Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

wata jakar leda ta mika masa, Ina gaida yaran da Auntyn da jiki.". "Sai na kira." Ya fadi a takaice "Karka damu kanka Yaya in don Ni, mu kwana lafiya." Ya tsaya kawai yana kallonts, shi a ganinsa ma alla-alla take ya bar mata gidan tana korarsa don rashin damuwa da al'amarinsa, bai san daurewa take ba, na ciki na ciki." Har ya saka kafa daya a kofa zai fita ya fasa ya juyo gareta "Zo amshi nayi mantuwa.".. Ta tako ta iso gabansa, ji kawai tayi ya rungumeta yai mata kyakkyawar kiss da numfashinsu ya balaguro na dakikoki kafin ya saketa, ya fita ya barta a tsaye. Ta girgiza kai da yai mata dum ta taka a hankali ta koma kujera ta zauna tayi jum har saida ta daina ganin jiri-jirin da bugawar zuciyarta ta haddasa mata, hankalinta ya dawo jikinta, cikin natsuwa ta dauki gift din da ya bata ta fara ciro wasu kananan cards da wani sansanyar daddadan kamshi ke fitowa daga garesu, ta ajiyesu gefe, ta dauki wani gift din da aka yi wrapping ta bude tacu karo da wani karamin box mai kyaun gaske na glass, to ba dan akwatin ba abinda ke cikine ya burgeta, cike yake da ruwa taf, kasansa kananan kifaye ne da mami wota a tsakiyar ruwan, ta kurawa gift dinshi ido cikin tambayar why zai bata kyautar Nan, meya hadata da *Mermaid* Kuma?, Ga Kuma wani key holder da aka yiwa design na wasu kifaye biyun manne da juna jikinsu nata walkiyar ruwan ruwan azurfa, daga jikinsu aka rubuta sunanta wanda sai an kura ido za a gani. Ta ajiye wadannan bisa cinyarta ta dauki cards din ta bude tana karantasu daya bayan daya, kalaman da aka tsaro cikin na karshen yafi daukar hankalinta, ta sake karantaea a fili *I enjoyed your company so much, that I will like to enjoy it again, I never knew that you could give so much fun... I used to think that you're always shy* Kamshin turaren *Impression* ya cika mata hanci, jatta hannayenta kamshin turaren Ya Haseeb suke, ta mike ta adana cards din kana ta yiwa dan box dinta na fishes mazauni kan bedside drawer dinta. 17/09/2020, 16:22 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami 42 Yana shiga gidan da sallamarsa ta doka tsaki ba amsawa ba sannu da zuwa balle yaji sanyi a kokon ransa. Bai kula ba Kai tsaye ya wuce sashensa ya gama abinda zaiyi ya sake fitowa, yaransa na zaune a falo suka rugo ya rungumesu "Dama kuna cikin gidan Nan?" Abdul ya nuna uwar "Mummy ce ta hanamu fitowa." Yace "Ba komi, baku tambayi Dan uwanku Abdul ba " Nan da nan suka ce "Ka taho mana dashi ne Baba?" Ya girgiza Kai "Ah ah amma ga sakonku inji Aunty Rahima." Har suna rige-rigen karba, suka zazzage kayan kwalam din da ta ciko musu leda dashi suka baje kowanne ya dauki abinda yake so ya fara ci, Zuwa ta mike ta fisge na hannun kowanne ta zubar tasa kafa ta tattake sauran tana tsiya " Aikin banza da wofi, ni za a nunawa yarana iya hila, Kai ka gaya mata 'ya'yanka basu cin irin wannan da za a kwaso tarkacen banza kayan zawo a kawo musu?" Yaran suka fashe da kuka, ta bisu zata bubbugesu ya kamasu ya rungume, bai ce da ita komi ba sai rarrashinsu yake "Me kuke son ci yanzun?" Khalifa yace *Ice cream?