Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

lakanta Aunty Zuwaira irin matan Nan ne masu son rayuwar jin dadi kota halin kaka, masu son kashe kudi da neman kudin kota wacce irin hanya Kuma.. Da alamun ilmin addini bai gama ratsata ba, abinda tafi sani shine ta daura zani komin tsadarsa, ta saka latest takalmi ta rataya jika cike da dimbin naira ba tareda tunanin komi ba, tana da son cin dadi daoilin hakane yasa ko ta dafa nama a tukunyarta ka'ida ne duk daren duniya a sawo mata gasashshiyar kaza, 'yan shila, tsire ko balango taci ta kwanta. Babban abinda ya bata mamaki babu wani kusanci Mai karfi tsakaninta da mijin da take ikrari tana masifar son, kowa harkar gabansa yake..... Saida ta tabu kafadarta ta dawo daga duniyar tunani.. "Duk tunanin angon ya barki ne haka? Tafdijan da kece matar Dakta ya za kiyi?" Rahima ta share maganar tace "Aunty lokacin dora abincin rana yayi ko?" Ta zabura "Tabbas Ni bana manta inada baki cikin gidana ba, taso mu shiga kicin yau muci girkin amare." Suna aikin Zuwaira naci gaba da yi mata bayani nau'in sanaar sa take yi, Dubai take ziwa saro manyan bedsheets harda zinari, a cewarta ba zata iya wahalar karatu ko wani aikin gwamnati ba. "Me kike karantawa ne a school? Ta tambayi Rahima. Ta amsa "Special Education ne, tunda shi accountancy yake yi." Tace "Me ya kaiki karatun wani special education?" Tayi 'yar dariya "Wallahi Aunty Zuwaira Ina matukar tausayin yara makafi, gura gu da bebaye da kurame, da ma wadanda ake haihuwarsu da karamar kwakwalwa, a ganina hanyar da Zan iya taimaka musu kadai kenan." "Kice kawai kina son wahalar da kanki da rai da lafiyarki baki koyar a normal school ba sai makarantar kurame, ah ah wahala dai kike shaawa." Ta girgiza Kai "Banyi tunanin wata wahala ba gaskiya, abinda na sani shine kowanne aiki na zabawa kaina dole in zama Mai dauriya da hakurin jure kowacce irin wahala ke tattare da aikin, na zabi wannan fannin ne don bada tawa gudumuwar." Zuwaira ta gyasa Kai "Daukarwa rai dai Allah ya taimaka ai kin kusa karewa ko?" " Da ikon Allah karshen shekara nan zamu gama Basu tafi ba sai bayan laasar, zuwa lokacin maigidan ya fita tuni kafin ya fita ya ba Zuwaira kudi a baiwa sarakuwarsa. Da kyar ta amsa, a ganinta dawainyyar tayi yawa ta isa yanzun su ya rage su nemi nasu na kansu su ci gaba da kwatanta alkhairin da ake musu don shege kawai ke mance alkhairi Dan halas bai mantawa komin kankantarsa. Watanni takwas kacak suka rage su kare digirinsu na farko, cikin watannin ne Rahima ta Kara shakuwa da mijinta, kaunarsa ta fara zurfi da tasiri cikin zuciyarta har abin na daure mata Kai. Yanuwa da abikan arzikinsu sai shaawar zaman nasu suke musamman yanayin tafiyar da rayuwar auren nasu Tunda akayi auren sai Kara ji da juna suke, suna samun natsuwa da kwanciyar hankali irin wadanda ake samu muddin aka yi katari da dacen abokin zama, ba abinda yafi musu dadi illa Kara fahimtar juna da suke ko yaushe. Rahima bata da damuwar data wuce taga ta kare karatunta lfy, bayan so da kaunar mijinta tayi dace da sarakuwar da take ji tamkar ita ta tsugunna ta haifeta itama, koda wasa Hjy Kaltume Bata son ganin bacin ran Rahima ko na dakika gudane, duk abinda ta samu indai naci ne sai taba Rahima taci kafin takai bakinta, idan kudine ko yaushe tana tattalin ta bata su Wai karta zauna baby na kashewa, dangane da abubuwan hidimomin yau da kullum kuwa