, ta daukeshi tana sumbatarsa "Oyo-oyo Abdul Ina Hajiya?. Hankalin yaron ma wajen Walida, ganin hakan ta sauke shi, Walidan ta fara kukan sai ya bata jirginsa. Rahima tace Baba ya hada rigima kenan dole gobe inje in sayo miki naki jirgin". Wani yaro Dan makwabtansu ne ya shigo Yana sallama suka amsa "Wai ance ana Kiran maman Abdul a waje."... Rahima ta kakki Maryam kinji Kuma Bala da gulma shi daya saba shigowa har cikin gida a gaisa ". Maryam tace "May be sauri yake, fita kiji in zai koma da Abdul dinne tunda ban gansa da kayansa ba." Maimakon ta tsaya saka hijab, katon gyalen Maryam ta dauka ta yafa ta fita cikin sauri. 08/09/2020, 13:42 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 19 Tun daga kan soron farko kamshin turaren 'fame' ya fara dukan hancinta, zuciyarta ta fara bugawa cikin sauri, ba dai zarginta zai zan gaskiya ba? Ta karisa cikin tsakiyar soron gidansu inda tayi arba da *HASEEB* in person, rawar da jikinta ya fara, bai hanata saurin durkusawa cikin ladabi tace "Barka da yini, ya su Aunty Zuwaira?" Ko kallon arziki bata samu daga gareshi ba Ya amsa a takaice "Lafiya." Ya shiru Ta dan jima tsugunne tana jiran taji da wacce ya taho tunda bai taba zuwa gidansu ba. Da ya tuna bai da wata mafita dole ya fadi dalilin zuwansa kamar yadda yaiwa Mahaifiyarsa alkawari,ya cije, cikin isa da miskillancisa ya tambayeta "Magana ta kawo ni ko zan sami damar Fadi?" Kamar ta amsa cewan bata da lokacin saurarensa, saita tuna kaninsa,da irin girmansa da yake gani kamar uba ba wa ba, ta tuna dawainiyar da yake dasu, hakan yasa ta hadiye zuciyarta tace "Ba damuwa Ina saurarenka." Ya gyara tsayiwarsa sosai ya jingine da bango tareda goya hannayensa a kirji yace "Hajiya tace tayi miki bayanin komi don haka ba zan tsaya wani dogon bayani ba tunda kin amince da shirinta nima hakan akan dole yanzun ya rage naki kiyi shawarar yaushe kike ganin ya dace a daura auren?" Gabanta ya buga rugugu, aure? Haka ake zancen auren cikin isa da kasaitar mulki, aiki jawur, tun kafin tafiya tai nisa bata iya cewa ta fasa, daman ta amsa ne saboda bata san shine ba, wata zuciyar kuma tace zaki zan mai karya alkawari kenan wanda a addinance hakan ya zama munafuci, can ta nisa, tace "Bani da yancin kaina koda nike bazawara, iyayena keda hakkin wannan sai abinda kika ce." Shi kansa yasan nai kyauta, bai dace ya furta mata wadannan kalaman ba, ba ita ta Kar zomon ba, yaja numfashi yace "Okay zan jira su zartas da shawarwarinsu, nawa iyayen zasu taho in Sha Allah." Da yaji ba zata kara cewa komi ba,sai ya Kara gyara murya yace "Abdul kuwa bai ji dadi ba amma naga ya warware, dazun jikin yafi masa zafi." Tana dai tsugunne kanta sunkuye har zuwa lokacin, maganar da yake yi bai sa ta dago ba balle tayi responding. Ya kada Kai "Ni

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66