Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

arzikina ya dawo." Yace."Ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauki insha Allah. ***** Alhaji Sha'aibu shi ya cigaba da kwantar masa da hankali, amma duk da haka kullum cikin lissafin wattanin cikin yake sai da ta haihu sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu shi ya bashi bashin kudi wanda yayi wa 'yar da aka haifa siyayya, sannan kuma shine ya jagorance shi zuwan gidan, kunyar duniya ta isheshi sai sunkuyar da kai yake, Alhaji Sha'aibun ne mai k'ok'arin magana Baba ta kalleshi da fadin." Da dai banyi niyyar yi maka magana ba amma ta kama dole sai nayi inaso ka bude idonka sosai ka kalli wannan 'yar dake hannunka." Yayi ta maza ya daga kai ya kalleta da fadin." Ai tunda na kalli yarinyar nan na tabbatar da cewa ni ne ubanta saboda haka don Allah Baba ayi hakuri kada ayi tone-tone duk abubuwan da suka faru a baya tsautsayi ne amma na san ban kyauta ba. Ta girgiza kai da fadin." To naji maganarka wane suna kake ganin za'a sanyawa yarinyar ."? Da murmushi a fuskarsa yace."Sunan mahaifiyata nake da niyyar sanya mata Maryama kenan." Tace."Shikkenan Allah ya raya ta yasa cikon addinin musulunci ce." gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah." Da zasu tafi ya ajiye mata dubu biyar da fadin duk hidimar da ta tashi tayi da kudin kafin ranar suna." Ba tace komai ba har suka fita daga gidan, Ta girgiza kai da fadin." Kullum yana fama da malin-malin(babbar riga) sai kace limami amma shaid'ancisa yafi karfinsa. Itama Mariya dake uwar dakin maganar da take kenan, idan yana magana kamar mutumin kirki amma mugun halinsa yafi dubu! gabad'aya yanzu bata kaunar ta bude ido ta ganshi ta tsaneshi don dai kawai kaddarar aure ta ratsa a tsakaninta dashi babu yanda za tayi tunda ya kasance uban 'yarta dole tayi hakuri ta manta da abubuwan da suka faru a baya. Ashe rigima ce take jiransa a can gidansa. Ya shiga gidan cikin nishadi da walwala domin kuwa gani yake kamar Mariya ta dawo gidansa ta gama tunda Alhaji Sha'aibu ya fada masa shawarar da ya yanke kan cewa shi din ya amince zai yi *(Auran kisan wuta)* da ita zai saketa idan tayi wata daya ko biyu a gidansa, To tunda ya fada masa wannan magana yake farin ciki tabbas ya san Alhaji Sha'aibu ba zai cutar dashi ba. A tsaye ya sameta a tsakiyar tsakar gidan sai kace wacce aka dasa! tsoro ta bashi da sauri ya kira sunan Allah kafin ya fuskanci itace yaja mummunan tsaki da fadin." Talatu ke wace irin jahila ce zaki tsaya tsakiyar tsakar gida sai kace aljana ko wani siddabarun kike min a gida."? Ta fusata! dama a wuya take ta hayayya'ko! masa tana kumfar baki tace." Rufe min baki algungumi! munafiki duk halin da kake ciki na sani tsohuwar matarka daka saki ta haihu har kana siyayya kana kai wa jaririyar data haifa bayan da bakinka ka furta cewa ba kaine ubanta ba." Ya daga mata hannu da fadin." Kinga saurara min! idan kuma kin 'kiya zanyi maganinki ni ba shashashan namiji bane da zaki titsiye da maganganun banza ni ne nan Uban yarinyar da Mariya ta haifa kuma a yau nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyata Maryama saboda haka ki hadiyi zuciya ki mutu." Ihu! ta kurma! taje ta cikwikwiye masa riga tana zaginsa da fadin." Ya cuceta wallahi ba zata yarda ba sai ya sake ta. Ya fizgeta daga jikinsa ya yar! a gurin yana fadin." Dama ai ke din baki dace dani ba saboda tunda na aureki komai nawa ya lalace baki da amfani a gurina a