Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

"Eh wajen Rahima zani mu karike shirye-shirye, Ya Haseeb yace in kai masa kiyasin abubuwan da suka rage ya bani yasan ya gama da hidimar." Hajiya tace "Gaskiyane, an gode masa Allah ya Kara budi, kaima ince ko kana yi masa adduar?" Yace "Duk rana ta Lillahi Hjy, tsakaninmu dashi adduar ce kadai abinyu don ko godiya nayi masa sai yaita fada." Tace karka fasa don nasan yana jin dadi, tashi ka tafi Kar dare yayi kace Ina gaisheta." Har ya mike ta tsayar dashi ta bude wata Jakarta ta fiddo sabbin kudi ta mika masa bandur na dubu biyu 'yan naira ishirin tace "Amshi ka Kai mata." Yasa hannu ya karba Yana tambayar "Ina kika sami sabbin kudi haka?". "Sai kaji inda suka fito? To kyautar Yayanku ne ya bani Ni Kuma na ajiye maka." Rabi'u yai tsaye shiru.." Kinga Hajiya ko kusa bai dace ba, ya zai miki alkhairi don ki amfana sai ki bani, gaskiya ba zaiji dadi ba." Ta hararesa "Kai zaka tafi ka fada masa ko wane, to idan ma baka karba ba Hayatu ya taho ya amsa tunda shi kullum cikin neman karin na cefane yake." Ya maidasu a aljihu yace "Ah ah Ina so Hajiya, Allah ya saka miki da aljanna madawamiyya." Ta amsa "Ameen Auta, hanzarta ka gani, sai ka dawo." Ya fito har zai hau babur dinsa sai shaawar takawa a kasa yazo masa, ya fasa ya bi titi yana takawa daidai, irin tafiyar yaro matashi Mai jini a jika. A cikin gidansu Rahima tuni ta dade da kimtsawa tana jiran Rabiun, a yau shigar wando da riga suka yi ita da Maryam 'yan Pakistan tsarabar Umrah ne da Baffansu ya kawo musu, duk kalarsu guda watau ruwan hoda da zanen kalar gwaiduwar kwai a jikinsa, banbancinsu kawai na Maryam yafi nata girma tunda ta fita girman jiki. Ita Rahima yarinyace gajera, baka mai dan jiki, ba kyakkyawa ba ce ba Kuma za a kirata mummuna ba, Maryam ta fita kyaun fuska nesa ba kusa ba, ita kuwa halittar jiki Ubangiji ya kyautatata mata. Tana da kyaun siga kwarai da gaske, kirar jikin matan Nan da ake Kira masu kirat kwalbar coca-cola. Duk da ita ba Mai kiba bace Allah yai mata halittar wasu guraye murde a wuyanta, layi-layi uku. So da dama akan kirata mai karuwar jiki kasancewar kowanne irin sutura ta saka su kanyi mata kyau suyi ras a jikinta tamkar dominta aka yi. Bayan wannan ba kowa ke yarda idan an fada masa shekarunta sun kai ashirin ba saboda jikin da fuskar basu nunawa. Sanin yadda sutura ke amsar jikinta suna fito Mata da shape yasa babu yadda za ayi mutum ya ganta ba tare da after dress ba, ga addini ya ratsata sosai domin Alh. Mamman ba daga baya ba wajen kyautata tarbiyyatr yayansa. Alhamdulillah su Rahima sun gogu da addini sun san hanyayoyin tafiyar da harkokinsu ta yau da kullum musamman tsarin addinin islama, tsakar gidansu kadai mutum zai shiga yaga kalar tufafin da ta saka saboda tsananin bin dokar Ubangiji. Cikin wannan shiga ta kamala ta fito ciiin natsuwa da kamun Kai ta tarbi maigida to be da harkarta yadda suka saba yiwa juna, suka gaisa a mutunce. Rabi'u ya isar Mata da sakon Hjajiya. Rahima ta amsa da "Kasan kuwa da kace Hajiya na gaisheni wani irin dadi kan rufe ni, ni shar kenan don wannan alama ce ta dace da sarakuwar kwarai." Ya gyara hularsa cikon jin dadi "In don Hajiya Kar kiji komi, ta yaba dake fiye da zatona, ke ko matan Ya Hayatu da suke kullum cikin bala'i bata kyamace su ba, ba abinda ke tsakaninsu sai