Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi Joining domin samun damar karanta littafi na d'aya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *23&24* Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidansa wanda ke unguwar giginyu, cikin kamala ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai k'aramin hannu kansa sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi. Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu. Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku." Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar. Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye." Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali." Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria. Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban?" Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne." Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida. Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai. Shi da abokansa suka rasa bakin godiya. To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu. **** Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take. Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci. Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji." Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata. Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma. Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai." Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri. Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci. Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba. Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba. Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta. Bakinta na rawa ta kirayi sunansa. Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake k'asan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu. Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki. Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.'' Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take. Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda take da 'kyankyami Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});