Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

koda yazo gaisuwa babu alhini a tattare dashi, kwalliya yayi sosai yana uban kamshin turare kamar sabon ango! komai na jikinsa mai tsada ne. Wannan shine abunda ya faru a baya, Shahida ta cigaba da zama gurin Baba Asabe tana kula da ita ci da sha suttura harkar karatu da kula da lafiyarta duk Baba Asabe ta dauka. sana'a take sosai domin macace mai kamar maza. Hujaj mantawa ma yake yana da wata 'ya a wani guri mutukar ya tuna da ita to yaje gidansu ne, mahaifiyarsa tayi masa maganarta, anan zai girba 'karya yace ai yana zuwa ya duba yarinyar har kudin abinci yana kaiwa, alhalin tun bayan haihuwarta bai sake zuwa gidan ba. gabadaya ya manta da ita, domin ko lokacin da Kawu Musa yaje kasuwa ya sameshi domin ya sheda masa lalurar yarinyar, sai da ya gama sauraransa tsaf sannan yasa hannu a aljihu ya dauko dubu daya ya bashi da fadin." Suyi hakuri insha Allahu zai zo ya dubata.'' Takaici yasa Kawu Musa ya fita daga shagon ba tare da ya karbi kudin ba. Tun daga ranar Baba Asabe tayi al'kwarin cewa ta daina neman komai a hannunsa, za ta cigaba da kula da yarinyar da ikon Allah babu abinda zai gagare ta. *Abubuwan da suka faru kenan a baya, yanzu zamu cigaba da labari* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin nan. Su yi joining domin samun karanta littafi na d'aya. A yi hakuri a daina bi na pravite Na gode* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *17&18* *AIRPORT* babban filin tashi da saukan jirage na Malam Aminu dake Kano. A hankali nake bin su da kallo sun jeru tsaf dasu cikin uniform gefen maza daban na mata daban, suna tsaye kowanne da 'yar jakarsa a hannu da alama screening ake musu kafin shiga cikin jirgin. Na dinga ayyanawa a raina cewa wata shekarar insha Allahu dani cikin masu hauke farali. Ajiyar zuciya na sauke a hankali na gyara takardar da biron dake hannuna nayi saurin matsawa gefe jin horn na mota a dab dani. Motar na zubawa ido tare da ayyana wani abu a raina. Da sauri na kalli jiragen dake daukar fasinja. sunan mutumin dake bayan motar irinsa ne a jikin jiragen dake d'aukar fasinjan domin zuwa kasa mai tsarki. *'DANGASKE AIR LINE* sunan dake tambare a jikin jiragen kenan. *'DANGASKE41* shine a rubuce a jikin hamshakiyar motar da tayi parking gefan da nake tsaye. Ido na zura akan motar domin ganin wanda yake kokarin fitowa. kafarsa sanye cikin brown din takalmi mai gidan yatsa da kafar da takalmi duk abin kallo ne. Ya fito bakinshi na dan motsi yanda na fahinta kamar addua yake. direban ya mayar da murfin motar ya rufe ya dan bashi hanya, kira kuma sai ya shigo wayarshi dake rike a hannunsa. A sace nake kallonsa ina sake nazari a kansa. babu shakka shine hamshakin attajirin mutumin nan da sunansa ya mamaye ko'ina a fadin Najeria da ma kewayenta. Yana sanye da milk din shadda 'yar gasken dinki tazarce rigar har kasa da aikin rumi a wuyan rigar kanshi sanye da brown din hula (dara) ya nad'e hular da farin hirami, hannunshi daure da wani irin agogon sarka white colour, a irin kallon kurrula irin nawa na fahimci cewa shi din ba yaro bane kamar dai yanda jama'ar gari suke maganarsa, babban mutum ne kamili mai shekarun da suka wuce arba'in, a kalla dai shekarunsa na haihuwa zasu kai hamsin da biyu zuwa da uku. da akwai tsalli-tsallin furfura a kwantaccen gashin da yake zagaye da bakinsa. Yana