Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu." Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu." Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana." Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare su ka yi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita." Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar fige ta da karfin gaske ta fita daga gidan, kai tsaye rijiyar zaki ta nufa gidan Hajiya Zaliha domin sunyi waya da Mamanta ta ce ta sameta a gidan domin itama ba ta jima da sauka a garin ba. **** Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa. Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri. Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru." Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.'' Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .'' Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa. **** "Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba." Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka." Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.'' "Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi. Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri. Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka." Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi. Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ." Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata." Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ." Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi. A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya. **** Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin. Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin. Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});