halin yanzu, Mariya ce mahad'in arzikina kuma zata dawo gidana babu gudu babu ja da baya, sannan wannan maganar da nake miki itace ta farko kuma itace ta karshe duk sanda kika sake cewa na sake ki to wallahi na gama auranki har abadah ni ba'a haka dani mace tamkar riga take a gurina.'' Yana maganar yana buge! babbar rigar dake jikinsa. Tsallake ta yayi yaje ya bude dakinsa ya shiga ya barta a gurin cikin wani irin hali mai wuyar fassara! babu abunda ya dameta a halin yanzu sai ganin ta samu haihuwa dole ta dauki mataki akan irin cutar da yake mata ta daina yarda yana dubga mata kwayoyi kuma ba zata sake yarda yasa condem (kwaroron roba) idan yazo auratayya da ita ba, dole itama ta haihu tunda har ya amince da 'yar da Mariya ta haifa a matsayin 'yarsa. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *15&16* Hujaj gabadaya hankali da tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin Mariya ta dawo gidanshi, domin shi kansa yanzu ya kara tabbatar da maganar malaminsa Mariya itace taurarinsu suka daidaita domin tunda ya aureta k'ofofin samunsa suka bude, ko wace harka ya buga yana samun nasara amma tun sa'ilin da ya rabu da ita komai nasa ya lalace ya rasa gane kan al'amuransa, saboda haka shawarar abokinsa Alhaji Sha'abu itace dai-dai da abinda yake zuciyarsa ya tabbatar da cewa abokin nasa ba zai cutar dashi ba. To cikin ikon Allah akayi suna yarinya taci sunan mahaifiyarsa Wato Maryama kamar yanda ya fad'awa Talatu, sosai yayi bajinta Alhaji Sha'aibu ya bashi aron kudi yayi duk abinda ake bukata na haihuwa dan ragon suna manya guda biyu ya sayawa maijego bayan uban naman 'kaurin daya siya mata, duk wannan facakar da yake Talatu tana da labari, hankalinta ya tashi ainun! lokacin ta shiga sauke samirun dake kan kwabarta ta kulle a dankwali ta nufi kasuwar bakin asibiti. Talatu na siyar da Samirun ta hada kan kudin tsaf ta nufi gurin malaminta domin ya taimaka mata akan al'amuran da suke faruwa. Yamma likis ta dawo cikin tarin gajiya da yunwa ta kwanta a tsakar gidan tana tunanin abinda za taci domin kwayar shinkafa basu da ita, gashi tayi ragwan azanci gabadaya kudin dake hannnta ta tattare ta bawa Malamin babban burinta ace Mariya ta lalace ta kuma yi nesa da ita. Sallamarsa ce ta dawo da ita hayyacinta. Ko kallonta bai yi ba ya kama hanyar dakinsa yana baza babbar rigar sabuwar shaddar dake jikinsa, tunda ya shigo gidan ya game da Kamshin turaransa, a zahiri ka ganshi zaka dauka wani babban hamshaki ne wanda yaci ya tada kai saboda yanayin sutturun da yake tu'ammali. Ta hadiye kakkauran yawun dake bakinta gatsal ta ambaci sunansa."Jamilu." Ya juyo yana kallonta fuskarsa a murtuke! mugun haushinta yake ji yana ganin duk ita ta janyo masa shiga talauci dan dai kawai Malaminsa yace kada ya sake ta amma da tuni ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda." "Kasan tun safe haka nake zaune banci abinci shin baka tsoron hakkina ya kama ka." Cikin taushin harshe tayi maganar. Yaja tsaki da fadin." Talatu ashe kin iya kwantar da murya ai na d'auka karfinki ne zai kwatar miki." Murmushin takaici tayi tace." Jamilu kenan ai ni yanzu na daina kishi da Mariya babban burina ka dawo da ita mu zauna tare tunda na fahimci cewa itace farin cikinka. Murmushi yayi yace." Kin ci albarkacin Mariya." Hannu ya zura cikin aljihu ya dauko kudi duba daya ya zara a ciki ya cilla mata da fadin." Gashinan da yau da

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});