Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

raye ba za'ayi wannan auran ba." Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba. Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar." Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu." Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba." Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so." Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake. A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana! Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa." Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan." Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa. A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci! Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata. Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani! Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido. Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta. Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin. Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin. ''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."? Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka." Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."? Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci. Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."? Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa." Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza! Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin." Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi." Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin. Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya. Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......*MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. *33&34* *KANO* Unguwar giginyu. Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take. Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai! Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje. Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko? A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah." Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida." Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar. Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba. Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara." Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka! Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar dalili ita kad'ai ce babu wasu. shiyasa take lallabata. ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba. Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa. Tana rufe

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});