Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nutse ya zauna kan kujera yana kallon Shukuran dake tsaya da alamun rashin gaskiya a tattare da ita. "Kin yi sallah?" tambayar da ya yi mata kenan. Sai ta hau diri-diri kafin ta ce." Daddy bani da tsarki ai." Shuru yayi be ce komai ba, da shagwaba ta ce" Daddy don Allah ka bari na je gidan bikin nan, kamar hakan bai dace ba tunda Aunty Samira 'kanwar mommy ce kuma kai ma 'kanwarka ce ka taimaka Daddy don Allah." ta 'karasa maganar tana karyar da kai. Shuru yayi bai ce uffan ba, ta kalleta da fadin." Hajiya kisa baki don Allah" Kallonsa tayi da fad'in.'' Alhaji Habu ina nema mata alfarma." Yanda ta fad'i maganar cikin 'kaskantar da kai ya bashi dariya! Ya ce" Na amince amma ba don halinta ba, kuma ban yarda da kwana ba, aje a dawo." Tsalle ta buga da fad'in." Daddy na gode Allah ya 'kara girma." Duk abinda suke tana takure a gurin tana kallonsu, sai dai ba sosai take jin abinda suke tattaunawa ba. ita gabad'aya zaman sa a gurin shi ya 'kara firgitata! ta kasa gane wane yanayi take ciki, haka kawai mutumin yake cika mata ido. Hajiya ta nuna ta da yatsa da fadin." Yallabai wannan ita ce amaryar Sule fa, wallahi da farko na dauka irin masu zuwa neman taimako ne, sai da ta gabatar min da kanta tukkuna na tuna amma ga dukkan alamu tana da matsalar rashin ji kurma ce" Kallon da yake mata ne yasa duk ta tsargu! ta kasa 'kwakwkwaran motsi. A hankali ya kalli Hajiyan da fadin." Ya sunanta?" "Shahida sunanta, ai na ce na samu abokiyar hira duk da cewa ba ta ji sosai hakan bai zai hana ta d'ebe min kewa ba." Ya ce." 'Kwarai kuwa nima wannan ne dalilin da yasa na bashi guri a gidan nan, na ce ya zauna saboda ki samu walwala. Ta ce." Maganar auranka dai shuru Alhaji kullum sai kace kana kan hanya.'' Shukura da sauri ta ce." Hajiya ai daddy ba sabon aure zai yi ba, Mommyna zai dawo da ita.'' Wani irin kallo yayi mata kafin ya mi'ke ba tare da ya ce musu komai ba ya haura samansa. Hajiya ta ce." Shukura mahaifinki ya tsani ayi masa maganar Fatima mutukar kina so ki ga b'acin ransa to ki ambaci sunanta, wannan k'iyayyar tayi yawa." A sanyaye ta ce."Wai Hajiya me ya faru ne? na lura daddy ya tsane ta sosai kuma yana da ri'ko! kome tayi masa ai sai yayi hakuri tunda na shiga tsakani, sannan da dangantaka a tsakaninsu." Ta ce." Shukura labarin yana da tsayi sosai! amma babu shakka Fatima ta yi abubuwa da yawa marasa kyau a can baya! wanda ba su da amfani, saboda haka tayar da al'amarin yana nufin 'bacin ran mu gabad'aya. A sanyaye ta ce." Shikkenan to Allah ya kyauta." ta amsa da "Ameen ya rabbi." Shahida na zaune tana satar kallonsu, yanayin fuskokinsu da yanda suke magana a hankali cikin rashin walwala yasa ta gane cewa lallai abinda suke tattaunawa ba mai dad'i bane. **** To kwana d'aya biyu har ta saba! kullum idan ta tashi za ta gyara gurinta, kafin tayi wanka ta shirya jikinta tsaf! sai ta karya kummalo ta nufi cikin gidan a can take yini tare da hajiya, idan lokacin shiga kicin yayi ta je ta taimakawa masu aiki, sosai Hajiya take jin dadin zama da ita, wannan dalilin yasa ta umarce ta cewa duk abinda take bukata kada tayi 'kwauron baki ta tambaye ta, anan take cin abinci rana da dare. sai tayi sallar isha'i take tafiya gurinta, sai dai abinda yake damunta yanda Shukura ke 'kyamarta! hantara! kyara! wataran harda zagi! kuma kullum ita ke