Chapter 59
Chapter 59
suka mike cikin farin ciki, Khalifa ya kama hannun Abdul yace "Mama mu kwana a can?" Ta gyada Kai"Manufata kenan, oya, ku wuce ku bamu wuri " A guje suka fita sunata murna, shi kuwa yana zaune tamkar baiji diramar da suke yi ba duk da kasancewar yaji dadin furucinta ba zai nuna ba domin gudun ko halin neman maganar ce nata ya taso ko da wata manufar ta aikata hakan. Ta bude baki zata yi masa magana kenan sallamar Husaina y katseta, kafin ayi mata iznin shiga ta shige, masifar kamshin turarenta mai shegen hawa kai ya da doki hancin Daktan, yai saurin mikewa, ita Kuma ta rusuna cike da ladabi na kissa ta gaishe tana wani kashe murya sai kace karuwa, ya amsa a dakale ya nufi sashen sa. 20/09/2020, 12:08 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by jami 49 Husaina ta kalli tace "Ni dai da sa'a nike, duk lokacin dana taho sai in tadda Oga na gida." Takaicin furucinta yasa Zuwaira shan mur, a zahiri kuma ta gaji da irin dirar mikiyar da aminiyar nata ke mata, bata taba zuwa gidanta sai ranar girkinta ta kuma tabbatar da zata sami Daktan a gida me take nufi? Kalli irin shigar data yi ma, har tana wani rausaya murya kasa -kasa don zata gaisheshi.... Husaina ta mike kafafunta ta kalli 'yantsun hannunta da faruttan da suka ci adon jan farce ta yaba da kanta tukunna sannan ta tabo Zuwaira "Meye matsalar naga kinyi shiru fuska a daure" Zuwaira ta kalleta a shagube "Wace irin matsala bayan kin shigo kin ganni muna zaune lakadan muna hira da mijina! Ta kura mata ido na dakika guda "Zuwaira kenan ni banga hakan ba yanayin murtuke fuskar da yayi, da kyar fa ya amsa gaisuwata, shine kike ban mamakin rabuwa dashi ki huta tunda ba kanin tsohonki ba ne." Kalamanta sun yiwa Zuwaira daci amma ta daure tace "Ba zan rabu da mijina ba Husaina tunda Ina son abina." Tayi wata 'yar shewa irin tasu ta 'yan duniya tace "Aiki ya ci sai ki kawo kudin biyan Malam." Zuwaira ta tabe baki "Ina ce sai an ga fa'idar abu ake biya?" "To a cewarki komi normal sai ki biyani." Zuwaira ta gyara zama ta kalleta daidai ta mika hannu ta dauki cup din da Daktan yasha lemo bai shanye ba shigowarta yasa ya aje cup din ya fita, ta Kai bakinta kenan Zuwaira ta kabe cup ya fadi ya fashe. A fusace ta zabura "Kan uba! Wane irin iskancine kike ji ne yau?" Zuwaira ma ta zaburo ta mike a fusace "Ha ki nan babbar 'yar iska da kike neman raina min hankali, ki rasa cup din da zaki sha lemo sai wanda mijina yasha a ciki?" "Ke din ce babbar 'yar iska har yaushe kika san darajar mijin da kike kuri dashi, yanzun me Kika san mutuncinsa?" Maimakon amsa mari Zuwaira ta shararawa Husaina..tace ki sake kirana 'yar iska kika yadda zanyi dake... Husaina ta rike kuncinta ta saki ta dunkula hannu ta sakarwa Zuwaira a ciki, ba sai dambe ya kacame ba, nan Mai aikinta ta saka ihu ta ruga sashen Rahima ta fado mata tana kuka. Rahima da Uwale suka rugo a guje, inda ta shiga tsakiyar aminan sa idanunsu ya rufe saboda masifa ba su ga zuwanta ba, wani cup din Husaina ta raruma ta wurgi Zuwaira dashi ta kauce bai sameta ba sai Rahima ya yanketa daidai saman girar ta. Jinin da suka ga yana zuba yasa suka daina masifar, Husaina ta suri Jakarta ta barta gidan a guje, Zuwaira da Uwale suka yo Kan Rahima suna