Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yaran ashe ba zai jima tare dasu ba Allah ya dauki rayuwarsa. Uwargidansa dama bata haihu ba wannan dalilin yasa ana raba gado ta tattara kayanta ta tafi garinsu. Gida ya rage Baba Asabe da 'ya'yanta, Tun daga lokacin ta kafa sana'ar sayar da abinci wanda da yawa mutane da dama suka dinga ganin rashin hankalinta a ganinsu ai bata wuce aure ba amma zata zauna ta lalata 'kuruciyarta a banza a wofi, To Duk zantukan dake yawo a gari suna dawowa kunanta, tayi banza da surutan mutane ta cigaba da sabgarta da kula da yaranta. Da yawa wasu mazan da biyu suke zuwa sayan abinci gurinta domin su kafa gwamnatinsu, cikin ikon Allah Alhaji Haruna ya samu shiga a gurinta ta kudiri aniyar auransa domin tana yi masa kallon nagartaccen mutum ashe kallon kitse takewa rogo auran beje ko'ina ba ya lalace a sakamakon nuna kyara! da hantara! da yake akan 'ya'yanta. Da farko ta nuna masa kuskuransa akan abinda yake ta kuma gargad'eshi ya daina. Sai shi kuma yayi kunnan uwar shegu da maganarta duk sanda yazo gidan to fa yaran basu da walwala sun dinga takurewa kenan gabadaya sun tsorata dashi domin kuwa wani sa'in har fakaitar idonta yake ya doke su, mahaifinsu kuwa dake karkashin 'kasa yana shan zagi! Sosai Alhaji Haruna yake *(Kishin kushewa)* akan yaran. Baba Asabe data gaji da iya shegen da yake mata sai kawai ta fito masa a mutum tayi masa wankin babban bargo, 'Karshe tace dashi babu lallai babu dole idan ba zai juri zama da 'ya'yanta ba to ya saketa domin kuwa ba zai zo har gida yana cin arzikin yara ya takura musu ba.'' Alhaji Haruna ya fusata! ransa ya baci a ganinsa babu amfanin auran macen dake da 'ya'ya tunda duk tsiya watarana sai ta tuna ubansu kuma soyayyar da take nunawa yaran ai kamar ubansu take nunawa, kawai sai ya yanke shawarar sakinta domin dai shi yana kishin ya budi ido yaga yaran a matsayin 'ya'yan wani ba nasa ba, Sai kawai ya rubuta mata saki biyu ya kama gabansa. Baba Asabe ranta ya baci sosai tayi kuka😭 mai yawa ta share hawaye ta barwa Allah lamarinsa, amma a zahirin gaskiya abin ya jima yana cin ranta ace wai shikkenan daga zarar mijin mace ya mutu ko kuma mace ta rabu da mijinta kan wani dalili shikkenan ita da 'ya'yanta sun zama abun 'kyama da wulakantawa a gurin wasu mazan, wannan ba daidai bane wallahi maza kuji tsoron Allah ku tausayawa mata mutukar mace zata sadaukar da rayuwarta a kanka da 'ya'yanka meye abin gudu a tare da ita, 'Ya'ya ne abin gudu kai ma kana dasu, kuma ba dole akace ka rike 'ya'yan da ba naka ba, *(Maza idan zaku auri bazawara to kuyi adalci kada kuso zuciyarku kan wani dalili shi aure na mutum biyu ne yarda da aminci shike janyo har a kulla auratayya amma sai kuga wasu mazan suna gudun mace mai 'ya'ya sai kace ance dole suyi wa yaran d'awainiya da d'an mutum da dukiya ba ai musu mugunta kuma ita rayuwa juyawa take wanda kake gudu sai ya taimake ka watarana)* Tun daga wannan lokaci Baba Asabe ta cire rai da aure kawai ta cigaba da neman kudinta, Allah kuwa ya shiga cikin al'amarinta tafi karfin yau da gobe da duk wani abunda ba za'a rasa ba. ******* Manyan mutane masu mutunci da dattako suka dinga turereniya gurin zuwa neman auran Mariya amma funfurus! ta shafawa idonta toka ta kore su, al'amarin daya fusata! Baba Asabe kenan ta rufeta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ta