Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

Yana mai sakin kyakkawar ajiyar zuciya yace "Ni kuwa ni'ima nike ji duk lokacin dana kalleki, shin Rahima kinsan irin mutuwar son da nike miki kuwa? Ta rufe bakinsa "Rayayyen so dai mijina idan kace mutuwa ai ba zance kenan, na yarda da so da kaunarka, nima hakan yake a zuciyata, domin Ubangiji ya karfafa mana dankon soyayyarmu ne ya bamu wannan." Ta kamo hannunsa ta dafa cikinta. Da farko bai fahimci inda zancen ya dosa ba, daya dago ya zabura ya cakumota ya riketa gam ya fara tsalle Yana sumbatarta "Da gaske cikine dake Rahima alhamdulillah." Tace "Da gaske Ina dauje da bebinka Rabiu amma idan baka daina juyi dani haka a tsakar daki ba zamu ita rasawa don likita ya shaida mun saina rinka kukawa in bi a hankali mahaifata Bata da kwari. Nan da Nan ya ajiyeta a hankali yace "Are you ok?" Tace "Banda wata matsala sai adduar Allah ya rabamu lfy." Murna ta rufesa ba sauran barci kenan, ya zauna ya fara plan din tarbon jaririn da sauran kusan watanni bakwai kwarara kafin ya fito duniya. Alla- alla yake ya kare sallar asuba, ya shuga gaida Hajiya yai Mata albishir, saboda tsabar farin ciki ranar tuni tayi Bata ci komi ba, farin ciki ya kosar da it's, can gidansu Rahimar ma abinda iyayenta suka kashe suka tsare kenan, jiran ranar haihuwar 'ya'yansu biyu, Maryam da Rahima. 04/09/2020, 13:45 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 10 Lokacin tafiya bautar kasarsu yazo, Rabi'u ya shiga ya fita aka barsu a garin Kano, inda shi yake Bank Rahima Kuma ke koyarwa a makarantar kurame. Watanni bakwai da 'yan kwanaki Rahima ta kamu da zazzabin malaria, Rabi'u ya rikice musamman da yaji likita ya gaya masa ba a son mai ciki ta kamu da zazzabin saboda yana iya haddasa miscarriage ko yaiwa uwar lahani. Kowa ya dukufa adduar Allah ya bata lafiya ya kareta da abinda ke cikin, kwana biyu kamar taji sauki ana uku zazzabin ya dawo wannan karon hade da ciwon baya da mara. Likitoci sunyi kokarinsu amma kafin awa guda nakuda ta taso haihuwa ce gadan-gadan, da taimakon Allah ta haihu lafiya ta sami danta bakwaini. Iyaye da 'yanuwa da abokan arziki suka cika asibiti sai dai kash da kyar aka barsu suka ga jaririn a hannun nurse aka wuce dashi aka saka shi cikin incubator sabida bai gama yun kwari ba ga rashin lafiyar jundice da akan haifi wasu jariran dashi. Ba a sallamesu ba sai ana gobe suna tare da gargadin Kar a bari a rinka daukar yaron gudun jagwalgwalo Hajiya Kaltume ta Kira Rabiu don su shawarata sunan da za a sanyawa jaririn yace "Hajiya na riga nayi masa huduba tun ranar da aka haifesa kinsan addini ya koyar daamu da zaran an haihu mu yiwa yaranmu huduba,bayan munyi musu Kiran sallah da kalimatu-shahada a kunnuwansu ba sai an jira sai wani ranar suna ba. Koyar Manzon Tsira ne." Tace "Naji ustaz, wane suna ka saka masa Ina fatan ba irin na zamanin nan masu wuyan Fadi ba." "Ko daya, wannan ko sau nawa zaki iya fadi cikin mintu guda kacal." "Wai zaka fada min ko sai ka gama ja min rai Rabi'u?" Yayi dariya "Sunan Ya Haseeb yaci, Abdul Haseeb karami ne Hajiya." Ta gintse dariyarta tasha mur "Maimakon ka sa sunan mahaifinku da Allah yaiwa rasuwa, mene naka na saka sunan wanda yake raye?" Rabi'u yace "Ina Sunusin Ya Hayatu sunan baban yaci Hajiya, tunda yasa ba lale nima sai na saka ba, bukata a