Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gwangwanin ta je fa masa wanda ya sauka a goshinsa, tana zubar da hawaye ta ce" Ban yafe ba daka ta'ba ni." yanda ta ke rawar jiki da yanda take kuka har cikin ranta ya tabbatar masa da cewa ta ji ciwon abinda ya yi. Sai ya mi'ke da azama ya nufe ta, ta zabura! a guje tayi hanyar fita, garin kici-kicin bud'e kofar ta zame ta fad'i a gurin, rintse idonta tayi ganinsa a tsaye a kanta ya yi mata rumfa. Ta rufe fuskarta da tafin hannunta "Don Allah kada ke ta min haddi, ka dubi darajar aure kada ka sake ta'ba ni." tafad'a jikinta na wani irin rawa. Hannu biyu yasa ya d'ago ta ta mi'ke tsaye, ya tsirawa fuskarta ido, hawaye sai tsare suke a saman fuskar, harshe yasa yana tsotse hawayen, gabad'aya k'afafunta suka kasa d'aukarta, sai k'o'karin zubewa take a gurin, yana tallafota. Yanzu ma haukan ta sake yi masa tasa dukkanin 'karfinta ta dinga dukansa a k'irji har sai da ya saketa, ta zube a gurin tana wani irin kuka mai cin rai! Tayi tur! da wannan rayuwa da take. tayi Allah wadai da ita. Ya tsuguna gabanta tare da k'okarin daidaita yanayinsa ya ce." Ko na kwanta dake mijinki babu abinda zai ce, saboda iko na ne, ke kuma baki da wata daraja! sannan na ji kina maganar aure! to ki daina daukar wannan auran naku da mutunci, domin duk ina da labarin yanda akayi shi, da kud'i na aka fansheki a gurin mahaifinki, saboda haka ina da iko da damar nayi duk abinda nakeso dake. Wani irin kallo take masa bakinta ya mutu murus! gabad'aya ta rasa a wane mizani za ta ajiye maganarsa. Ganin tayi sanyi ta gagara magantuwa yasa ya mi'ke tsaye, anan ne ta girmansa ya bayyana sosai! ya tashi, saboda yanayin kayan dake jikinsa masu kwanciya a jiki ne, wannan dalilin yasa girmansa fitowa, gaskiya ta tsorata! da yanayin, sai tayi gaggawar d'auke idonta tana kiran sunan Allah a zuciyarta, tunda ta ke, bata ta'ba ganin girman namiji irin haka ba sai akan wannan mutumin da yake kokarin keta mata alfarma. "Tashi ki fitar min a daki.'' Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta tashi har dankwalin kanta yana fad'uwa, anan ne ya ga tarin sumar kanta, ya sake shiga rud'ani, domin a rayuwarsa yana masifar son mace mai gashi, kawar da kansa yayi daga barin kallonta ya nuna mata hanyar fita da fadin." Yanzu nan zan kira mijin ki na sheda masa irin zagi da cin mutumcin da ki kayi min." Ya fadi maganar ne yanda za taji. Muguwar harara! ta buga masa kafin ta ja dogon tsaki! ta fita ta barshi a tsaye da kwantaccen murmushi a fuskarsa. Jiki a mace ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, gabad'aya jikinsa ya rikirkice sha'awa ta shekara da shekaru ta taso masa, bai san ya zai yi ba a halin yanzu. Yinin kuka da damuwa tayi, duk ta tsargi kanta da kanta, sa'i da lokaci idan ta tuna al'amarin sai gabanta yayi ta fad'uwa, adduar kariya kawai ta lazumta domin ita kad'ai ce magani a gare ta. Wajejan goma da rabi na dare ya turo mata text cewa ta kiyayi 'bacin ransa idan ya dawo domin ya ji labarin abinda tayi wa maigidansa saboda haka tayi gaggawar zuwa ta bashi hakuri. Amsa ta bashi kamar haka; "Da kasan abinda ya faru a tsakanina dashi ba zaka fad'i haka ba maigidanka mutumin banza ne don haka ni ba zan bashi hakuri ba. Sai ya bata