Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidanshi sai godiyar Allah domin da k'yar! yake bayar da kudin awo watarana matar gidan itace take cefane da yake tana awarar siyarwa shiyasa suke raba daidai. Da yawa mutane suna mamakin yanda yake sanya manyan sutturu da bajinta a waje amma 'ya'yanshi suna yawo babu sutturar arziki babu makaranta mai kyau, uwa uba kuma matarsa na sana'ar siyar da awara wannan dalilin ya sanya wasu ke zaginsa suna ganin arzikinsa ya tashi a banza tunda ya kasa sauke nauyin iyalinsa sai dai ya fita yana neman suna a gurin jama'ar gari. A zahiri sana'ar sa wacce kowa ya san shi ida ita sayar da takalma a cikin kasuwar wambai shago guda ne dashi yake bada sarin takalma na roba dana fata amma irin wanda akeyi a cikin kasuwar bayan wannan sana'ar tashi akwai wata wacce ya jima yanayi a 'boye kuma itace take kawo masa ma'kudan kudin da yake facaka dasu. Yau zaka gan shi da sabuwar mota amma idan aka kwana biyu sai gan shi cikin a daidaita sahu ko kuma a kafa yana tafiya idan ka tambayeshi sai kawai yace motarsa tana gareji ta samu matsala 'karya kamar kudin guzuri a gurinsa, wannan dalilin ya sanya jama'a suke d'aukarsa a matsayin mai rariyar hannu ko kuma d'an bariki har yanzu babu wanda ya hasaso irin sana'ar dake sanya abubuwan hannunsa suke salwancewa. Ko a cikin a daidaita sahun ma sai jan 'yar tashi yake da wasa yana tsokanarta wai lallai sai ta fada masa sunan saurayinta. Ita dai Shahida murmushi kawai take tana mamakin halayyar mahaifin nata, kwata-kwata baya jin nauyi da kunya idan yana wasu abubuwan. Da yake yamma tayi ya sanya titin ya cunkushe da ababan hawa bayan jama'ar dake kai kawo a gurin. Duk wanda yake cikin garin *KANO* ya san cewa titin *JAKARA* yana bukatar gyara daga mahukunta, amma anyi shakulatun 'bangaro dashi duk da irin gudumawar da matasan unguwar ke bayarwa a lokocin za'be amma ko wane d'an takara daga zarar ya samu abunda yake so sai ya manta da wad'anda suka sha masa wahala. mai adaidaita sahun yace."Alhaji ko zaku sauka anan ne yamma tayi gashi gowslow nan yaki sauki. Yace."Aa akwai sauran tafiya kayi hakuri ka shiga damu ciki, Yace."To shikkenan amma zaka 'kara min wani abu." Yace."Babu damuwa." Da karfi! tace."Subahanallahi." hankalinsu ya dawo kanta kokarin fita take daga babur din ya rike hannunta yana tambayarta, ta nu na masa shi wanda yake can tsallaken titi wani mai babur ya kusa buge shi jama'a har sun taru a kansa. Hawaye ta share tana fadin." Allah ya kiyaye da tuni mai babur ya buge shi Allah sarki Baban- baba." Yace."Ke wai baki da hankali ne kike magana ke kadai. Mai babur din yace."Alhaji baka lura bane ai mummanan al'amari ne ya kusa faruwa akan wancan mahaukacin dake tsallaken titin can.'' Yaja tsaki da fadin." Ni ai ban lura wallahi ba kaji yanda hankalina ya tashi ba ke ina ruwanki da mahaukaci Shahida." Yana kallonta yake maganar. Hawaye ta share da fadin." Haka kawai nake tausayinsa." Tsuke fuska yayi da fadin." Malama shige mota mu tafi bana son shashancin banza a garin tausayi ake cutarku wancan mutumin da ka gani ba mahaukaci bane akwai manufarsa. Ta share hawaye da fadin." Eh Baba nima bana masa daukar mahaukaci tunda wani sa'in duk abu na masu hankali yana aikatawa rashin galihun da yake cike ne yake damuna, da za'a samu wasu masu imani da tausayi su taimaka masa da abin yi Abbah ka duba fa kaga kayan jikinsa duk daud'a duk sun yage fuskarsa bakikirin