cigaba da cewa"Shi wanda kike kulafuci shin kina da tabbacin zai aureki? Babu wanda be san halin Jamilu ba gurin yaudarar yaran mutane me zakiyi da Jamilu manyan mutane masu mutunci suna tururrubi akanki! Ko kin dauka kinfi karfinsu ne? to bari kiji bayan kyawun jikin da kike dashi to baki da komai sai tarin muni duk ga 'yan mata nan masu kyau a gari wanda suka fiki komai basu dauki kansu wata tsiya ba sai ke to mutukar ni na haifeki ba zaki auri Jamilu ba." Da jin wannan magana sai ta dora hannu aka ta kurma ihu! tana kiran ta shiga uku ta lalace! Makota suka shigo suna tambayar ba'asi. Takaici da bakin ciki yasa Baba Asabe kasa magana ta koma ta zauna tana me cigaba da sabgoginta. Mariya ihu! take tana fadin." Ban ta'ba yi miki rashin kunya Baba ban ta'ba bijirewa umarninki ba duk abunda kike so shi nake so, ke kika zama gatana ban taso da ubana ba amma kin share min hawayen maraicin uba ina so kiyi min adalci a rayuwata kiyi hakuri na auri wanda nake so Jamilu shine rayuwata!" Jama'ar dake tsaye a gurin suka shiga mamakin al'amarin, Baba tace."Kun dai ji da kunnuwanku abunda take fada, Shin kuna da tabbacin Jamilu auranta zaiyi ko kuma yaudararta yazo yayi sanin kanku ne kafin yazo gurinta ya yaudari 'yan mata da yawa a cikin unguwar nan to me zai sanya ina ganin kashi da rana na taka auran Jamilu bashi da fa'ida tunda shi bashi da hali uwa uba kuma bashi da sana'a" D'aya daga cikinsu mai suna Huwaila tace."Ki yi hakuri ki barwa Allah al'amarin domin kuwa shi aure nufi ne na Allah kuma naji kina maganar Jamilu bashi da sana'a Aa yana da sana'a domin shago guda ne dashi a kasuwar wambai kawai dai aure ne be yi ba ya tsaya shiririta amma ki bari ni nayi miki alkwarin zuwa gidansu domin mu tattauna da mahaifiyarsa idan da gaske yake to ya fito ayi magana idan yana yaudaran yaran mutane to mu ba zai yaudare mu ba." Baba Asabe ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Huwaila Na gode Allah ya jishshemu alkairi." Huwaila ta amsa da ameen kafin ta rungume Mariya tana rarrashinta. Koda Huwaila ta samu mahaifiyar Jamilu da maganar kai tsaye tace ita sam bata ma san da maganar ba, amma idan ya dawo zata tambayeshi duk yanda ake ciki zata zo har gida tayi mata bayani. Bayan sunyi maganar da mahaifiyarsa ya nuna mata shi sam be san da wata Mariya ba ballantana ya je neman auranta saboda haka ta daina yarda da jita jitan mutane akansa aure nufi ne na Allah idan lokacinsa yayi to ko yana so ko baya so sai yayi. Sai jikinta ya mutu tace."Anya Jamilu ba zaka nemi maganin baki ba kuwa na fahimci cewar mutanan unguwar nan sun sanya maka ido." Dariya kawai yayi ya shashantar da maganar. Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin ya zauna yayi dogon tunani akan al'amarin a zahirin gaskiya Mariya bata da wani kyawun azo a gani amma kyawun jikinta yana mutukar rud'arsa yana masifar son cikakkiyar mace amma kuma yana so ya dawo gida yaga kyakykyawar fuska nayi masa sannu da zuwa. Murmushi yayi lokacin da ya tuna ai Ubangiji Allah ya hallata masa auran mace fiye da d'aya saboda haka zai auri Mariya saboda kyawun jikinta nan gaba kuma idan ya samu fara kyakykyawa sai ya aura ya samu ta shiga cikin taron jama'a wacce zai sanya a gaban mota yana zagaya gari da ita. Ya shedawa mahaifiyarsa shawarar da ya yanke kan cewa

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});