Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar. Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani. Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta. Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take. **** "Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba. Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan." Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki." Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta." Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida. Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba. Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri. Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen" ***** _"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_ Wannan shine abinda Saliha ta rubuta. Tana hawaye take tura amsa kamar haka. _"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_ Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba. Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa. Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali. Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta. Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah. Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.'' Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari." Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da har zai farauce ki, to shikkenan misali a ce maganarki gaskiya ce, ni na amince ki bashi kanki a madadina domin bani da wata cikakkiyar lafiyar da zan kwanta dake, na fad'a miki wannan mutumin ya fi karfin komai a guri na, saboda haka na amince a duk lokacin da ya buk'aci wani abu a gurinki ciki kuwa harda kwanciya dake, to kada kiyi masa jayayya domin yin hakan na barazana da auranki, ki amince masa kai tsaye kuma ki sakar masa jiki sa'anan kiyi k'o'karin faranta masa, ki ji a ranki kamar kina tare dani, wannan shine abinda za kiyi ki faranta min rai. *WASA FARIN GIRKI!πŸ₯°* Ko ya zata kasance? ina fatan za ku biyo ni domin karanta cikakken labarin, don wannan sominta'bi ne, kada ku manta akwai labari a 'kasa jingim! don haka masoya kada ayi 'kasa a gwiwa gurin biyan kudi domin jin yanda za ta kasance. Ni ce taku a koda yaushe *BINTA UMAR ABBALE* MARUBIYAR *1-NANA KADIJA* *2-YARO DA KUDI* *3-GIMBIYA BALARABA* *4-BABBAN YARO* *5-MASHAHURI* *6-LADIDI KWADAGA* *7-RUWAN DARE* *8-SADAUKI OMAR* *9-NIDA YAYA SADAM* *10-YAR BANGAR SIYASA* *11-DA WATA A KASA* *12-MADADI* *13-KWARYA TABI KWARYA* *14- GA IRINTA NAN* *15-MATSALARMU A YAU* *16-GOJE* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALEπŸ’* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *ABACHE POULTRY FARM*πŸ“πŸ“πŸ“ *Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.* *08069459550* *08039451082* 57&58 A tsorace take kallonsa a lokacin da yake 'kokarin zuwa gurin da take tsaye. Cikin wata irin tafiyar isa da ta'kama! ya tsaya daf da ita hucin numfashinsa na dukan fuskarta. hannu ya sa cikin aljihu. kafin yasa d'aya hannun ya rungumota jikinsa! rikon tsauri! yayi mata da hannu d'aya yana sumbatar gefen fuskarta. Wani irin hauka da buge-buge! ta shiga yi duk domin ta 'kwaci kanta daga hannunsa! ta samu gefen kafad'arsa ta gartsa masa cizo! wanda yayi sanadiyar sakinta, sai ta matsa gefe tana mayar da numfashi tare da wani irin kuka! mai ciwo! jikinta na kyarma! tsigar jikinta gabad'aya ta tashi. Kallonta yake da idanuwan da suka sanja launi! ta zabga masa muguwar harara! cikin tsananin jin ciwo da takaicin abinda yayi mata ta ce." Wallahi ka ji kunya! ashe dama baka da kirki ko?" Ya tsira mata rikitattun idanuwansa dake cike da tsantsar fitina ta shekara da shekaru! gabad'aya yarinyar ta gama tayar masa da hankali. Ta je ta rarumi gwangwanin turare a kan madubi ta jefa masa tana kuka ta ce." Sai Allah ya saka min abinda kayi min, kuma sai na fad'awa mijina." Ya 'bata rai! kafin ya bud'e muryarsa sosai ya ce" Kafin ki fad'a masa ni zan riga ki, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka ki fice min daga daki" Da k'arfi ya k'arasa maganar yana nuna mata hanyar fita da hannunsa. Ta sake d'aukar wani

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});