takalmin kafarsa ya sud'e ya tsinke kullum karkashin mota yake kwana rana zafi iska ruwa babu wanda ya damu dashi da ci da shan sa." Yace."Shahida Irin wad'annan mutanan da kike gani basu da gaskiya shiyasa Allah yake mayar dasu haka watakila akwai wani mugun abun da ya tafka wanda yasa Allah ya nuna masa kuskuransa saboda haka idan za ki yi tausayi da imani ki tausayawa 'kananun yara ko kuma marayu ko nakasassu irinki amma ba irin wad'annan mutanan ba." Direba yace."Gaskiya ne Alhaji nima na jima ina mamakin mutumin nan da yake ina yawan shigowa unguwar nan ina ganinsa sai nayi ta mamakin yanda akayi rayuwarsa ta lalace haka koda yake duk mutumin da bashi da gaskiya yakan 'kare rayuwarsa a firgice ba tare da ya san ina ya dosa ba." Hawaye ta share tana jin zafin magangansu tace."Abbah ku dai kuyi masa Addua dashi da masu lalura irin tashi watakila kuma babu d'aya daga cikin abunda kuke zargi mybe jarabtace daga Ubangiji." Murmushi yayi ya dauko tafkekiyar wayarsa yana dubawa yace." Shahida irin halinku daya da mahaifiyarki Allah ya gafarta mata." Ta amsa da ameen tana goge fuskarta. Suna zaune a tsakar gida ita da Saliha suna gyaran kayan miya suka shiga gidan. Koda ta amsa sallamarsu sai kawai ta mayar da kanta kasa ta cigaba da abinda takeyi tai bala'in shan kunu! Da yake ya iya Siyasa sai ya cire takalmansa cikin ladabi da 'yar dariya a tare dashi yace."Baba sannu da aiki." Ciki-ciki ta amsa ita kuwa Saliha ko kallonsa ba tayi ba ballanatanta ta gaisheshi hakan ya 'bata mata rai sosai sai itama ta kudiri aniya a zuciyarta kan cewa duk sanda babanta yazo gidan ta daina gaishe shi. Da fara'a a tare dashi yace."Ai dawowata kenan na samu yarinyar nan a gidan shine take sheda min abunda ya faru har kika kore ta daga gidanki haba Baba ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar." Hannu ta d'aga masa da fadin." Dakata! Jamilu kazo ne kayi min dadin baki ko kuma kud'ina kazo ka biya ni bana son neman gidin zama ko kuma dama can hakkin rike yarinyar nan a hannuna yake?" Maganar ta 'bata masa rai amma sai ya basar yace."Haba Baba ki kwantar da hankalinki muyi magana ta fahinta mana ake rasa mutum ma ballanatana kudi." Tsaki! taja tana cizge alayyahun dake gabanta ta ce." Mutuwa dole ce amma da gangan yarinyar nan tayi min wasarere! da kudi har 'barawo ya sace saboda haka ka tashi ka bani guri bana bukatar tsari da dadin baki mutukar ba biya na kudi za kayi ba." Ya girgiza kai har ila yau da murmushi a fuskarsa yace."Wai shin ma nawa ne kudin naki.?" Ta kalleshi she'ke'ke! kafin tace."Kaji fa! kamar gaske har wani tambaya kake kamar wanda zai iya biya." Dariya yasa baka ta'ba ganin 'bacin ransa saboda ya iya siyasa yace."Ko ba zan iya biya ba ai yana da kyau na sani." Ta'be baki tayi da fadin." Babu amfanin na fad'a maka tunda ba iya biya za kayi ba." Ya gyad'a kanshi yana kallonta minti biyu ya giciye yana gyara babbar rigarsa ta zuba masa ido tana kallonsa ya zaro yan dubu-dubu sabbi kar dasu har wasu na zubewa a kasan gurin. Cike da mamaki take kallonsa yana irgawa cas ya cake mata dubu hamsin a gabanta ya gyara zaman babbar rigarsa da fadin." Gashinan duk da na san ban isa na biya kudin hidimar da akayi min ba ayi hakuri da ni da hali na na san anyi min kokari." Kunya ce ta rufe ta sai ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai ba har ya gama maganarsa

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});