Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

kyau tun laraba ake ganeta, wallahi haka nake son namiji yasan mutuncin 'ya mace. Rahima tayi dariya "Ai ko mazan namu ana samun wadanda basu San darajar macen ba, da na dauka jahilci ne yasa wasu mazan ke maida matansu tamkar jakuna ashe ba hakan bane, ko a birnin haka wasu mazan suke, kiga namiji bai san mutunci da darajar matansa ba, mace bata isa yai shawara da ita ba, don a ganinsa shirme ne, ke wani fa ya dau mace tamkar Mai karamar kwanya ce don haka baki Kai matsayin da zai fada miki wasu sirrinsa ba, sai kiji wani na kiran matarsa Wai dabba ko jaka don rashin sanin kimarta da rainin hankali, amma bai hana ya nemi biyan bukatarsa, bayan haka sukan manta mace dai ta haifesu suke mata isgillancinka bayan Allah ya daukaka darajar martabarta, saboda duk inda namiji ya Kai da mukaminsa, sarauta, jin Kai dole macen yake dawowa. Uwale tace ai baki ma san wani abu ba, mijina madokine, kina masa laifi komin kankantarsa sai ya jibgeki, shi bai kyautata yadda Allah yace ba, bai baki isashshen abinci ba, ba suturarsa fa sai an bamu kwance nida yara, ya rinka hura hanci yana tafe yana busar iska da shan kamshi sai kace Wanda aka kadawa tambari, dare nayi yaje gashi nan bisa kanki, kina gardamawa ya kile ki yayi abinda yake so, ya barki da tsamin jiki ga yunwa dake kwakularki tunda ba ki ci abinci ya isheki da daren ba, gari na wayewa ki shiga fafutukar nemawa yara kalaci. Rahima ta kyalkyace da dariya tace "Uwale Kar kisa cikina ciwo don Allah don Allah ki daina maganar mamaci haka, ki yafe masa tunda ma ai kusan lefinki ne, wa yace ki rinka gardama bayan ance idan baki amince ba kuka kwana yana fushi dake mala'ikun rahama tsine miki za suyi, Allah yai fushi dake." "Hhmmm Hajiya na sani amma sai aka ce suma kar su kyautata mana su sauke hakkokinmu a kansu, kullum ko wa'azi aka tashi sai dai kiji ana fadin mu mata mu sauke hakkokin mazajenmu, su Kuma su rinka tinkaho suna gadarar aljannar mu na karkashin duga-duginsu, suna takamar tunda ance matarka gonarka ce ka zo mata duk lokacin daka so, ko a saman rakumi ne." Rahima ta Kara kyalkyacewa da dariya "Shin Uwale zaki bari mu karya mu kimtsa ko sai kinsa cikina ya cika da dariya tukunna?" Uwale ta kece da dariya itama "Da takaici ne Hajiya.". Tace "Kuma na yarda da batunki, ya dace maza su rinka bamu darajarmu da Allah ya bamu su daina raina hankali da tunaninmu, mu ma muna da kaifin hankali da zurfin tunaninmu, mu ba dabbobi bane mun san ciwon kanmu mun san ya kamata, mun san hakkinmu, mun san nasu, ya dace ace yadda muke kokarin kyautata musu suma su kyautata mana don mu kara ingantuwar zamantakewar aurenmu. Uwale tace "Hakane wallahi,idan muna kokartawa zamu rinka ganin canji, Allah ya taimakemu. Bayan sun kammala kalacin safe, Rahima tayi wanka ta tsala kana ta rinka zagaye sabon gidan nata. 29 Gidan Rahima sashe-sashi biyu ne sai fili daga can gaba, ginin kansa ya tsaru sosai, ga furanni masu fitar da kamshi daban-daban, tun kafin ta tare saida aka yi mata saukar qur'ani da adduoin neman tsari da albarkar zaman baki daya.. Sun gaisa da maigadin Mai suna Mal. Hassan yayinda dansa Haladu ne zai rinka yi musu wanki da guga da share-sharen waje da gyaran shukoki. Sha daya amaryar ta fara baki, zuwa azahar sai ga uwargida Zuwaira da tawagarta sun danno mata baya, suna