zuwa ta gyara mata d'akinta ta wanke mata bandaki da sauransu, amma bata ta'ba godiya ba, wannan abu yana damunta sosai! Kasancewar ta samu caji a wayarta yasa ta tura masa text na gaisuwa da kalaman soyayya! tana jiran amsarsa, shuru bai bata amsa ba, jikinta ya 'kara yin sanyi gabad'aya bata da wani kuzari, yau kwanansa tara da tafiya babu wata magana da ta ta'ba shiga tsakaninsu ta hanyar sadarwa. Cikin kwana goma da tayi a gidan ta sauya fatarta tayi luff! tayi kyau daidai gwargwado kuruciyarta ta sake bayyana, Shahida bata da wani kyau na ku zo a gani, sai dai tana da dirin jiki mai kyau akwai cikar kirji tare da kyakykyawan k'ugu ko'ina a jikinta a cike yake bata da rama kuma tana tsakatsaki ita ba doguwa ba sannan ba gajeriya ba, tana da yawan gashi cikkake irin na asalin hausawa, bakikirin! haka take d'aure shi da ribbon ya taru sosai a kanta, tana yanayi da Nafisa Abdullahi jarumar finafinan hausa, sai dai har taso tafi Nafisa cika da kwarjini. ba ta da makusa bayan matsalar kunne (rashin ji) da Allah ya hallice ta. Yau kwana goma sha biyu kenan da tafiyarsa, tana lissafi saura kwana biyu ya dawo,sai murna da farin ciki take, domin ita kad'ai ta san irin halin da take shiga a duk lokacin da za tayi bacci! tsoro take ji ita kad'ai a wannan gurin, koda wani abu ba zai shiga tsakaninsu ba, idan tana jin motsinsa a gidan rahama ne. Shuru lokacin da ta shiga falon, sai sallama take babu wanda ya amsa, cikin zuciyarta take tunanin ko Hajiyan na d'aki bata fito ba, sai ta yanke shawarar shiga dakin. a lokacin ne yake saukowa daga sama cikin pyjamas (kayan bacci) irin masu falmaran amma babu ta ciki kirjinsa wanda ya ke cike da kwantaccen gashi 'baki duk a waje! Da saurin gaske ta kawar da kanta! tana jin wani irin fad'uwar gaba, 'kafafunta ne suka shiga kyarma! ta zube a k'asa tun kafin ya 'karaso gurin da take. "Alhaji Ina kwana?" tafad'a cikin sar'kewar murya. Bai amsa ba da hannu yayi mata alamar ta tashi. Tashi tayi amma ta gagara kallonsa, gabad'aya ma tsigar jikinta ce take tashi ganinsa haka. Gurin cin abinci ya nufa ya zauna domin karya kummalo. Ita kuma jiki a mace ta kama hanyar fita, ya tsirawa bayanta ido, duk da cewa a cikin hijabi take hakan bai hana shi ganin 'kirar jikinta ba, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! yana danne abinda ke taso masa. muryarsa ya bud'e sosai kafin ya kira sunanta. Juyowa tayi tana kallonsa, yayi mata alama da hannu ta je gurinsa. Gabanta ya tsananta da fad'uwa, shin idan ta je me za tayi masa? abinda take rayawa kenan a zuciyarta. amma tuno gargadin mijinta yasa a sanyaye ta nufi gurin nasa kamar yanda ya umarce ta. *Littafi na daya yana daf da k'arewa ku yi hanzari ku biya kudin littafin na biyu domin cigaba da karanta labarin.πŸ₯° Yanzu ne fa za a fara wasan. ina fata za ku yi mini kara gurin sayan littafi na biyu. Allah ya yassare.* *Normal group posting sau daya a rana #500... Vip group posting sau biyu a rana 1k. 0502382124...Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini mgn ta WhatsApp 07084653262.. Mutan nan Nijar dala dari Vip jakka daya katin airtel za ku tura mini ta WhatsApp* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALEπŸ’* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *ABACHE POULTRY FARM*πŸ“πŸ“πŸ“ *Shahararran kamfanin da

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});