wayar ina kallonshi tare da nazartarsa tabbas ya cika cikakken mutum mai kima da mutunci gami da daraja dan adam ko ga yanayin kalamansa a waya, a nutse babu baragada da hayaniya. Escort dinshi uku suna tsaye a kusa dashi, sai kuma wata matashiyar budurwa dake d'an kama dashi kad'an a gefensa a tsaye sai zumbura baki take tana dauke kai tana sanye da jallabiya baka mai duwatsu tayi roling da pink din gale hannunta rike da wayoyinta da kuma handbang dinta. Murmushi yayi ya dan gyara zaman gilashin dake sakaye da idonshi yace." Yanzu dai ni already ina airport tare da Shukura da Hajiya bana tsammanin kan wannan dalilin zan janye abinda nayi niyya saboda haka duk abinda ya dace ayi ina gari ko bana gari duk abinda kayi dai-dai ne Sule a cigaba da duk abinda aka saba kada a sauke min tukunya a gida " Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Okey to hakan yayi Allah yasa albarka a ciki sai mun dawo." daga haka bai sake wata magana ba ya kashe wayar ya mayar da ita gaban aljihun rigar dake jikinsa. Ya juya yana kallonsu a nutse yace."Ina Hajiya.? Shukuran ce tayi magana. "Tana cikin mota wai kafafunta ke ciwo." Girgiza kai yayi ya san za'a rina dama ko a gida ma kuka take da kafafun amma saboda rigima tace lallai sai taje aikin hajji tunda da iko to duk shekara ba za tayi fashin zuwa ba. Hannu yasa ya bude motar gyangyadi take. sai abin ya bashi dariya yayi kadan kafin ya fara kiran sunanta. Firgigit ta bude idonta tana kallonsa, da sauri tace." Wane irin baccin asara ne yake nema ya kwasheni a mota nida nake da niyyar zuwa gaban ma'aiki SAW." 'Kokarin fitowa take tana cigaba da surutai." Wannan kafa ita kadai ce damuwata a duniya amma Allah yayi min komai saboda haka babu abinda zan fasa na ibadah." Duk wani bayani da k'auli da zai kawo mata ba zata yarda ba, shiyasa yaja bakinsa yayi shuru kawai yabi ra'ayin ta akan duk abinda takeso babban burinsa su rabu lafiya. Yace." Ki zauna kada ki fama kafafun bari akawo keke a sanya ki a ciki. "Wa za'asa a keke?" a tur'bune tayi maganar tana hararsa." Shima ya gyara fuska babu wasa yace." Ke mana ko kin dauka idan mun isa can ma zaki iya d'awafi da kanki.? Shuru tayi tana tunani. da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa domin wani irin ciwo kafafun nata ke mata. Ya d'an juya tare da kiran daya daga cikin Escort dinsa. Ya risina cike da ladabi yana sauraransa. "Adamu kaje ciki ka fito da keke za'a dora Hajia a kai." Ya amsa da sauri cike da bin umarni ya bar gurin. Ina nan tsaye a raka'be kamar wacce tayi wa sarki k'arya har wanda aka tura ya dauko keken ya dawo suka dora ta akan idona suka shige Ban samu damar bin bayansu ba saboda akwai securities (masu tsaro) sai na dinga leken su ta tsakanin 'karafuna anan ne naga yanda ma'aikata da jama'a fasinjojin dake gurin ke bashi girma, fuskarsa ba 'boyayya bace idan akayi duba da yanda jaridu da gidajan television media ke nuna hotonanshi. Yanzu ma dai tunda ya shiga gurin masu daukar labarai sai d'aukar hotonshi suke da duk wani motsinsa. Cikin kamala da dattako yake dagawa jama'ar dake gurin hannu yana amsa gaisuwarsu fuskarsa a sake saboda daraja dan Adam har sai da ya cire farin gilashin dake sakaye da idonsa. wannan ya bawa gidan television din NTA dama daukar vedio sa lokacin ya juya da niyyar

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});