Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

goma, ya cika dan halas domin matukar girmamawar da yake masa yasa koda yai masa tayin auren diyarsa Zuwaira bai musa ba duk da Yana ji da ganin irin gurbatacciyar tarbiyyarta. Wajen hidimar auren Alhajin yaso daukar nauyin hidimar komi, Abdul Haseeb yaki yarda yace hakkinsa ne ya dau nauyin iyalinsa. Tunda Allah ya azurta shi yake dawainiyya da iyaye, 'yanuwa dana matarsa. Da Allah ya tashi ikonsa ya aikowa Mal Junaid hadarin motar da yai sanadin dakushewan kwakwalwa, bai iya tuna kowa da komi, hatta mata da 'ya'yan cikinsa. Asibitin Murtala aka kwantar dashi lokacin bai bude nasa ba. Duk da haka shi ya dau nauyin hidimar komi Wanda yasa matar uban kuka da hawayenta sharaf -sharaf tana roko gafarar Kaltume da danta, Wai Ashe tun kafin ta auri Mal Junaid tayi asirin farraqa shi da mahaifin gudun Wai kar tazo ta haihu ya nunawa Haseeb fifiko (Kunji wani rashin tunanin) to ta cimma burinta amma ta dawo tana dana sani wace a baya takan tsaya inji hausawa. Shin mu mata bama tunanin cewan duk yaron da aka tsana cikin gidansu Allah na iya daukaka shi ba? Shin bamu tunanin tunda bamu muka halicci mutum ba bama iya tsarawa wance ko wane abinda zasu zama a rayuwa? Allah ya kiyashemu aikata aikin dana sani, domin da mutane sun san hassada takin arziki ga Wanda ake yiwa da ba ka yi ba. Ta roki Kaltume da danta gafara sun yafe mata to shu mijinta data ha'inta yake kwance bai san inda yake ba fa, wanda ya rasu kwanaki uku da yin hatsarin, wata shari'ar sai gobe kiyama. Bayan rasuwar mahaifinsa ya dauki nauyin kulawa da dukkan hidimomin kanninsa da uwarsu. Bayan an raba musu gado ya budewa kowannansu shago a kasuwa saboda sun nuna sunfi son kasuwanci ba karatu ba balle aikin gwamnati, ko da aurensu yazo ma shi ke kan gaba wajen basu gudumuwarsa, uwarsu sai godiya take tunda ta dawo hanya ta tuba Allah ya sahale mata bakin cikinta kullum cikin istigfari, tsakaninta da Haseeb sai san barka. Mahaifinsu ya rasu da shekara guda tal Allsh yaiwa mijin mahaifiyarsa rasuwa, Haseeb yayi babban rashi yai kukan rashinsa, a dalili da duk fadin duniya su hudu kawai ke zaunar dashi su fada masa gaskiya, daga mahaifiyarsa sai shi sai Alh. Muhd sai kuwa abokin mahaifinsa daya saba dashi tun Yana zuwa daukar karatun allo, to ko da ya girma bai yada malaminsa ba Bayan ta gama takaba ne ya saya mata gida a Yakasai da yake daman gidan Mal. Sunusi na tarayya ne, shekara na zagayowa ya kaita ta sauke faralli, ta dawo ta bata jali tunda ta nace sai tayi sana'a. Dr Haseeb Junaid ya saki wata doguwar ajiyar zuciya, ko me yasa brain dinsa tariyo masa abinda ya wuce oho don wasu tuni ya fara mantawa sai fa yau. Tunaninsa ya koma Kan yadda ya rike kaninsa da suke ciki daya, ko girmamawar da suke masa ya isa yai hidimta musu cikin kowanne hali in ya ture batun shakuwar da yayi dasu kenan, su Hayatu na kaunarsa fiye da zatonsa musamman marigayi Rabi'u, ya tuna yanayin aurensa da ya taso a gurguje haka ma haihuwar ashe ba dadewa zaiyi a duniya ba A kullum ya tuna wasiyyarsa garesa inda ya bashi amanar Rahima da Abdul ransa kan dugunzuma ya bacu ya rasa me ke masa dadi a sararin duniya, to sai gashi wai shine da Shirin auren matarsa, babu irin tunanin da bai yi ba kan issue din but tabbas akwai Shirin da Allah cikin al'amarin, yes da akwau hukuncin Malikal