Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

had'asu ba to amma ya yi imani da cewa ita d'in mai 'kaunarsa ce, Abinda tayi a yanzu shine ya tabbatar masa da zarginsa. A nutse yace."Ki yi hakuri kinji ko." Shiru bata d'ago kanta ba, jim yayi yana nazari wani 'karamin icce ya d'auka ya zungureta dashi. a firgice ta d'ago kanta idanuwanta sunyi fululu fuskarta har ta kumbura! Tsigar jikinshi ce tashi ya mayar da kanshi kasa yana wasa da icce hannunsa. Tsaye ta mike tana karkad'e jikinta gabanta sai dukan uku-uku! yake! Ta kalli gabas ta kalli yamma kudu arewa sai kawai ta d'ora hannu a ka ta kurma ihu! tare da fadin." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una! Ya mike tsaye da sauri yana kallonta so yake yayi magana amma jama'ar da suka fara taruwa a gurin suka hana shi idanuwanshi kawai ya zuba mata. Haladu wanda ya kasance ma'kocinsu ya 'karaso gurin da fadin."Ke Shahida menene? me kike a gurin wannan mahaukacin."? Cikin kuka tace." Zuwa nayi na kori yaran da suke tsokanarsa shine suka sace kudin kuma Baba Asabe ce ta aike ni bakin asibiti na saro mata man gyada." Yace."In ban da shashanci irin naki da hauka yaushe zaki iya watsa yaran da suka dad'e suna tsokanar wannan shashashan mutumin nan wanda bai san ciwon kansa ba, shashahar banza kawai gashinan garin hauka kin janyowa mutane asara to kada kiji da wai sai na fad'a mata yanda akayi komai ya faru." Tana kuka take fadin." Don Allah kayi hakuri kada ka fada mata ." Tsaki yaja ya gyara zaman daddumar dake kafad'arsa ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Ganin haka yasa mutanan dake gurin suka watse. Komawa yayi ya zauna tare da rungume hannuwansa a kirji, Ta kalleshi da fadin." Baban- Baba Don Allah baka ga wanda ya daukar min kudi ba?" Girgiza kansa yayi alamun bai gani ba, hawaye suka sake zubo mata tace."To ko zaka duba min cikin takarcen kayanka ko Allah zai sanya suna ciki." Beyi mata jayayya ba ya fara dudduba tsummokaran dake gurin yana musu filla-filla babu komai sai tarin ledoji na pure water da sauran robobin lemo da yake tarawa. Ba tare da tsoron komai ba tazo ta tsuguna daf dashi tana sake hargitsa ledojin babban burinta ace taga ledar dake d'aure da kudin Baba Asabe. Sosai yake mamakin rashin tsoron yarinyar da yawa yara duk fitsararsu daga nesa suke tsayawa su tsokane shi, basa iya kusantar gurin da yake duk da cewa baya doke-doke amma hatta da manya basa iya zuwa inda yake amma abun mamaki ita ba taji tsoronshi ba tazo ta tsuguna kusa dashi duk da ta san cewa shi din ba mai cikakken hankali bane. Gabadaya jikinsa ya mutu wata iriyar kasala da kaunar yarinyar suka sanya shi kasa dauke idonsa daga kanta. Ta kalleshi da jajayen idanuwanta da karfi tace."Babu kudin sun sace ban san wane irin hukunci Baba Asabe za tayi min ba." Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda alamun yana bata hakuri. Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya. Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa! _NA YI AMFANI DA SALO BIYU GURIN RUBUTA WANNAN LABARI, INA FATAN MASU KARATU ZA SU FAHIMTA_ *BINTA UMAR ABBALE* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi join don samun dama karanta littafin na d'aya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) Na *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO... _____ _Fatan Alheri ga marubuta Amanar Binta💯🥰_ *Hasinatu (Autar Manya)* *Sadiya Rimi* *Binta Garba Saleh* *Matar ya sayyadi* *Real Esha* *Jamy 'Yar kankia* *Fatima Sunasi Rabi'u* *Dr Ms Agadaz* *Ummu Mahir* *Jasmine* *Zee Kumurya* *Shamsiyya Manga* *Autar Marubuta* *Indo Aisha* *Maman Teddy* *Zahraty Takwara* *xayyishatu Humaira* *3&4* Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a. Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu. Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa. Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta. Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?" Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake kansa. Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?" Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi." Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai! Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru. Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga ne?" Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba. Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada mata. Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace." Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau." Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san kansa ba." Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina. Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali. Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});