* Yace "Okay ku zo mu tafi a sawo. Tana ganin sun fita ta biyo bayansa "Ni ban yarda wani ice cream za a sayowa ba, can din dai zaka koma.". Tankawa yabawa, ya saka yaransa a mota yaja suka sake fita gidan. Tana ganin haka ta ruga cikin gida ta dau waya ta dannawa aminiyarta Husaina kira, tana dauka ta fara "Ke ni fa nayi yadda kika ce banga alamar zai canza ba, wallahi ko a jikinsa bai kulani ba, ya mai sheni wata mahaukaciya." Husaina tace "Tunda hakan bai tasiri ba, ba zamu ciwo kansa ta hanyar tsiya ba kenan, yanzun ki kwantar da hankalinki itama ki nemi shiryawa da ita Amma ba farad daya ba don karta dago manufarmu, data saki jikinta dake sai mu far mata." Zuwaira tace "Nima naga hakan zai fi gaskiya don a kyaleka kayi ta haushi kai kadai kamar wata karya da takaici sosai." "Ai ke Zuwaira na rasa abinda yasa kika lakewa namiji kwara daya tal yana wulakanta ki sai kace shine autan maza, yana sonki zai miki kishiya kuma ma matar kaninsa?" "Hhmmm zaki gane bane Husaina, sai wata zuciya tace in rabu dashi wata ta rinka kwadaita min irin dacen da nayi dana sami miji irinsa, ke wallahi Dakta fa gwarzon namiji ne, duk macen data dandani zumarsa ba zata iya rabuwa dashi ba ( kunji sakarcin banza, ahir dinku mata wajen tona sirrin aurenku. Tuni ya dace Zuwaira ta fahimci manufar kawarta a kan mijinta ko don yadda ta kan rinka kyaun likitan ko yabon halinsa da sauransu, sakarcinta ya hana, to gashi tana Kara kwadaita mata shi, Allah ya ganar da ita) my To gashi dai ta bata shawara kamar kullum ko zata dauka oho. Kafin Daktan ya dawo da yaranta tayi wanka ta kalelaita jiki ko'ina ta zauna jiransa... Yana tuki yana dan waigen yaran nasa guda biyu da Allah ya bashi, duk sunyi barci, tausayinsu ya kamashi, su dai kam ba suyi dacen uwa ba, gaba daya ya sabo su ya shigo cikin gidan ta wuce dasu dakin barcinsu ya shimfide, ya tofa musu adduoi ya rufi musu kofa ya wuce bedroom dinsa yai kwance ya rufe ido yana nazarin al'amurran rayuwarsa da irin destiny dake playing role hanya daban-daban. Ya kalli agogo, karfe sha daya saura na dare, tasan zaiyi wuya ace Rahima tayi barci by now don macece mai son raya dare da ibada, son jin muryarta ya tsananta a garesa ya kasa daurewa, nan take ya zaro wayarsa ya kirata. Tana dagawa ya fara tambayarta "Ya kin taho da Abdul din?" Tace "Eh ya biyoni da kyar may be don bai ganka bane, Ni na rasa dalilin da yasa bai son zama a wajena." "Karki damu kanki kinsan Dorayumi is a new place a gareshi, zai saba a hankali, be patient with him.' Daga nan duk sukayi shiru, ba abinda ke bakanta masa rai da ita irin miskillancin ta, ko shi kadai take yiwa hakan? At least he has done his best ta bangarensa wajen kokarin sakin mata fuska ya aje nasa miskillancin but taking ta warware, me take son yai mata Kuma? Wani dogon tsaki ya fito daga bakinsa, Mata ko!! Idan mutum ya biye musu sai hallakar dashi wallahi, but shi din ya riga ya amincewa zuciyarsa yana son matarsa, son da ya kebe a wani bangaren na zuciyarsa, may be idan taji hakan ta dan rangwanta masa... Zuwaira ta sallama ta shigo,bai daga ido ya kalleta ba har ta zauna, ta dauki 'yan mintoci ba tace komin ba itama, shi Kuma yaci gaba da maganarsa "Mu kwana lafiya, I will call you again." Ya ajiye wayar ya juyo kan Zuwaira yace "Kinga idan ba maganar arziki ta kawoki ba don Allah ki sarara min ga hanya ki fita ki ban wuri

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66