Mulk don haka gara ya cire komi a zuciyarsa ya rungumi kaddara. Shigowarsa biyu kenan yana ganinsa cikin zurfin tunani don bai ko san ya shigon ba sai a na uku ya sallama ya fada falon, ya amsa yaga kamar Daktan na share hawaye tunda ya cire glass dinsa, yai kamar bai gani ba ya mika masa hannu suka gaisa."Ka dade kana jira ko afwaan." Cewar surukinsa. Ya manna dark glasses din a fuskarsa tukunna kafin yayi dan murmushi "Ai ban wani dade ba Alhaji". Ya mayar masa. Sanin miskilancinsa da rashin son yawan magana yasa Alhajin baiyi masa shishshigi bai tambayarsa sai abinda yaso fada masa da bakinsa, ganin halinda yake ciki na damuwa ma baisa ya nemi jin ko menene ba har suka yu 'yar hirarsu, zuwa can Alhajin yace "Wai Ina Zuwaira ne tazo ta zubar da yara daga zanje un dawo yau kwana biyu kenan bata ba labarinta?" Ya amsa "Tana can suna hidimar bukin wata kawarta ce, nasan ko zata waiwayesu sai an kare komi." Uban yaja tsaki "Watau ita dai ba zata daina halinta ba ko? Amma ban zargin kowa sai kaina Dana shagwabata, na manta cewan diya mace ce komin dadewa aure zata yi, nasan da wani take aure da tuni ta sako min it's, an taba mace na sanin ya kamata ba kamun Kai?" Haseeb yace "Allah ya kyauta a ci gaba da yi Mata adduar shiriya don tayi nisa Alhaji." Ya nisa "Wallahi tuni na fahimta wace bata damu da yayan cikinta ba ma? Wallahi ko jiya Saida muka yi maganar nan da uwarta, duk dai kuskuren ne, gata ko cuta? Shawarar dana yanke idan ka gaji da halinta ka sakota ko Allah zaisa tayi hankali karta gurbata maka tarbiyyar yaranka." Haseeb ya sunkuyar da Kai "Allah ya tsare, tsakanina da ita babu saki unless haka Allah ya rubuto Mana Ina Nan Ina Mata addua." Alhaji ya girgiza Kai "Duba Nan Dakta wallahi kasan rantsuwar musulmi kenan ko? Idan kaga ba zaka iya zama sa ita ba ka sauwake mata ka huta, nuna haifeta nasan halinta sarai don haka na baka izni, kar kaji nauyin komi Kar Kuma kayi tunanin yadda muke da Kai, tsakaninmu da ban hulda da matarka daban, ni ba zanso ace ka zauna da ita tana cutar ka kana hakuri sabida ni ba, nima na fara gajiya da halinta, uwarta ma tayi fushi da ita muddin Kuma ba zata zauna gidan aurenta tabi dokokin Ubangiji ba bani bata." Ya fara rarrashun tsohon yace "Allah ya huci zuciyarta insha Allah muna fatar ta natsu, may be idan taji zanyi aure." Alhajin yace "Alhamdulillah kamar ka shiga zuciyata, shawarar da nayi niyyar baka kenan ince ka Kara aure ka huta da wahala wannan yar banzan." "Don Allah Alhaji ka daina zaginta kayi hakuri, daman abinda na zo shaida maka kenan batun auren amma har ga Allah bani na nema ba, iyayene suka ga ya dace in auri matar marigayi Rabiu, gaskiya da ban amince ba amma daga baya sai Ina ganin watakila auren ya zama sanadiyyar shiriyyar Zuwaira domin yarinyar tasan addinita na yaba da hankalinta kwarai." "To Masha Allahu haka ake so, Allah yasa ayi damu, yaushe ne daurin auren?" Ya gyara zama "To ai kune masu neman auren Alhaji shine nazo sanar maka gobe idan Allah ya nuna mana sai ku tafi, nan dai Yakasai inda aka daura auren marigayin, daga nan zan nufi wajen Malam Nuhu ne in sanar dashi shima." Alhaji yace "Karka damu amma Ina fatar ba za a dau dogon lokaci ba." Haseeb yace "Nima hakan nike so." Daga nan ya nufi Sharifai gidan Malamin nasa ya shaida masa

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66