Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mata komai ba. "Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya. A dakile ya amsa. Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji." Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?" A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata. "Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?" "Ba haka bane Daddy." Ya ce." Nayi 'karya kenan." "A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take." Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana." Tana kuka take bashi hakuri! Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba." Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace! Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo hanyar warware matsalarta. **** "Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa." Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi da safe. Ta d'an 'bata fuska da fadin." Har kin manta ko?" Girgiza kanta tayi ta ce." Ke shahida magana mai muhimmanci ita nake ajiyewa a cikin raina domin abubuwan da suka dame ni suna da yawa." Ta 'karasa maganar tana kokarin kwance lalitar dake d'aure a k'ugunta. Sunkuyar da kanta tayi idonta yayi ja! alamun ranta ya 'baci! Ita kuwa Saliha dariya kawai take mata tana 'yan 'kananun maganganu wanda ta san ba za ta ji ba. Wutar nepa a ka kawo Saliha da sauri ta kunna musu fanka domin zafi ake a garin. Ita kuma Shahida ta je ta dauko hijaban ta domin ta goge. Ta kalle ta da fadin." Kin san dutsen gugar nan yana da jan wuta Shahida da ki bari na gama kallon labarai idan an gama sai kiyi gugar ki." Ta ce."Baba idan su ka dauke wutar fa.''? Ta ce." A'a ba zasu dauke ba insha Allahu, ke Saliha kunna min talabijin din NTA KANO zaki kai." Ta ce." To." da sauri ta janyo 'yar yawo (cover socket) ta jona kayan kallon tana kokarin gyara Area domin hoton ya fito. Shahida d'aki ta shiga ta kwanta ta shiga tunanin masoyinta. An gama labaran, 'karshen kawai suka riska. A in da mai gabatarwa yake fad'in kanun labaran 'karshe, cewa wannan Attajirin d'an kasuwar Alhaji Saddiku wanda aka fi sani da *'Dan gaske* zai yi rabon shinkafa a babban company sa dake sharad'a, za a fara rabon abincin da karfe hudu har zuwa karfe goma na dare. Baba Asabe ta ce." Wannan karon ma sai na je ko Allah zai sa na da ce." Saliha ta ce." Da rabon kiyi asarar kudin motarki, har kin manta 'bakar wuyar da ki kasha a wancan lokacin" Ta ce." Wuya ai mai shigewa ce 'yar nan a wannan zamanin shinkafa 'yar gwamanti babban buhu ai ko kwana zanyi a gurin ba zan damu ba mutukar zan samu, saboda haka yanzu ma zan tashi na shirya sai ki kula da masu shige da fice. Girgiza kanta tayi a zuciyarta ta ce." Wanda ya 'ki sharar massalaci ai yayi ta kasuwa! samun shinkafar nan ai sai mai tsananin rabo. "Baba ina za ki je kuma?" ta fada tana kokarin tashi zaune. Tana gyara hijab din dake wuyanta ta ce." Unguwa zani amma ba zan dade ba insha Allah." Ta ce." To don Allah kiyi sauri ki dawo kada kuma ya zo ba kya nan." "To." kawai ta ce ta kama hanya ta fita da sauri tana mamakin wautar yarinyar. **** Gurun cike yake da mata da maza dattijai da matasa matan aure kai harda 'yan mata, dama irin wannan na faruwa mutane babu uzuri sai su tarkato 'ya'ya da jikoki a zo a bi layi kowa kansa ya sani idan kai ka samu ba zaka bari d'an uwanka ya samu ba, wannan shine abinda yake cutar damu wato son kai. Gurin yayi cikar kwari! hayaniya ce kawai take tashi wasu ma fad'a suke yi akan bin layi mussaman mata wasu babu kamun kai! don ma da akwai masu tsaro (securities) da abinda za ayi a gurin sai yafi haka. Duk yana kallon abinda yake faruwa ta cctv camera ya umarci yaransa cewa su je su raba number kowanne ya san matsayinsa lokaci yana cika afara rabo." Abinda ya faru kenan mutum goma ke raba number 'bangaran maza mutum biyar 'bangaran mata mutum biyar. Baba Asabe dai ita ce ta dari hud'u da talatin da shida😂 ta tambayi cewa ita ce ta nawa ? ya fada mata cewa sai an bawa mutum dari hudu da talatin da biyar kana za a zo kanta, amma bata sare ba! ta gyara tsayuwarta a gurin tana adduar Allah yasa tana da rabo. Wasu na fita wasu na shigowa haka ake ta turmutsutsu! a gurin, duk wanda rabo ya zo kansa ana bashi yake jan buhun ya fita daga gurin da yake kan titi ne abun hawa baya wuya. Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da farar dara irin ta larabawa ya nade da farin hirami sai k'afarsa dake sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi. Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi. Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. *"Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! bangon sukari kowa ya jingina sai ya lasa! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka 'DAN GASKE!* *'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya."* Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});