Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.* *08069459550* *08039451082* _*'Karshen littafi na d'aya kenan, sai mu tara a cikin littafi na biyu, wanda ya kasance na kud'i #500 vip 1k za a tura kudin ta wannan account din...0542382124...Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan numbers.. 07084653262.or 08089965176. BINTA UMAR ABBALE*_ 59&60 Ya jima yana jinyyar karan hancinsa kafin ya daina masa ciwo, sai dai sa'i da lokaci idan ya tuna abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar sai yayi murmushi! cikin zuciyarsa yake addua'a akan Allah yasa ta cinye jarrabawarsa, domin d'an zaman da su kayi tare sonta da k'aunarta ya gama mamaye jini da gangar jikinsa. A na ta 'bangaran kuwa daina walwala tayi a gidan, motsi kadan za ta tsorata, domin tana fargabar kada ya kawo mata farmaki har gurinta. Bata sake saki jikinta ba sai da su Hajiya suka dawo sannan. ta warware amma duk da haka Hajiyan sai da ta lura da wani abu, sai take tambayarta ko akwai abunda ke damunta ta daina sakewa, da sauri ta ce "babu komai wallahi kaina ne kawai yake ciwo." Hajiya ta ce'' Ai fa na ga alama saboda ba haka muka tafi muka bar ki ba, to amma kin shedawa mijinki domin naga kina da k'wauron baki'' Murmushi tayi ta ce." Eh na fada masa har ya siyo min magani na sha." Ta ce."To Allah ya raba lafiya." domin ita Hajiyan a tunaninta ko ciki ne da ita. Ta ce." Ki je ki kwanta ki huta ai sai da lafiya ake komai." Sosai tayi farin cikin hakan, sakamakon ganin saukowarsa tasan tabbas idan yana gurin ba zata iya sakewa ba. Ya zauna kujerar dake fuskantarta. sai ta sunkuyar da kanta a hankali ta ce." Ina kwana?" ya d'aga mata hannu ba tare da ya amsa ba. Hajiya ta kalle shi da fadin." Yarinyar nan bata da lafiya har nake zargin ko ciki ne da ita?" Gabansa ya fad'i ya kalle ta da fadin." Wane irin ciki kuma Hajiya duka-duka yaushe su kayi auran?" Murmushi tayi da fad'in." Yo tsakanin mace da miji ai sai Allah, ai yanzu kamar tuntu'be akeyi dashi a hanya, shine nake tambayarta mijinta ya sani, ta ce" Eh har magani ya siyo mata." Ya kalle ta tare da bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce" Ke da gaske ciki ne dake?" Kunya duk ta rufe ta, sunkuyar da kanta tayi tana jin nauyi don gani take kamar maganar tayi kama da ta rainin hankali! kwana d'aya kacal da aurensu ya dauk'e mata miji ya kai shi uwa duniya, zai zo yana tambayarta sai dai idan shine yayi mata cikin. ita da zuciyarta take magana. Hajiya Saude tasa dariya da fadin." Kai ma dai da wani abu, to idan shine a tunaninka za ta fad'a maka ne? ni ma hasashe kawai nake. Ba tare da ya ce komai ba ya dubi agogon dake daure a hannunsa, ya kalle ta da fadin " Hajiya zan fita" Ta ce" To Allah ya bada sa'a." ya amsa da "ameen yana kokarin tashi. Shukura ta fito daga d'akinta. Sai ya tsaya yana kallonta, ta ce." Daddy ina kwana?" ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta ce."Hajiya ta fad'a maka sakon mommyna." Ya kalli Hajiyan domin jin 'karin bayani. Ta ce" Neman magana ne kawai irin na Hajiya Fatima, mun shirya dawowa gida ne shine take ba mu sa'kon gaisuwarta gare ka. Bai ce komai ba ya kama hanyar fita, sai suka bi shi da kallo jikinsu a sanyaye Hajiya ta riga tasan halinsa tun yana yaro mutukar ya bar abu to bar shi har abadah, wannan dalilin ne yasa take tausayawa Hajiya Fatima duba da irin wahalar da take sha a kansa ya'ki sauraranta, shekara da shekaru da rabuwar auransu, ta'ki aure ita lallai tana jira yazo ya mayar da ita d'akinta, in da shi kuma ya ci alwashin sai dai ya mutu babu aure mutukar sai ya zauna da ita ne. 'Yan uwa da ita kanta kakar tasa sunyi-sunyi har sun ha'kura, domin mai daki shi ya san in da yake masa oyoyo, shi kadai ya san irin wahalar da ta bashi a lokacin da suke tare. **** BAYAN KWANA BIYAR Tana zaune 'kasan kafet tana cin abinci wanda ci kawai ta ke yi saboda ta kori yunwa ba wai don abincin babu dadi ba, A'a sai don ta san mutukar ta kwanta da yunwa to tabbas zata tashi a galabaice! shiyasa take tuttura abincin tana had'awa da ruwa. Motsi ta ji ana kokarin bud'e kofar shigowa, gabanta ya yanke ya fad'i! ta tsirawa kofar ido tana addua a zuciyarta, domin ba ta kawo cewa mijinta bane ta fi tunanin maigidan ne da yake kai mata hari a duk lokacin da su had'u sai ya san yanda yayi ya ta'ba jikinta, wannan abu yana yi mata ciwo mutuk'a! ita ba abun ta zazzage shi ba tana cikin gidansa, sai dai duk sanda ya ta'ba jikinta ko ya cire mata dankwali sai ta yini tana share hawayen takaici wanda ya ajiye ta ma bai ta'ba ri'ke mata hannu ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta. Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje! Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta. Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba. A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba. Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta. Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu. Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});