mata kirari "Sai ke uwargidan likitan likitoci.. Tayi musu maraba cikin ladabi, ta gaishesu suka share, tasa Uwale ta kawo musu kayan motsa baki dasu lemu shima ko kallo balle su dandana sai sakin magana suke. Ba inda Rahima ta burge kowa sai da taki kulasu tayi tamkar bada ita suke maganar ba don ta lura so suke ta tanka su ci mutuncinta, da taga haka maimakon suyi tafiyarsu sai ta mike tace su biyota wai suga cikin gidan, kawayen Zuwaira su bakwai suka bita duu tana gaba suna biye, Saida suka gama zagaye ko'ina kana suka dawo falo ta tsaya a gaban Rahima tace "Miko min key din dakin Dakta sabida Nan ne kadai ban shiga ba." Cikin natsuwa Rahima tace "Kin dai shiga inda suka dace ki gani, inda kike batu yanzun kuwa sai ki jira amincewar mai dakin tukunna in ya dawo." Kawar Zuwaira Hussaina ta girgiza Kai "Lalle yarinyar nan taga gadon barcinki ta rainaki wallahi." Wata cikinsu kuma tace "Ya dace ji nuna mata da gidan da maigidan dyk mallakin kine." Tana wani jijjiga jiki kamar Mai shirin hawa bori tace "Ki kiyayeni wallahi, zaki bani ko sai rayuka sun baci tukunna?" Rahima ta yunkura ta mike tsaye ta bisu da ido tace "Kin ban mamaki Aunty Zuwaira da zaki tsaya kadangarun bariki na hura miki m wuta a gidanki. Da akwai girma da arziki watakila in daure in baki keys that's in ke kadai ce ma, amma yanzun ba Zan iya ba, kiyi iko da naki gidan inyi da nawa, abu na karshe Ina rokon don Allah ki kwashe tarkacenki gayyar na ayya kuyi gaba. Daga yau idan ba girma da arziki zai kawo ki ba please Kar ki sake zuwa min gida, nagode da ziyara, Kuma a rinka taka tsantsan da duniyar nan tamu mai halin Dan mangwaro, sai kana shansa dadi ya fara tsumaka ya subuce maka, hakan nan ita din rawar 'yan mata ce, na gaba Kan koma baya... "Tafdijan! Lalle wuyar yarinyar nan ya isa yanka, to ke Kyaleta za kiyi Zuwaira ta rainaki a gabanmu?" "Zuwaira ta cika tayi fam tace "Wai ita 'yar gani lasheni.. Daya kawar tace "Ba ki sharara mata mari ta gane banbancin aya da tsakuwa?" Kamar go ahead kawai take jira ta daga hannu zata kaiwa Rahima mati, tayi wuf ta rike hannun cikin sa'a tana girgiza kai "No Aunty Zuwaira Kar ki fara, duk haukar da za kiyi zan kyale but Kar kiyi mistake din hannunki ya Kai ga jikina, don ni din Dan hakin daka raina ne, Ina iya tsone idanunki." Zuwaira tayi kokarin kwace hannunta ta kasa, kawayen nata na ganin haka suka tasowa Rahima haikan, ta kallesu a wulakance tace "Duk wace ta matso kusa dani sai buzunta." Suna cikin haka tawagar iyalan gidansu Haseeb dana bangaren su Haj. Kaltume suka shigo, kanwar Hjy Kaltume mai suna Hjy Iya ta rafka salati sauran jama'aa suka dauka suma "Me zan gani Rahima? Ta saki hannun Zuwaira tace "Tambayi Aunty Zuwaira... Ta juya wajen Zuwairan tace "Ya kike son zubar da girmanki, anyi bukin nan an watse lafiya, meye na tayar da husuma, tunda Allah ya hadaku zaman tare ba sai kuyi hakuri da juna ba, mijinku na can na nema muku abin rufin asiri, ku kuna nan gaban jama'a kuna zubda mutuncinku, ina amfaninsa. Zuwaira ta figi gyalenta ba tareda Kara cewa komi tace wa mutanenta "Mu tafi, ai zamu sake dawowa." Suna fita mutane suka shiga tseguminsu, Rahima ta katse su "Ni dai ku daina cin namansu din Allah, kuyi musu adduar shiriya idan zaku iya, idan ba zaku iya ba kuyi shiru." Da dare ne Maryam

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66