Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sheda." Ya kar'bi zungureriyar takardar ya yi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba. Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana. Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai." Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar maca ce san kowa k'in wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu." Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake buk'ata daga jikin mace falillahil hamdu.'' Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta." Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata." Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za ta yi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin. *Turkashi!* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *25&26* Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu. Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo. Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi." Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan." "Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne?" Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje." Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni. Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka." Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa. Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji." Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri." Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai. Jallabiya yasa ya fita. Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne. Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo." Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba." Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka." Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin." Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa. 'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka." Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah." Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul sai uban 'kyalli yake. Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa. **** Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya. Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara." "Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});