Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya samu kudi masu yawa, burinsa a yanzu bai wuce siyan babur ba, zai sayi vespa d'an 'kasa irin wanda manya alhazawa suke hawa a duk lokacin da ba suyi ra'ayin hawa mota ba. Tura kofar dakin tayi sai yayi saurin boye kudin a bayansa. Tayi sallama tare da tsayawa 'kerere a gabanshi, yace."Kefa dadina dake rashin ladabi meye haka kin shigo ba tare dana nemeki ba kin tsaya min 'kerere a ka." Ta gyara daurin zaninta da fadin." Ka san kwanan zance ai bana so muyi hayaniya da kai a gaban yara saboda haka ka bani kudin dana ranta maka." Yaja tsaki da fadin." Wai shin har nawa ne kudin naki?" "Dubu biyu da dari hudu ne kada ka manta yau kwananka uku baka ba da ko kwabo ba tun daga safe har dare ni nake d'awaniya da gida to tunda Allah yasa yau ne cikar alkawarin da kayi min ba zan fita ba sai ki biya ni kud'ina." Kashingid'a yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa. Tace."Jamilu meye haka zaka dinga yi min murmushi kada fa kayi min wata magana don wallahi baza mu wanye lafiya ba." Ya sosa gemunsa da fadin." Ki je yanzu zan fito zan baki kud'inki ina jin shikkenan ko?" Kai ta girgiza da fadin." Ba fa zan fita ba sai da kud'ina a hannu. Ya mike zaune da fadin." Idan kika matsanta min wallahi zan ha naki ni nace kije zan baki idan na fito sanin kanki ne bana san takurawa." Ta yi jim tana kallonsa kafin ta gyada kai da fadin." Na kawo maka abincinka ne.? Sai da ya mula tukkuna ya ce."Aa ki bawa Jamila da Shahida suka 'kara ni na koshi." Ba tare da tace komai ba ta juya ta fita, koda ta fito daga dakin a maimakon tayi abinda yace kai tsaye kicin din ta nufa ta dauko abincin nasa tasa a gabanta ta dinga ci sai kace jaka, Walida dake sud'e hannu tace."Talatu d'an k'ara min wallahi ban koshi ba." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kai loma bakinta, yarinyar dake mara kunya ce ta yatsine fuska da fadin." Talatu ki dai ci a hankali kada ki 'kware wannan loma haka." Bud'e baki tayi za tayi magana aikuwa ta shaki shinkafa ta hanci tari ya sar'ke ta ta dinga yi hawaye na zuba, yarinyar ta tashi ta bar gurin ba tare data debo mata ruwa ba. Shahida da Jamila haka sukaci abincin ba tare da sun 'koshi ba, suka fito domin wanke hannu nan suka ga Talatu tayi wurjajan ido yayi jawur har yanzu da sauran tarin amma saboda zulama bata daina cin abincin ba. Shahida ta banka mata harara ta wuce dama duk sanda tazo gidan abinda ke shiga tsakaninsu kenan harar juna, sai taso take gaishe da ita, Hadiza ta fito daga d'aki Talatu tace."Kinga 'yar iskar yarinyar nan saboda ban zuba mata abinci ba take hararata. Hadiza tace."Take harararki kamar sa'arki." Tace."Au! keda baki ta'ba gani ba? ai a duk san da zata zo gidan nan hararace take shiga tsakaninmu." Bagazan! bagazan ta nufi inda take ta juyo da ita suka fuskanci juna, murya ta d'aga da fadin." Don Uwarki mahaifiyarmu sa'arki ce?" Jamila tace."Hadiza neman fitina bashi da amfani me kuma tayi miki? Ta juya tana yi mata bayani yayin da ita kuma Shahida ta juya inda Talatu ke zaune ta dinga watsa mata muguwar harara tunda ta lura da abinda bata so to ta daura d'amarar 'bata mata rai. Talatu ta rike ha'ba da fad'in.'' Ni kike harara don Ubanki! ta dauke kanta tana jan tsaki tare da niyyar barin gurin. Hadiza ta fizgo kafad'arta tana nema ta kai mata duka, sai