Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,223 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ni ban san abinda kake aikatawa ba na san dai kullum babu fashi za ka zo ka sayi abinci a gurina wannan shine abinda na sani." Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki hularsa yasa a sanyaye ya kama hanyar fita jikinsa duk a sa'bule, Shahida kamar ta fashe da dariya duk suka bi shi da kallo yana tafiya zugwi-zugwi kamar wanda k'wai ya tashewa a ciki. Bayan fitarsa dariyar da take boyewa ta sub'ce a fili ta ce."Karshen munafiki jin kunya." Saliha ta kalleta kamar za ta yi magana sai kuma ta ja bakinta tayi shuru tana girgiza kai. Ita kuwa Baba Asabe surutai take ita kad'ai akan maza masu irin wannan hali ko meye abin burgewa a gurin mazan dake ganin k'yashin ciyar da iyalinsu oho! **** Bayan kwana biyu ta fakaici idon Baba Asabe tasa hijibi ta fita, kai tsaye bakin titi ta nufa, idonta a gurin zamansa babu shi babu dalilinsa sai tarkacen kwaran-kwacamansa! ta jima a bakin titin tana kalle-kalle gabad'aya jikinta ya mutu saboda rashin ganinsa idanuwanta suka cika da ruwan hawaye. Wani yaro dake tafiya ta tsayar dashi tana tambayarsa. Yaron yayi mata wani irin kallo kafin ya ce."Ni ina ruwana da wani Baban- Baba ki je ki tambayi 'yan uwansa mahaukata" Yana gama maganarsa ya shige ya barta a gurin, taji kamar ta janyoshi ta gaura masa mari ta tsani a dangantashi da mahaukaci domin ita a ganinta ba taga haukan da yake ba tunda baya doke-doke. Wani kuttun! abu yazo ya tsaya mata a wuya ta juya domin komawa gida tamkar mara jini a jika haka take tafiya salo-salo! har ta isa gidan bata daina tunane-tunane a kansa ba. Kai tsaye uwar daki ta shige ta kwanta kan gado kai tasa a cikin hijabi ta fara zubda hawaye. Baba Asabe dake kokarin hura wuta ta ce."Saliha tunda ta dawo daga gantalin jeki ce tazo tayi wannan wanke-wanken. Saliha ta amsa da "To." Kai tsaye dakin ta shiga ta tsaya a kanta, "Ke! ki je ki kiyi wanke-wanke inji Baba." Tana jinta tayi mata banza, Tasa hannu tana kokarin fizge hijab din data rufe fuskarta dashi, Cikin zafin nama ta doke hannun! har sai da yayi 'kara. Saliha ta fita da hannu a sage! murya na rawa tace." Baba tana jina sai magana nake tayi min banza 'karshe ma hannuna ta buge duba sai zafi yake min." Tace."Rabu da ita zan shiga dakin na sameta." Saliha ta koma ta zauna da fadin." Wallahi Baba akwai ranar da zan sanya bulala na zane ' Yar iskar yarinyar nan na gaji da abinda take min." Tana kokarin fitowa daga kicin din tace."Idan kina ganin zaki iya da ita bisimillah ni babu ruwana to ka ji." 'Dakin ta shiga sai kawai taji shashshekar kukanta A sanyaye tace."Saboda na ce kizo kiyi wanke-wanke shine kike kuka?" Shuru tayi mata, Baba ta sake daga murya gami da maimaita maganarta. Ba tare data bude fuskarta ba tace." Me yasa kullum ni nake wanke-wanke a gidan nan idan gaskiya ne itama Saliha tayi saboda kinfi sonta shine kika bata aiki mai sauki ni kika bani aiki mai wahala ni wallahi na gaji haka kawai sanyi ya kamani idan gaskiya ne ki dauki 'yar aiki mana." Baba Asabe ta ji kanta yana juyawa da ita a gurin al'amarin ya bata mamaki mutu'ka. Ta ce."Shahida ni kike fad'awa wannan maganganun yaushe kika lalace?" Tana kuka tace."Ni kuskuranki nake so na nuna miki abinda kike ba daidai bane." Baba Asabe ta fashe da kuka da fadin." Mariya