Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *9&10* Kwana biyu da faruwar al'amarin Shahida ta samu sau'kin tsangwama! gami da aikace-aikacen da aka d'ora mata, Yanzu Baba Asabe tana k'okarin kamanta adalci a tsakaninsu, tunda ta fahimci cewa yarinyar na yi mata. mummunar fahimta. Tsakanin Saliha da Shahida babu mai magana da d'an uwansa gaba su ke yi duk da laifin na Saliha ne tunda a daran ranar da al'amarin ya faru ita Shahidan tayi mata magana amma taki amsawa. Sai kawai itama ta watsar da ita ta cigaba da sabgoginta ita kad'ai, Ita kuwa Baba Asabe jira take Kawu Musa yazo ta sheda masa abinda yake faruwa tunda ita basa jin maganarta. Baba Asabe na daga cikin rumfar kwanon da take zama domin sayar da abinci, gabanta babban baho ne cike da shinkafa fara da gurasa a ciki gefe guda kuma manya-manyan tukwane ne a kan murhu cike da miyar tattasai da taushe da nama tare da 'kashi a ciki, miyar sai k'amshi take. Baba Asabe ta jima tana sana'ar sayar da abincin shiyasa tayi suna a unguwar kowa ya santa a kan sana'arta kayan miya mota guda ake sauke mata, bayan sana'ar sayar da abinci tana sayar da man gyada da manja da sauransu, mijinta ya kai shekara ashirin da mutuwa tunda ya mutu ta kafa sana'a da ita ta dogara take rufawa kanta asiri har ta taimaki wani d'anta Kawu Musa da ya rage mata a duniya tana masifar sonsa shiyasa take fifita 'ya'yansa akan kowa kuma duk rabin abinda take nema nasa ne kullum idan yazo gidan kamar k'aramin yaro sai ta 'dauki kudi ta ba shi, shi kuma saboda rashin tausayi yasa hannu ya kar'ba, Kawu Musa babu yanda be yi da ita ba akan ta mayar da Shahida gidan ubanta tace A'a ba zata mayar da itaba tana kallonta a matsayin mahaifiyarta, A ransa baya son zaman Shahida a hannunta a ganinsa ba itake da alhakin d'aukar nauyinta ba shiyasa duk sanda yazo gidan sai ya zuga ta akan yarinyar watarana ta d'auki maganarsa sai su had'u suyi ta caccakar uban yarinyar a gabanta don ma dai kurma ce ba taji sosai amma dai duk ranar da suka so ta ji zagin da sukewa ubanta da 'karfi suke maganar Sai dai kawai ta shiga daki tayi kuka, Wannan damar Saliha ta samu take yi mata iskanci iri-iri. Kabewa take ferayewa ita kuma Saliha tana gyara Alayyahu, Haladu yayi sallama a gidan, kai tsaye gurin da'aka tanadar musu ya nufa ya zauna tare da cire hularsa ya kifa a gwiwarsa. Ta kalleshi da fadin." Haladu da alama yanzu ka dawo daga kasuwa.? Yace."Kwarai kuwa uwar towo dawowa ta kenan ko gida ban shiga ba na garzayo gurinki domin na 'barje gumi na." Baba Asabe tasa dariya tana gyara zaman lalitar dake rataye a wuyanta, tace."Hohoho! Haladu ba dai son dad'i ba ina jin dai kana adalci a gidanka ma'ana kana yi musu kyakykyawan cefa ne." Gemunsa ya sosa cikin inda-inda ya ce."Sosai nake musu cefane mai kyau amma shashashan babu abunda suka iya sai rage kudin cefane gabad'aya babu wacce ta iya abinci a cikinsu shiyasa nake zuwa nake cin kud'ina anan." Tana 'yar dariya ta ce." To Allah ya rufa asiri me zaka siya shinkafa ko gurasa da miya?" Ya ce."Shinkafa da miya da rabin kaza." Da yake da dan 'karfi yayi maganar yasa tayi saurin kallonsa tana girgiza kai dama haushinsa ta ke ji ta san abinda za tayi masa. Baba Asabe ta had'a masa komai ya juya bayansa yana ta kai loma. Saliha ce kad'ai ta lura da fitarta to da yake ba magana suke da juna ba shiyasa bata tambayeta ina za ta je ba. Minti biyar ta dawo ta cigaba da aikinta, ba tare da damuwar komai ba. Lokacin da Haladu yake ya gar cinyar kaza lokacin suka shigo gidan hayaniyarsu tasa cinyar kazar ta su'bce ta fad'i kasan gurin, ya lashi 'kasan bakinsa yana bin su da kallo. Indo Uwar gidansa tabi cinyar kazar da kallo kafin ta kalleshi sai muzurai yake kamar kace kyat ya ruga a guje alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare dashi. Lubabata amaryarsa ta sunkuya ta d'auki cinyar kazar tana nuna masa da fadin." Ashe abinda kake kenan a bayan fage Haladu wai me yasa kai azzalimi ne? Kullum sai kace mana kasuwa babu ciniki ashe nan kake zuwa ka baje kolinka mu ka barmu da wahalar yara da da'wainiya dasu. Indo tayi 'kwafa tana girgiza kai tace."Yau Allah ya tona maka asiri Haladu daga nan gidan sai gidanmu dama na gaji da zaman wahalar nan." Baba Asabe tace." Haba Indo ai ba za'ayi haka ba idan rai ya 'baci hankali ake sawa ya duba shi kiyi hak........"Ke kin ga dakata Asabe!" Lubabatu ce ta katseta tana hura hanci ta ce."Ai dole ki fadi haka mana tunda kullum ke yake zuwa ya yi wa ciniki saboda haka kawai ki ja bakinki kiyi shuru. Baba Asabe ta rike baki da fadin." Lubabatu rashin kunya zaki min daka gyara kayanka sai ba'kar magana. Cikin borin kunya ya ce."Ki rabu dasu Uwar towo duk in da za su je su tafi dama meye amfaninsu ku tafi din, amma ku aje min yara na domin ina da yanda zanyi dasu kudi kuma dole na ci abuna tunda ba uwar uban wani ne ya nema min ba." Fadin wannan magana da ya yi sai ya fusata! su suka shiga ci masa mutunci da gore-gore! Baba Asabe hankalinta ya tashi mutuka tsoronta Allah tsoronta Annabi kada Haladu ya saki matansa akan wannan dalilin. Da kyar ta rarrashesu suka fita daga gidan, shi kuwa Haladu har bayan magariba yana gidan ya kasa tafiya ashe duk fuffukar 'karya yake ya aika yara har biyu domin su duba masa sai su dawo suce gidan a bude yake Indo da Lubabatu suna nan babu inda su ka je Jikinsa yayi masifar sanyi fargabarsa d'aya kada ya shiga gidan su ci 'kwal ubansa dama kansu a had'e yake duk kisan mummu'ken da yake musu basa fad'a da junansu k'o'karinsu ya za'ayi su rufawa kansu asiri. Tsaki ya ja ya cire hularsa ya ajiye ya cigaba da zare ido akan jama'ar dake shige da fice a gidan. Sai da jama'a su ka yi sauki kana ta kalleshi da fadin." Haladu kayi jugum! ka tashi kaje gida komai yayi zafi maganinsa Allah amma don Allah ka sauya halinka ban ji dadin abinda ya faru ba kaga yanzu ni kaina a cikin zargi nake tunda a gabanka matarka Lubabatu take nuna ni da ya tsaya tana so ta dauki laifin kacokan ta dora min alhalin

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});