kyautatawa." Rahima tace "Ta hutawa zuciyarta da masifa, daman har addua nike Kar Allah ya hadani da muguwar sarakuwa mai sa ido da kasa kunni a harkar matan danta don in kaji labarin masifar wata tsohuwar sai auren ya fita ran mutum gaba daya." Yayi dariya "Banyi tsammanin Hajiya zata kula matar Ya Hasseb ba balle na Ya Hayatu koda ace gida daya suke zaunre balle Allah ya raba zaman, Ya Hasseb na Galadanci, Ya Hayatu na Gwammaja ita tana Yakasai, bata zuwa gidan kowannansu balle ta gano abinda zai tayar Mata da hankali, sune dai duk sati suke Kai matansu su gaisheta, mu kuwa saboda kaunar da take miki ne yasa tace da ita zamu zauna." Tace "Lalle Dan lelen Hajiya, wai Rabiu daman kana da sauran turaren nan ka daina fesawa na daina jin kamshinsa." Ya kyalkyace da daruys "Kinsan na gaya miki nima fa Ya Haseeb ya bani, da naga ya kusa karewa ne na boye, ban san kina son shi ba dana kawo miki tuni amma zan adana miki sauran in kinzo in baki." Tace iye dan gatan Ya... Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin Yayan Rabiun ta kasa fadin sunansa duk da bata taba ganinsa ba. . Ya girgiza Kai "Ba zaki ma tabbatar da hakan ba Saida batun aurenmu ya taso, gaskiya Ya Haseeb ya cika danuwa kaunar zumunci da taimakon zumunta kamar yadda Allah yai mana horo muyi. Gaskiya kullum Ina jinjina masa, yana kaunata, yana ji dani matuka, nima bani da kamarsa Rahima." Ta nisa tace "To Allah ya barku tare Rabiu, Allah ya kaika matsayin da zaka kyautata masa kaima.' Ya amsa "Ameen, insha Allahu zanyi struggling, bari harkar bukin nan ya kare mu gama karatunmu ki gani da taimakon Allah zamu ba marada kunya." Tace "Ko shakka babu sai mun ba mutane mamaki.". "Kar ma dai ace 'Yan B.U.K da suke yada surutan banza, kinji maganganun da suke yi dana Kai musu IV, wasu har karyatawa suka yi." Taja tsaki "Kai kake kulasu, ai ni banda lokacinsu balle in saurari surutunsu.". Suna nan tsaye Umma da Maryam suka dawo unguwa, ya durkusa ya gaisheta ta wuce cikin gida, Maryam tana tsokanarsa "Ango kasha Mai, har an fara Shirin angoncine?" Yai dariya "Ban sanki da haka ba Aunty Maryam, Ina kuka fito da dare Nan?" Ta amsa "Gandun albasa, kasan can za a Kai amaryar taka rufi wajen Inna kanwar su Umma, Kuma don Allah ka daina kirana wata Aunty sai kaina ya rinka girma." Rahima tace "Girma ai ya hau kanki Auntyn Rabiu." Ta harareta "Kina korata ne kawai Kar in bata muku hira, Rabi'u Saida safe, ke Kuma zaki shigo ki sameni." Suka yi dariya suna kallon shigewarta gida. Rabi'u ya kurawa Tahima ido tun tana kaucewa har ta gaji tace "Wai lafiya?" Ya jingine da bango ya amsa "Kallon kyakkyawar fuskar amaryar Rabiu nike, wallahi Rahima tunda aka sa ranar aurenmu so da kaunarki dada tofo suke cikin zuciyata, so da yawa ina share awowi ina tunanin zamanmu a school, yanayin shakuwarmu da irin ji da juna da muke ashe soyayya ce ke shigarmu bamu fahimta ba. A kullum godewa Allah nike days kaddaro kasancewar hakan tsakaninmu, da Allah bai rubuto ke mata ta bace Rahima ya zanyi da Raina, Ina zan Kai wannan kololon son da ya cika min Zuciya har ya zamanto babu sauran ko masaka tsinke na kaunar wata, Rahima you're my life, don Allah ki so ni yadda nike sonki.". Ta saki ajiyar zuciya kafin tace "Ina sonka Rabiu, kaunar da nike maka ne ta haifar

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66