Chapter 23
Chapter 23
ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci." Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane." Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi." Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina." Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake." Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba. Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin." Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta. Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado. Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu. Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba. Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa. Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar. **** Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye. Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa. Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa. *Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *31&32* "Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar. Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita. "Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa! Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan! Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali. Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse? Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata k'arfin iko na a kan 'ya ta." Ta ce." Me take nufi to? Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana." Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke." Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa. Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa. Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya." Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!" Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki." Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan." Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta." Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50