ta rike mata hannu cikin yanayin maganarta tace."Hadiza ki kiyaye ni wallahi ni nafi karfin ki dake ni." Ta fizge hannunta tana d'ura mata ashar!! Ya fito d'aga daki da yanayin bacci a tare dashi ya ce." Baku da hankali ne? sukayi shuru ya kalli Shahida da fadin." Me yasa duk lokacin da ki kazo gidan nan sai anyi rigima dake? Ido ta zuba masa, yaja tsaki da fadin." Ana magana kin tsare mutune da ido kizo ki tafi inda ki kafi wayo." Da yake da 'karfi yake maganar duk taji komai sai tace." Ai na dawo gidan ubana da zama." Talatu ta zabura! ta mike tsaye da fadin." A'ina.? Babu tsoro tace." A nan." Jikinsa ya mutu ya ce."Kinyi mata laifi ko?Fashewa tayi da kuka ta durkushe a gurin!. Talatu cikin masifa ta ce."Wallahi ko kukan jini za kiyi baki da gurin kwanciya a gidan nan aikin banza kawai." Ya kalleta da fadin." Kin san dai 'yata ce ko?" A fusace! Tace."Na sani amma wallahi ba zan zauna da ita ba." Ya girgiza kai da fadin.'' Duk lokacin da nayi ra'ayi 'yata zata dawo hannuna da zama." Tana numfarfashi! tace."Ni kuma a ranar zan tattara kayana na bar maka gidanka domin kuwa ba zanyi kishi da uwarta nazo nayi da ita ba. Murya ya d'aga gurin kiran sunanta, ta d'ago kai tana kallonsa fuskarta gaje-gaje da hawaye, Ya ce."Tashi muje ki fad'a min laifin da ki kayi mata." Ta mike tana share hawaye tabi bayansa zuwa dakinsa, kallon banza Talatu ta bisu dashi tayi k'wafa tana girgiza kanta. Duk abinda ya faru ta sheda masa tana kuka, ya ce."Kiyi hakuri kinyi sara a bakin ga'ba matsalar Baba Asabe kudi za'a biyata kud'inta" Cikin izzah! da nuna isa yayi maganar kamar wanda yake da burin biyanta kud'in dawainiyar da tayi masa daga farko har 'karshe. Yasa babbar rigarsa da fadin." Tashi mu tafi." Ta mike da sauri ta fito, shima ya fito yana kokarin kulle kofa tazo ta ta rike k'ugu tare da jan tunga a gabansa. Hannu yasa cikin aljihu ya zaro sabbin 'yan dubu-dubu uku ya watsa mata. Ta tsuguna tana tsincewa da fad'in." A banza dai duk abinda za kayi ni na rufa maka asiri." Ya gyara zaman hularsa ya kama hanyar fita ba tare da ya tanka mata ba. Ta kalli Jamila dake kan rijiya a zaune ta ce." 'Yar uwata na tafi na gode da zumunci." Jamila tana murmushi tace."To Aunty Shahida ki gaishe da Baba Asabe da kyau." Tace." Za taji da kyau." Hadiza tace."Banzaye kawai wannan munafurcin naku babu inda zashi." babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Shahida tabi bayan mahaifinsu ita kuma Jamila ta shige daki tana jiyo irin zagin da sukewa Shahida tamkar maguzawa! *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO... _____ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Kuyi join domin samun damar karanta littafi na daya. *Marubuta* _Nimcy luv (Sarauta)_ _Hassana Bamalli_ _(OmApanan)_ _Sa'adatuBintuAbdullahi_ Ina godiya 'kwarai💯 Kyautar feji zuwa ga: _*Ummul-Khairi Shaik*_ _*Muhammad (Kairatu)*_ Binta tana godiya da k'auna tare da k'warin gwiwa🥰 *7&8* Jamilu Ya hujaj! mutum ne mai fara'a da wasa da dariya shiyasa yake da jama'a yara da manya duk inda ya gifta za ka ji ana fadin "Ya Hujaj! Shi kuma ya dinga washe baki kenan yana dariya idan da kudi a jikinsa ko nawa ne sai sun k'are domin bai iya gwaninta ba kyautar dubu biyar a gurinsa ba abu ne mai wahala ba, mutuk'ar yana da kudi to na bajinta ne amma fa

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});