samu magaji an samu ai, ba Kuma sai mutum ta mutu ake saka sunansa ba, Hjy Ya Haseeb ya cancanci wannan adalcin daga garemu din da taimakonsa Allah ya hadamu aure, don haka kiyi fatar alkhairi kawai.". Daman ba Wai bata ji dadi bane, ah ah ta yaba da kaifin hankali da tunaninsa kwarai, ta gyara zama tace "To Rabiu Allah ya raya mana shi yasa dadin musulmi ne yasa ya gaji mai sunan." "Yauwa yanzun ki Kai magana, Ameen Hajiyata." Anyi suna an ci an sude, Hasseb babba yana can wani aiki a babbar asibitin dake kasar Morocco, sai labarin haihuwar yaji da labarin anyi masa takwara. Da zai dawo sayayyan musamman ya yiwa uwa da namesake dinsa din nuna jin dadin karamcin da aka yi masa, yazo har gida yaga jaririn da ake fadin yafi kama dashi a bisa mahaifinsa. Cikin watanni biyu Abdul Haseeb ya murje yayi 'yar kiba har ya fara wayon gane iyayensa da kakarsa da yake yini can wajenta. Suna gab da kare bautar kasa wata rana, Rahima ta gama shiryawa maigidan abincin rana ta girka masa tuwon shinkafa miyar alayyaho abincin da yafi so kenan, sai gashi ya dawo ya hayo sama dauke da Abdul a kafadarsa yana rike da jakar aikinsa a hannu daya. Ta tarbesu ta amshi jikar tana masa sannu, ya amsa Yana ci gaba da yiwa dansa wasa, ta tsaya ta zuba tagumi tana kallonsu tace "Kana bani mamaki, yanzun daga shigowarka kaje ka dauko yaron nan ko kunyar Hajiya baka ji, haba ana son kawaici don Allah." Ya kyalkyace sa dariya "Ita Hjyr bata damu ba, ki tuna tun safe yake wajenta sun yini tare, Ni kuwa sai yanzun na Sami damar wasa dashi." Ta kalli Abdul "Hhmmm ko baka koya masa kimi ya koyi kyuya, duba yadda ya kura maka ido Yana kallonka." Rabiyu ya zaunar da Abdul bisa cinyarsa yace "Da Kuma fa gaskiyarsa gashi ba nine babansa ba." Ta bude baki cikin mamaki "Ba kaine ba to waye ubansa?" Ya amsa "Maida wukar, nina haifi abina mana Amma Ya Haseeb ne babansa." Ta hararesa cikin wasa "Tunda aka haifi yaron nan kake wannan furucin, kowa yasan a mtsayinsa na yayanka dole a kirasa baban Abdul ka taba ganin an raba anta da jini?" Yace "Inda Mai iyawa ai sai a basa ya gwada mu gani." Ta gyara zama "Hhhh Ni dai kawo sa kaci abinci." Ta karbesa ta goya, ta jera masa abincin ta zuba masa suna hira, yana cin abincin yana dan tsayawa , can ya ture plate gefe yace "Na koshi." Ta kallesa cikin damuwa" Abinda na lura kwanannan baka son cin abinci ka koshi har ka fara rama, wani Abu na damunka ne?" Ya girgiza Kai "Ba wani abu bane, just cikina ne ya cushe ko naso cin abincin sai inji na koshi dole nakan hakura." Tace "To muje asibiti mana, mutym ya zauna sa cuta a gida?" Ya taso ya dafa kafadarta "Karki damu kanki da yawa, dazun da ya taso min a office Nan da Nan na ziyarci clinic dinmu suka ban magani nasha naji dadi wallahi sai anjima karfe tara na dare zan Kara sha." Fuskarta ta canza "Rabi'u baka da lafiya ka boye min?" Ya rungumota "Afwaan Rahima ba wani sabon Abu bane da baki sani ba, kinsan na kanyi ciwon ciki muna school amma after 3-4 days nakan sami sauki inci gaba da harkokina, a gaskiya na dade ma banji ya tashi ba that's nima ban koma asibiti ba amma insha Allah gobe sai mu tafi." Tace "A takaice ma baka San kowacce irin cuta ke damunka ba." Yace "Sun Fadi Amma ban wani rike ba na manta." Ta sassauto "Hhmmm to Allah

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66