Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 49

Chapter 49

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don haka dawo ki tsaya." Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta tsaya tana facing d'in shi, ya 'kura mata mayunwatan idanuwansa masu je fata cikin tashin hankali. Sai da ya gama karyawa tsaf! sannan ya tashi ya fito daga tsakanin kujerun ya nufi gurin da take tsaye. Ta ji fad'uwar gaba sosai! amma ba ta karaya ba, domin kuwa tasan duk shaid'ancin mutum bai fi karfin addu'a ba, tana da tabbacin cewa sai ta samu rinjaye a kansa. Daf da ita ya tsaya yana lumshe mata shu'uman idanuwansa. Ta kawar da fuskarta tana cigaba da nanata addu'ar neman rinjaye a bakinta. Ya sanya hannu da nufin cire hijabin jikinta. Ba tare da jin nauyi ba ta buge hannunsa da karfin gaske! bahaushe ya ce ." Idan babba ya zubar da girmansa yaro zai iya hawa kai ya tattaka. Ya dube ta da fad'in" Ba ki ji nauyin abinda ki kayi ba?" Zum'bura bakinta tayi tana d'an ture shi da 'kokarin so ta fita daga tsakaninsa domin ya babbake gurin yayi mata rumfa. Ya sake kama 'kasan hijab din a karo na biyu, sai ta sake wancakalar da hannunsa, ta tsinci kanta da nuna shi da yatsa da fadin" Wallahi zan baka mamaki yanzu nan!" cikin zafin zuciya ta fad'i maganar jikinta na wani irin karkarwa! Bai wani tsorata ba, sai ma sake matse ta da yayi jikin bango (garu) ya tallafo fuskarta da hannunsa d'aya, aikuwa karan hancinsa dake daf da bakinta ta gartsawa cizo! tana nema ta gutsire masa saman hanci! babu shiri ya matsa gefe yana shafa gurin da ta cije shi wanda yayi sheda tare da rurucewa! Zazzafar harara! ta buga masa kafin ta ja masa dogon tsaki! tana 'kun'kuni! ta wuce ta bar shi a tsaye a gurin yana bin ta da kallo har ta bud'e 'kofa ta fita. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Ga hanyar da za a biya kudin littafin....Normal group #500 posting sau daya a rana, Vip group 1k posting sau biyu a rana. account number.... 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp da wannan lambar.07084653262....Mutanan Nijar za ku tura dala dari. Vip jakka daya, za a turo mini ta WhatsApp. Allah ya yassare.* 55&56 A nutse ta d'an tsaya a jikin daya daga cikin kujerun cin abincin, amma bata yarda ta kalleshi ba, kanta yana 'kasa, sai dai a jikinta ta ji yana kallonta. gabanta ya dinga fad'uwa tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! 'kadaicewarsu, a falon su biyu yana nufin abubuwa da yawa, saboda haka sai tayi ta maza! ta d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yalla'bai ko kana bukatar wani abu ne?" Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari. Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata. Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma k'afafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba. "Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba. Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita. Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta. Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa. Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane! Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan. Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa! Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce. _"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_ Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka. _Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_ Ya dawo mata da amsa kamar haka. _"Maigida na ya wuce komai a guri na, ba zan iya yin jayayya dashi ba saboda haka kiyi hakuri kawai"_ Kasa bashi amsa tayi sai uban kukan da take shirga! wai shin ita ya za tayi ne? wannan lamari da faru ya fara sanya ta cikin shakku da fargabar zama a gidan. Kwana tayi cikin zullumi da tunani da kuma rashin madafa, amma tasa a ranta cewa Allah shine madogara a gare ta. Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe. Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai. Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo." "Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari. 'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima. Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana. Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske. Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});