amsa da cewa; Ashe kuwa auranki yana gargada domin kuwa mutukar ba ki je kin bashi hakuri ba wallahi zan iya sakin ki." Jikinta yayi sanyi jin abinda ya ce. sai tayi shuru tana tunanin yanda za ayi ta je ta bashi hakuri bayan tasan shine mara gaskiya. Ya sake turo mata da wani sakon, cewa; "Lallai kada ta tsallake umarninsa a daran nan taje ta bashi hakuri. Agogo ta duba sha d'aya saura na dare, ya za'ayi ta iya fita a wannan daran. gaskiya sai dai da safe, shima don ba yanda za tayi ne. Yau cikin hijabi har 'kasa ta shirya jikinta, babu walwala a tare da ita nufi cikin gidan. Zaune a falo ta same shi kan wani keke irin na motsa jiki, yana sanye da singileti da wando iya gwiwa, cigaba yayi da motsa jikinsa ba tare da ya kalle ta ba. Tsugunawa tayi a gefansa da fadin." Ina kwana?" shuru yayi be amsa ba ya cigaba da abinda yake gabansa. "Don Allah kayi hakuri." Tafada cikin yanayin maganarta, gabadaya duk tayi sanyi ta fara nadamar wannan auran. Ya cire 'karamin towel din dake rataye a wuyansa. fuskarsa ya goge! kawai ya jefa mata towel din a jiki. Sai ta bi towel din da kallo tana mamakin abinda yayi. kallonsa tayi. suka had'a ido sai tayi saurin kawar da fuskarta. Ya tashi daga kan keken ya nufi gurin cin abinci ba tare da ya ce mata komai ba. Ganin haka sai ta ajiye masa towel din ta kama hanyar fita tana neman tsari dashi. Sunanta ya kira tana daf da fita. Ta juyo tana kallonsa fuskarta sam! babu fara'a. "Zo ki zuba min abinci" hankalinsa na kan wayarsa yayi maganar. Girgiza kanta tayi ta koma da baya domin bin umarinsa. Ta had'a masa komai ta ajiye a gabansa kafin ta ce." Zan iya tafiya?" Kansa ya girgiza alamun A'a. sai ta tsaya tana kallonsa da jiran umarni na gaba. Sai da ya mula tukkuna ya ajiye wayar hannunsa kafin ya kalle ta a sakarce ya ce." Kinyi kyau cikin hijabi." Tayi shuru dai ba tace uffan ba. Gabadaya girmansa ya zube a idonta. Ya ce'' Na ga kina ta wani rufe-rufe me ki ke b'oyewa ne?" Ta ce." Babu komai." Girgiza kansa yayi ya ce."Ban yarda ba gaskiya, ba zaki fita ba sai kin cire wannan hijabin na duba ki." Taji wani irin fad'uwar gaba! ta kalle shi idonsa k'ur! a kanta kamar tsohon maye! Ta ce" Shigowata ban kai minti goma ba kuma iyakata nan falon me kake tunanin zan d'auka?" Ya daga kafad'a da fad'in." Ni dai ban yarda ba saboda haka ki cire idan kuma kinyi gardama to zan cire miki da kaina. Cikin rawar murya ta ce." Kai fa uba ne, ka haifa kasan mai kyau da mara kyau, yanzu idan akayi wa 'yarka abinda kake min za ka ji dad'i?" "Ba zan ji dadi ba gaskiya" Serious ya fadi maganar. Ta ce." To mai yasa ka keyi min haka?" Shuru yayi be ce komai ba illah kofin shayi da ya d'auka yana kur'ba! Ta ce" Zan iya tafiya?" Ya ta'be baki "A'a nifa har yanzu ban yarda dake ba, mutukar zaki shigo nan to ki dinga sa mayafi wannan hijabin akwai munafurci a ciki. Cike da takaici da mugun haushinsa ta ce." Ba hali na bane sata, kuma ba zan fara anan ba, don haka ka daina d'aukar alhakina. Bagarar da maganar yayi ya cigaba da kur'bar shayinsa. Yanda ya ke wulakantata hakan yana yi mata ciwo mutu'ka! sai kawai ta kama hanyar fita a karo na biyu ya dakatar da ita da fadin." Har yanzu ban baki izinin fita ba

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});