mata sannu, nan take dai aka dauko first Aid kit aka wanke ciwon aka tsaida jinin kana aka rufe da plaster. Jikin Zuwaira yai sanyi sosai ta shiga cikin damuwar abinda zai faru da zaran maigidan ya dawo. Rahima ta lura tace "Don Allah ki kwantar da hankalinki tsautsayi ne Wanda ba a sa masa rana." Ta kalleta cikin jin nauyi sabida irin surutan da Husaina ta rinka barbadawa da gayya kuma tasan Rahimar da yaran gidan ma sunji (masu musu aiki) tace "Don Allah Rahima kiyi hakuri ki yafe min." Rahima ta kalleta cike da tausayi "Wallahi ban rikeki da komi ba Aunty Allah ya yafe Mana m baki daya ya tsare gaba." Suka dan zauna na 'yan mintoci kafin ta mike tace "Zamu koma can sabida ba kowa sai yara, mu kwana lafiya." Zuwaira ta amsa "Nagode a sanyaye." Ya dawo rai a bace dalilin yaje gidan Hajiyarsa ya shaida mata lalle zai rabu da Zuwaira muddin ba zata daina hulda da kawaye irinsu Husaina ba, ya taraa Hajiyar bata jin dadi dole ya kyale duk bai ce komi ba but yai deciding washegari zai kaita asibiti don ta samu proper care, ya dawo gida a fusace. Ya shige bedroom dinsa bai ga Zuwairan ba, ya gyada kai ai yasan ba zata dumfareshi ba yanzun tunda bata da gaskiya. Zuciyarsa ta rinka kuna, ya shiga yai wanka ya fito abin na cinsa a rai kiranta yayi ta waya. Kafin ta iso ya Kai ya komo cikin bedroom dinsa ita kuma tana can cikin fargabar masifar da zai mata, ashe Zuwaira ana tsoron manya, ko can wargi wuri yassamu. Ta sallama ta shiga tayi kamar ba zata zauna ba ta canza shawara ta dofane a gefen bedroom chair, yai kai ya dawo yai mata tsaye a gaba ba tareda yace uffan ba, ta rinka satar kallonsa da wutsiyar idon. ... Haseeb ya dan baya ya juya mata baya ya tambayeta "Zuwaira Ina son baki zabi wanda in kin riga kinyi an yi an gama, ba yi hakuri balle na tuba. Shin kina son zama dani ko ah ah?? Cikinta ya bada kulululu kamar mai jin zawo, cikin makyarkyatar murya tace "Me ya kawo wannan maganar Dakta?" Cikin muryar data tsani yai mata magana yace "Amsa zaki bani ko nima tambayata kike? Ta Kara kidimewa "Ah ah wace ni, yi hakuri, wallahi Ina sonka Dakta, ban taba son kowa ba sai ke, ka yafe min. .. Ba wannan amsar nake son ji ba." Ta gyara zama "Ina son zama da Kai har muddin rayuwa." Ya numfasa ya zauna yace "Ba na jin zaki sami wannan daman ta bangarena as long as za kici gaba da mu'amala da kawayen banza to zan sauwake miki aur..... Bata bari ya karisa ba ta mike zumbur tasa hannu ta rufe bakinsa tana kuka "Don darajar iyayenka karka furta, don kaunarka da Annabin rahama ka yafe min... Ta durkushe a gabansa ta dafa gwiwoyinsa tana rasgar kuka tana masa bayanin yadda suka yi da Husaina bayan fitarsa .. Jin an ambaci Rahima ya mike da sauri "What! Iskancin naku ya wuce kuyi a waje har cikin gidana har ku nemi kassara min mata ta?" "Ka saurareni don Allah laifine na riga na aikata, nayi kuskure but nayi nadamar dukkan abubuwan da na aikata tuni, inata istigfari dare da Rana, na gane illar kawancena da su Husaina na kuma janye daga gareta data lura ne ta kara shige min amma wallahi bada yawuna tazo gidana ba." Ya numfasa "Ba dole tazo gidanki ba tunda tanada manufarta Wanda a da banyi niyyar fada miki ba sai kin gane da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66