kamar su man shafawa sabulu wanka dana wanki duk wata zata kebe kudu a sayo ta kirata ta damkasu a hannunta, kayan lashe-lashe da tande-tande ba a maganarsu, ita dai Kar Rahima ta nemi komi ta rasa. Ita Kuma bata zubar sa tarbiyyar da akai mata tun a gida ba, daraja na gaba ko a Ina ne musamman tsoho, to ta mutunta wadanda bata San inda suka fito ba a titi ballanta uwar mijinta Mai kaunarta tamkar ta lasheta. Sai ya zama cikin surukanta babu kamar Rahima ba don ta kasance matar Dan autanta ba ah ah kima da girmamatan da take yi tun zuwanta gidan ya haifar da hakan. Kafin su fara karatu gadan garan ne suka shirya suka nufi Gumel gano kakanta da sauran dangin mahaifiyarta, duk sati zasu ziyarci gidajen 'yanuwa ba inda ta tsani zuwa sai gidan Hayatu sabida rashin zaman lafiyar da matansa keyi, ta tsani tashin hankali. Ba zata manta ba ranat da suka fara zuwa gidan ta riga Rabi'u shiga ciki tayi sallama aka amsa ta durkusa don gaida matar data gani zaune bakin famfo tana wanke-wanke, ta dago Kai ta Mike tsaye tana fadin "Lalle yau nayi farin gani, amarya Ina angon naki?" Kafin ta amsa Rabiu ya sallama yace "Aunty amarya gamu mun taho me kuka aje mana?" Sai nan Rahima ta gane wannan ce amaryar Yaya Hayatu sunanta Haulatu... Haulatu tayi dariya" Me kuka kawo mana goron amarci dai, ku shiga dafa ciki ka barta a tsakar guda tsaye." Yai musu jagora zuwa dakin uwargidan suka sallama bata amsa ba sai da ya daga labulen dakin suka ganta zaune abinta, Rabiu ya shiga ciki Rahima ta bishi syka zauna suka gaisheta ta amsa a ciki, suka zauna shiru-shiru na mintoci bata Kara ce musu kanzil ba, ya kada Kai ya umurci matarsa ta tashi su tafi, suka sake mara sallama ta share, suna fitowa suka shiga dakin Haulatu don su sake gaisawa itama su bata hakkinta, ita Kam tayi ta jansu da wasa har ruwa ta kawo musu da lemu tace su tsaya suci abinci kuma.. To ai kuwa zaman nan da suka yi dakin amaryarta ya tunzura Jamila, ta fito tsakar gida ta shiga masifa tana sakin habaici "Ahayye ayyririru, yau Ni za a gwadawa gulma da makirci irinta dangin miji, dadin abin kafin a auro wata Ni aka fara gani da sani dole a zauna dani komin kiyayya, magulmatan banza munafukan wofi.".. Ba Wanda ya futo balle ya tanka mata, ana haka Allah ya dawo da Hayatu gida daga wajen aiki, malamine a makarantar Shekara. Yana shiga gidan nasa yai katarin surutan da Jamila ke Fadi, Rabiu na jin muryarsa danuwansa ya fito Rahima ta biyo shi suja gaishe shi Yana amsa yace "Lafiya meke faruwa Rabiu?" Ya shafawa idonsa toka yace bai sani ba ya tambayi matarsa. Jamila tayi farat ta amsa "Dole kace baka sani ba mana algungumi, ka dauko wannan kekasasgahiyar matar taka Kun haddasa fitina, ta juya Kan mijin wallahi kayi mishi kashedi, hawainiyarsa ta kiyayi ramata.... Hayatu yaji zata zake ya buga Mata tsawa "Ke ar wallahi ko ki min shuru ko ranki ya baci sai in tattakaki yanzun nan inga me za ayi mutumiyar banza, ni kenan bani da ikon fita in dawo in tadda gidana lafiya, kaina farau aje mata biyu? To wallahi kinyi kadan, duk iskancin da za kuyi ku tsaya kaina Kar shegiyar data shiga sabgar 'yanuwana, sakararu marasa tunanin abinda zaije ya komo." Kafin ayi haka Haulatu ta banko labule ta fito a fusace " Ah ah Hayatu wasa yai wasa banda tsikarin uwar miji da tabarya, mene nawa a ciki Ni da na tarbesu nace su

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66