Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa. Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?" Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema." Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo" Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata." Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa. Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya. Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba. Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta. Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi. Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu. Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne. Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan. Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escorts dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! "Wannan ai shahararran attajirin nan ne da ake nuna fuskarsa a tibi." sake kallonsa tayi a karo na biyu cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara ya nad'a farin rawani a saman hular. as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an. Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya k'araso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta. Bai amsa ba sai dai ya yi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa. Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya. Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi ciyayi! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske. A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta. Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata. A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta, Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba. Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya." Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta . Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba." Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa." Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya. Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya." Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata. Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?" Girgiza kanta tayi ta ce." A'a babu komai, sai dai ki zauna ki d'ebe min kewa ai na ji dad'in zuwanki gidan nan saboda zaman kad'aici yana damuna, Shukura kuma ba gwanar zaman falo ba kullum tana daki da waya a hannu." Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin maganganunta, to shin maigidan bashi da aure ne? ko kuma ba a gidan yake zaune ba? bata da mai bata amsa sai kawai tayi shuru, tare da tsirawa tv ido kallon kawai take amma ba sosai take jin abinda ake fad'a ba. Cikin riga da wando na bacci ta fito daga d'akinta. ganinta a zaune yasa tayi turus! tana kallonta babu annuri a fuskarta ta kalleta da fadin." Hajiya wannan wacece kuma?" ta fada tana nuna ta da yatsa. Tana shirin bata amsa ya shigo, duk sai su kayi shiru suna kallonsa, a

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});