kin tafi kin bar baya da k'ura ni na haifeki a cikina amma baki tozartani kamar yanda 'yarki take tozartani ba, ni ba zan hofintar da zuriarki ba koda kuwa yarinyar nan zata dauko abin duka ta dake ni ba zan damu ba duniya ce ta ishi bagaruwa jima." Kuka take sosai wanda ya sanya Saliha ta shigo dakin hankalinta ya tashi sosai! sai rarrashinta take, A fusace! ta fita daga dakin, Ashe Kawu Musa ta kira a waya, ta sheda masa abinda yake faruwa, yace." Gashinan kan hanya. Baba Asabe na raku'be a jikin gado tana kuka da fyace hanci ita kuma Saliha tana tsaye a tsakiyar dakin sai Zaginta take da gore-gore! "Shegiya ai idan ba ki yi haka ba to ba ki cika 'yar gado ba, wannan mahaifin naki ai butulu ne masu ba'kin hali wai ace matar dake tallafarki ita kike wa rashin kunya ai yau zaki gane baki da wayo! Baba ta daga mata hannu da fadin." Saliha yi shuru da bakinki Ni tayi wa rashin kunya bake ba kada na kara jin maganarki. Gefe ta koma tana huci! Shi kuwa Kawu Musa yana zuwa ai bai yi wata-wata ba ya zari wayar redio ya fara lafta mata yana d'ura mata ashar! ,Fadi yake." Wallahi ba'kin cikinki ba zai kashe min uwa ba don ubanki yau sai kin bar gidan nan domin dama hakkin ri'ke ki ba a hannunmu yake ba. Da 'karfi yake maganar yana dukanta. Baba Asabe ta rike wayar tana janye shi daga gurin, "Ka daina dukanta kada kaji mata ciwo." Ita kuwa Fad'i take." Ki k'yale shi ya cigaba da dukana ya kasheni Kawu Musa idan baka kasheni ba wallahi baka cika dan halak ba." Maganar ta dinga yi masa kuwwa! a kunne! Ya nuna kirjinsa da hannu! " Ni kike fadawa haka? Tana kuka tace."Me yasa kake nuna min 'kiyayya! me yasa baka 'kaunata? me yasa kake fifita 'yarka a kaina? duk abinda kake min ina fahinta baka kaunata kullum idan kazo gidan nan cikin zuga Baba kake akan ta mayar dani gaban ubana, duk da ba naji sosai watarana na kan tsinkayi abinda kake fad'a akaina saboda haka nima bana sonka tunda baka kaunata." Kawu Musa jikinsa yayi sanyi, ya jefar da wayar redion ya kama hanya ya fita daga dakin kunyar duniya ta ishe shi. Ita kanta Salihan ganin yanda jikin babanta yayi sanyi yasa ta kasa daga kai ta kalleta simi-simi ta fita daga dakin. Tana kuka ta fara hada kayanta, Baba Asabe da sauri taje ta rufe sif din da mukkuli ta fita daga dakin.......Gabadaya haka suka kwana suka wuni cikin bacin rai mai tsanani, kuma tun daga ranar Baba Asabe take takatsantsan! da yarinyar bata tilasta mata kan cewa dole sai tayi mata aiki, Ita da kanta take tashi tayi abinda ba'a rasa ba amma ta daina aikin ruwa saboda tana gudun sanyi ya kamata, dama tayi wannan boran ne don ta samu sassaucin aikin ruwan da ake sanyata kullum ta Allah.*MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Fejin na yau na ku ne 'kannena biyu🥰* _Jamila Jamy 'Yar kankia_ Tare da: _Ummu-Hanifa_ Kuna da matsayi mai girma a gurina💯 *11&12* *WAIWAYE* Shekarun baya da suka wuce Baba Asabe da mijinta Malam Almu sunyi zama na mutunta juna gami da girmama juna, haihuwarsu biyu mace da namiji Musa shine babba tsakaninsa da 'yar uwarsa Mariya akwai tazara amma ba mai tsayi ba, A lokacin da Baba Asabe ta auri Malam Almu ya tsufa sosai bai ta'ba haihuwa ba har ya fitar da rai sai gashi cikin ikon Allah yana auranta Allah ya azurtashi da zuria, yayi farin ciki sosai ya dauki son duniya ya dorawa

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});